Ardabil gari ne daga cikin garuruwa masu sanyi na ƙasar Iran a lardin Ardabil da ke arewacin ƙasar. Wannan gari na da tarihin shekara dubu biyar. Manufarmu a wannan rubutu ita ce bayani a kan yanayin karatu, yanayin al’adu, rayuwa, yawon buɗe ido da sauransu na garin Ardabil.
Ardabil
A aikin ƙirge da aka yi a shekarar 2016, an samu mutum 529374 (iyalai 158,627) a garin Ardabil. Garin ɗaya ne daga cikin manyan garuruwan Iran. Mutanen garin na magana da yaren turkancin azeri, amma yaren da ake amfani da shi a hukumance a makarantu da ofisoshi farsi ne. Garin Ardabil na da girman murabba’in kilomita 17951.4.
Kasantuwar lardin Ardabil a kusa da dutsen Sabalan, lardin na cikin larduka mafi sanyi na ƙasar Iran. Matsakaicin awon ɗumin yanayi na shekara digiri 6 ne. Kasancewar lardin a kewaye da tsaunuka shi ne babban dalilin sanyinsa. Garin Ardabil na da matsakaicin yanayi a lokacin zafi saɓanin tsananin sanyinsa a lokacin hunturu. Saboda yawan ruwan sama, ana samun nau’i daban-daban na tsirrai da ganyayyaki a wurin. Haka kuma akwai duwatsu masu aman wuta a yankin, wanan ya sa ake samun idanun ruwa masu ɗumi.
Tsarabar garin Ardabil ta haɗa da zuma, dasƙararriyar madara da manshanu, fatir, halwa, ƴaƴan sunflower, saƙaƙƙun abubuwa, da sauransu.
Karatu
Akwai jimillar jami’o’i da cibiyoyin ilimi 24 a lardin Ardabil. Jami’ar Mohaghegh Ardabili ɗaya ce daga cikin fitattun jami’o’in garin (ita ce ta goma a tsakanin duka jami’o’in ƙasar Iran. Domin ƙarin bayani kuna iya ziyartar rubutunmu mai suna Karatu a University of Mohaghegh Ardabili).
Jami’o’in lardin Ardabil sun wallafa mujallu 18 na musamman. Har ila yau a waɗannan cibiyoyin, an wallafa maƙalolin ilimi guda 33326, maƙalolin mujalla 5050, maƙalar taro guda 21241, da maƙaloli 5050 a matakin ƙasa da ƙasa.
Zirga-Zirga
Lardin Ardabil na da tazara sosai da lardukan yammaci, gabaci, da lardukan tsakiyar Iran. Lardi mafi kusa da Ardabil shi ne lardin Azarbaijan Sharqi. Akwai hanyoyin mota da na jirgin sama da za su iya kai ku wannan gari, amma babu hanyar jirgin ƙasa. Ana iya amfani da motocin bus na kamfanin Vahed domin yawatawa cikin gari. Hakazalika akwai motocin haya na taksi a cikin gari masu fentin ruwan ɗorawa, ana iya ɗaukar shata ko shigar gabaɗaya.
Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido
Har ila yau, garin Ardabil na cikin muhimman wuraren ƙasar Iran da ke ɗauke da abubuwan tarihi da yawon buɗe ido. Mafi yawan abubuwan tarihi na wannan gari, na zamanin daular Safawiyawa ne. Wuraren shaƙatawa da yawon buɗe ido na na Ardabil sun haɗa da:
_ Tafkin Shourabil
_ Dajin Fandakhlo
_ Makwancin Shah Isma’il
_ Baƙi’ar Shiakh Safiyuddeen Ardabili
_ Gidan tarihi na anthropology
_ Gidan Manafzadeh
_ Gidan tarihi na Sadeghi
_ Tafkin Sooha
_ Gadar Haft Cheshme
_ Fadar Owltan Maghan
_ Idanuwan ruwa na Sar’ain
_ Tafkin Neor
_ Gardaneh Heyran
_ Wurin shaƙatawa na Bolagrar
_ Kogin Balkhalor
_ Balghi Chai
_ Ƙauyen Alvars
_ Mutum-Mutumin Baba Dawood
_ Da sauransu…
Cibiyoyin Magani
Asibitoci da cibiyoyin magani a garin Ardabil sun haɗa da:
_ Asibitin Dr. Fatemi
_ Asibitin Sabalan
_ Asibitin Imam Khomeini
_ Cibiyar kiwon lafiya ta Mirza Hoseini
_ Cibiyar kiwon lafiya ta Imam Reza (AS)
_ Asibitin Vali Asr (AF)
_ Asibitin Alawi
_ Cibiyar kiwon lafiya ta Imam Sajjad (AS)
_ Asibitin Ars Pars Abad
_ Asibitin Bu-Ali
_ Cibiyar magani ta Isar
_ CIbiyar magani ta Farhangiyan
_ Cibiyar magani ta Shook
_ Clinic ɗin Noor
_ Asibitin musamman na Arta
_ Da sauransu…
Hotel da masaukai
_ Shourabil Hotel
_ Sabalan Hotel
_ Hosein Apartment Hotel
_ Darya Hotel
_ Masaukin baƙi na Ideal
_ Negin Hotel
_ Sarae Hotel
_ Masaukin baƙi na Hayat
_ Ideal Boutique Hotel
_ Yakamoz Hotel
_ Masaukin baƙi na Qasr Chubi Khalkhal
_ Masaukin baƙi na Khane Habib
_ Rukunin masaukai na Nisan
_ Rukunin masaukai na Samiragh
_ Masaukin baƙi na Hayat
_ Da sauransu…
Ɗakunan Karatu
_ Laburaren Shaikh Safiyyuddeen Aradabili
_ Laburaren Arshadi
_ Laburaren Shahid Behzad Mohammadi
_ Laburaren Niyar
_ Laburaren Moghaddas
_ Laburaren Fadak
_ Laburaren ƙungiyar metaphysics na Prof Rinko
_ Laburaren Ketabshahr Iran
_ Laburaren Imam Ali (AS)
_ Laburaren gari na Shahryar
_ Laburaren gari na Sheikh Sharaful Deen
_ Da sauransu…