Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a jami'ar likitanci ta Shahid Beheshti

Karatu a jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti

Loading

Saboda muhimmancin ilimi da tasirinsa a rayuwar mutane, bayanai da suka shafi karatu a jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti kamar tarihinta, kwasa-kwasan da ake yi cikinta, makarantunta da sauransu, na da matuƙar muhimmanci ga ɗalibai masu son karatu a cikinta. Wannan maƙala za ta taimaka muku wurin samun waɗannan bayanai.

Gabatarwa

Jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti (Shahid Beheshti University of Medical Sciences) ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati a ƙarƙashin kulawar hukumar kula da lafiya da karatun likitanci, a lardin Tehran. Wannan jami’a tana karɓar ɗalibai tun farko.  Yanzu haka jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti tana karɓar ɗalibai a matakan associate degree, degree, masters, PhD, specialized/superspecialized phD, a sashen karatun rana ko na dare. Jami’ar ta fara ayyukanta a matsayin kwalejin likitanci mai zaman kanta ta farko a shekarar 1959 (A da ana kiranta da suna Melli University kafin a canza mata suna a ranar 20 ga watan maris na shekarar 1960 domin raya ambaton sunan Dr. Ali Shaikhol Islam). A shekarar 1960 lokacin da gwamnati na biyan kuɗin makaranta domin ɗalibai su yi karatu kyauta sakamakon kuɗin mai da take samu, wannan ya samar da dama ga mutane masu mabambancin ƙarfin tattalin arziki, domin su samu shiga wannan jami’a ta hanyar jarrabawar ƙasa, ita ma wannan jami’ar ta koma kamar sauran jami’o’in gwamnati.
Akwai ɗalibai 12600, malamai 1414, da sauran ma’aikatan sashen koyarwa guda 130 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa akwai an wallafa maƙalolin ilimi guda 5553 a wannan jami’a, a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, tare da mujalla ta musamman guda 24. Har ila yau, jami’ar ta shirya taruka 49. Baya ga haka, Jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti ta yi nasarar wallafa maƙala 691 a matakin ƙasa da ƙasa.
Daga cikin ɗakunan gwaje-gwaje (laboratories) na wannan jami’ar akwai; ɗakin gwaje-gwaje na pathology, anatomy, immunology,  parasitology, medical physics, biochemistry, microbiology a kwalejin likitanci (school of medicine), da ɗakunan gwaje-gwaje na skill lab applied tests, na immunology a school of nursing and midwifery, da ɗakunan gwaje-gwaje na organic chemistry and analysis, instrumental analysis methods with physical and chemical control, toxicology and pharmacology a shool of pharmacy, da kuma ɗakunan gwaje-gwaje na anatomy, restorative phantom laboratory, children’s dental laboratory, fixed dental prostheses laboratory and removable dental prostheses laboratory a cikin dental college.

Martabar jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti a tsarin ranking na Shanghai

Ɗaya daga cikin abubuwan da ɗalibai ke lura da su wurin zaɓen makaranta shi ne ranking ko martabar jami’ar a tsarukan ranking na duniya kamar tsarin Shanghai wanda a shekarar 2022 jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti ta samu shiga sahun 800-601 jami’o’i 1000 na duniya, sannan kuma ta zo na biyu a jami’o’in likitanci na Iran.

Karatu a jami'ar likitanci ta Shahid BeheshtiMakarantu

Jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti na da makarantu 13 kamar haka:
_ School of Medicine
_ School of Dentistry
_ School of Pharmacy
_ School of Nursing and Midwifery
_ School of Paramedicine
_ Faculty of Rehabilitation
_ Faculty of Nutrition Sciences and Food Industry
_ Faculty of Health and Safety
_ School of Traditional Medicine
_ Faculty of Modern Medical Technologies
_ Faculty of Medical Sciences Education
_ Varamin Health Higher Education Complex

Kwasa-Kwasan Shahid Beheshti University of Medical SciencesKwasa-Kwasan Shahid Beheshti University of Medical Sciences

_ Medical Documents
_ Biostatistics 
_ Midwifery
_ Nursing 
_ Science of Food Industry 
_ Anatomy
_ Physiology
_ Bacteriology
_ Parasitology
_ Biochemistry
_ Biomedical Engineering
_ Pharmacy
_ Dentistry
_ Medicine
_ Periodontics 
_ Oral surgery
_ Jaw and Face
_ Dental Radiology
_ Pediatric Dentistry
_ Fixed and movable Prosthesis 
_ Oral diseases and Diagnosis 
_ Endodontics
_ Orthodontics
_ Pathology of Mouth and Jaw
_ Kidney and Genitourinary Tract Surgery
_ Bone and Joint Surgery
_ Obstetrics and Gynecology 
_ Da sauransu…
Domin samun cikakken list na kwasa-kwasan da ake yi a wannan jami’ar, ku sauke wannan fayil na ƙasa.

Kwasa-Kwasan Shahid Beheshti University of Medical Sciences

Jadawalin kuɗin makarantar Shahid Beheshti University of Medical Sciences 

Kuɗin makarantar school of medicine

Asibitocin koyarwa da cibiyoyin kiwon lafiya na Shahid Beheshti University of Medical Sciences

_ Akhtar Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Imam Hossein (a.s.) Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Ayatollah Taleghani Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Punzdahe Khordad Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Shohadae Tajrish Medical, Educational and Treatment Center
_ Shahid Labafinejad Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Shahid Modares Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Tarafeh Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Mofid Medical, Educational and Therapeutic Center for Children
_ Luqman Hakim Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Masih Daneshvari Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Mahdieh Medical, Educational and Therapeutic Center
_ Imam Khomeini (RA) Firouzkoh
_ Ayatollah Ashrafi Isfahani
_ Zaeim Pakdasht
_ Sevom Sha’ban, Damavand
_ Martyrs of Pakdasht
_ Martyr Muftah Varamin
_ Shohadae Gomnam
_ Martyr Sattari

Cibiyoyin Bincike

_ Institute of Nutritional Research and Food Industries of the country
_ Research Institute of Pulmonary Diseases
_ Research Institute of Gastrointestinal and Liver Diseases
_ Dental Sciences Research Institute
_ Endocrinology and Metabolism Research Institute
_ Children’s Health Research Institute

Cibiyoyin Nazari

_ Functional Neurosurgery Research Center
_ Eye Research Center
_ Cancer Research Center
_ Research Center for Prevention of Cardiovascular Diseases
_ Research Center for Ethics and Medical Law
_ Genitourinary Stem Cells Research Center
_ Research Center for Safety Promotion and Injury Prevention
_ Stem Cell Research Center
_ Gastroenterology, Liver and Children’s Nutrition Research Center
_ Children’s Kidney Diseases Research Center
_  Genomic Research Center
_ Children’s Surgery Research Center
_ Bone, Joint and Related Tissues Research Center
_ Traditional Medicine and Medical Vocabulary Research Center
_ Children’s Neurological Research Center
_ Physical Medicine and Rehabilitation Research Center
_ Men’s Health and Reproductive Health Research Center
_ Poison Research Center
_ Midwifery and Reproductive Health Research Center
_ Pediatric Infectious Research Center
_ Children’s Respiratory Diseases Research Center
_ Neuroscience Research Center
_ Children’s Congenital Blood Diseases Research Center
_ Pharmaceutical Sciences Research Center
_ Infectious and Tropical Diseases Research Center
_ Behavioral Science Research Center
_ Kidney and Urinary Tract Diseases Research Center
_ Research Center for Social Factors Affecting Health
_ Chronic Kidney Diseases Research Center
_ Protein Technology Research Center
_ Trachea Diseases Research Center
_ Phytochemistry Research Center
_ Anesthesiology Research Center
_ Physiotherapy Research Center
_ Cell and Molecular Biology Research Center
_ Cardiovascular Research Center
_ Proteomics Research Center
_ Laser Application Research Center in Medicine
_ Telemedicine Research Center
_ Research Center for the Control of Harmful Factors in the Environment and Work
_ Dermatology Research Center
_ Research Center for the Prevention of Women’s Diseases
_ Mycobacteriology Research Center
_ Tobacco Prevention and Control Research Center
_ Neurophysiology Research Center
_ Neurobiology Research Center
_ Brain Mapping Research Center
_ Hearing Disorders Research Center
_ Skull Base Research Center
_ Food Health Research Center 
_ Air quality and Climate Change Research Center

Maƙalolin Kimiyya

_ Journal of Faculty of Dentistry
_ Medical Educational Journal
_ Bimonthly Researcher Magazine

Abubuwan more rayuwa na Shahid Beheshti University of Medical Sciences

_ Samar da inshorar lafiya da  inshorar haɗari ga ɗalibai
_ Gudanar da ayyukan ɗalibi a sassa daban-daban idan buƙata ta taso
_ Tsarawa,  tafiyarwa da kimanta tsarin zirga-zirgar ɗalibai da kyautata ayyukan da suka danganci hakan
_ Tsarawa,  sa ido da kimanta ayyukan cibiyoyin walwalar ɗalibai kamar buffets, shagon photocopy da typing, da sauransu
_ Samar da kayan karatu ga ɗalibai
_ Bashin ɗalibai
_ Bashin masauki
_ Ayyukan kula da lafiyar haƙora ga ɗaliɓai
_ Cibiyar bada shawara ga ɗalibai
_ Laburaren jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti (wanda aka assasa a shekarar 1960, babban laburaren yana da sassa a makarantu da cibiyoyin bincike daban-daban waɗanda yake tafiyarwa ta hanyar satellite.)
_ Wuraren kwanan Shahid Beheshti University of Medical Sciences (Tana da wurin kwana 14 na maza da na mata a cikin garin Tehran, waɗanda za su iya ɗauke mutum 4000. Waɗannan wuraren kwanan sun ƙunshi abubuwa kamar wurin cin abinci, wireless system, ɗakin karatu, masallaci, ɗakin kallo, kayan wasanni, wurin gina jiki, filin grass carpet, ayyukan kiwon lafiya da bada shawara, shagunan sayayya, da suransu.)
_ Shiryawa da tsara rubuce-rubuce na ciki da waje masu alaƙa da tafiyar da harkokin ɗalibai
_ Ci gaba da shiga cikin daurorin karatu na kowa da kowa, da kwasa-kwasan horo na musamman waɗanda suka shafi sanin makamar aiki ga ma’aikata
_ Ƙwarewar ɗaiɗaiku, aiki, da sauransu
_ Ikon amfani da kayan aiki na zamani da manhajojin fasahar sadarwa da aikace-aikace wajen shiryawa da tsara shirye-shirye, ayyuka da rahotanni (musamman darussan ICDL 7)
_ Gudanar da wasu ayyukan da akan buƙata daga sama

Kayan aikin Shahid Beheshti University of Medical SciencesYanayin Wuri

Wannan jami’a na nan a unguwar Valenjak, a titin A’rabi. Jami’ar na kusa da muhimman wurare kamar asibitin Ayatullahi Taleghani ta Tehran, cibiyar saye da sayar da Balut, makarantar likitanci ta jami’ar, rukunin zaurukan al’adu da wasanni na Sabz, cibiyar ayyukan genetic da genomic ta ƙasa, da bankin Refah.

Adireshin Shahid Beheshti University of Medical Sciences

Adireshi: Tehran, babbar hanyar Shahid Chamran, titin Yaman, titin Shahid A’rabi, kusa da asibitin Ayatollahi Taleghani


Tambayoyin da ake yi


  1. Wasu irin takardu ake buƙata domin neman admission a wannan jami’a ta Shahid Beheshti?
    Passport, hoto, transcript, certificate, cv, motivation letter, recommendation letter.
  2. Yaya ake biyan kuɗin makaranta?
    Ana biyan kuɗin makaranta ne kawai da dala, kuma a bankin Refah wanda yake cikin jami’ar.

Loading






Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *