تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Minene biza kuma minene fasfo?

Minene biza kuma minene fasfo?

Loading

Idan kuna buƙatar amsoshin tambayoyi kamar; minene biza da fasfo, minene bambancin biza da fasfo, kashe-kashen biza, kashe-kashen fasfo, ku kasance tare da mu. A halin yanzu, sabbin bayanan ƙididdiga na nuna cewa akwai ƙasashe 195 mabambanta a doron duniya a nahiyoyi 7 na Africa, Asia, Australia, Europe, North America, South America, da Antarctica.

Kowace daga cikin ƙasashennan 195 na da ayyanannar iyaka a ƙasa, ruwa, ko iska kuma tana da dokokinta na musamman da suka shafi yin tafiya ko hijira. Da gaske ne dukan mu ahalin wannan duniyar ne, amma ba za mu iya sauya muhallinmu daga wata ƙasa zuwa wata haka kawai ba tare da wani tsari ko mallakar wasu takardu na shaida ba. Hatta zama a wata ƙasar na gajeren lokaci ba tare da takardun shaida ko wani tsari ba ba abu ne mai yiwuwa ba.

Saboda haka ku kasance tare da mu a wannan rubutun domin mu yi muku cikakken bayani akan minene biza, yaya ake karɓar biza, bambancin da ke tsakanin biza da fasfo, da kuma kashe-kashen biza tare da sauran muhimman bayanan da ya kamata ku sani game da su.

Minene Biza

Minene Biza?

Babu shakka da yawanku za su iya sanin me ake nufi idan an ambaci sunan biza, to amma ga waɗanda ba su riga sun san ma’anar biza ba sai mu ce; biza na nufin izinin shigar mutum wata ƙasa da ba ƙasarsu ba.

A taƙaice za a iya cewa biza wani izini ne mai ɗauke da sharuɗa da ake bayarwa idan mutum zai shiga ƙasar da ba tasa ba na tsawon wani ayyanannen lokaci. Gwamnatin kowace ƙasa ita ke da alhakin sanya sharuɗan biza ga ƴan wata ƙasa da ba ƙasarta ba ko ta ɗaga ƙafa ga wasu bisa la’akari da irin siyasa da al’adunta.

Biza na iya zama ta gajeren zango (kwana 1 har zuwa watanni) ko kuma ta dogon zango, sannan tana aiki ne kawai a ƙasashen da aka bugata dominsu. Ana iya buga biza a matsayin stika a jikin shafukan fasfo ko kuma ta zama electronic wato ta cikin na’ura wadda ake bugawa online.

Minene bambancin biza da fasfo?

Biza izinin shiga wata ƙasa ne wadda ƙasa ke ba mutanen da suka cika sharuɗan da ta gindaya na shiga ƙasarta. Amma international passport wato fasfo takardar shaida ce (kamar dai ID card) wanda ake amfani da shi wajen gane mutanen wata ƙasa idan sun fita wajen ƙasarsu. Duk ɗan ƙasa na da fasfo na kansa kuma zai iya amfani da shi wajen neman biza ta mabambantan ƙasashe.

Amma idan ana magana a kan bambancin da ke tsakanin biza da fasfo, za a iya cewa biza na amfani ne kawai idan akwai fasfo kuma bai yi expiring ba. Mutum zai iya neman bizar daban-daban kamar bizar yawon buɗe ido ko bizar neman aiki a ƙasar Germany ko Australia ko wata ƙasar matsawar yana da fasfo. Wani abun dubawa a bambancin tsakanin biyunnan shi ne inganci da tasiri. Ma’anar inganci da tasiri a nan shi ne abubuwa biyunnan suna da janibobi daban-daban wanda da yawan mutane basu sani ba.

Misali idan mutum na da fasfo ɗin ƙasar America, baya ga yawan shekarun da fasfo ɗin yake yi kafin ya ƙare, yana da tasiri sosai ta yadda mutum zai iya amfani da shi wajen shiga ƙasashe 184 ba tare da biza ba.

Amma a babin biza, tana aiki ne iya na lokacin da aka ayyana ne kawai sannan dole a duba yiwuwar shiga ƙasa fiye da ɗaya da ita. Misali ana iya amfani da bizar Schengen a ƙasashe 26, hakan na nuna irin ƙarfin tasirin wannan biza.

Minene biza

Nau’o’in Biza

Yanzu kun san ma’anar biza, sai kuma bayani game da nau’o’in biza. Wannan batu ya ƙunshi ɓangarori daban-daban. Ɓangare mafi muhimmanci shi ne tsawon lokacin amfani da biza wanda ya kasu kashi biyu kamar haka:

 • Bizar gajeren zango
 • Bizar dogon zango

Yana da kyau ku san cewa bayanan da suka ta’allaƙa da biza na da muhimmancin gaske waɗanda sun zarce tunaninku sannan ko wace ƙasa na da nata kalar dokokin da sun keɓanceta ne ita kaɗai. Dukda haka za mu yi ƙoƙarin yi muku bayanin abunda ya sauwaƙa.

Da yawan mutane idan sun ji an ambaci bizar gajeren zango za su fara tunanin bizar yawon buɗe ido, amma yana da kyau ku san cewa bizar gajeren zango ba ta taƙaitu a iya bizar yawon buɗe ido ba, akwai wasu nau’o’in biza da su ma na gajeren zango ne kamar:

 • Transit: izinin gajeren zango ne (tsanani awa 24) domin wucewa ta iyakar ƙasa, ruwa ko ta sama ta wata ƙasa.
 • Tourism: Ana amfani da ita wurin yawon shaƙatawa da zama na ɗan gajeren lokaci a wata ƙasar. Haka ana iya amfani da ita wajen yin wasu ƙananan abubuwa irinsu ziyarar ƴan’uwa da abokan arziki, halartar tarukan kasuwanci ko na karatu na gajeren lokaci.

Su kuma bizojin dogon zango ga su kamar haka:

 • Bizar aiki
 • Bizar karatu
 • Bizar zama
 • Bizar hannun jari
 • Bizar kasuwanci
 • Bizar start-up

Wace irin biza muke buƙata?

Akwai nau’o’in biza da dama da ake bayarwa bisa la’akari da abun da zai kai mutum ƙasar da zai je. Haka kuma akwai yiwuar shiga wasu ƙasashen ba tare da biza ba idan ta kama. Misali idan za ka tafi yawon buɗe ido a ƙasar Turkey na tsawon wata 1 ba ka da buƙatar biza, amma idan aiki za ka je yi ko karatu, dole ne ka nemi bizar aikin ko bizar karatu a ofishin jakadancinsu.

 • Educational Visa: Idan kana son zuwa wata ƙasa karatu dole ne ka nemi bizar karatu ta wannan ƙasar.
 • Transit Visa: Idan za ka tafi wata ƙasa amma ba kai-tsaye ba har ya zama cewa za ku ɗan yi zaman jira a wata ƙasar a kan hanya, mai yiwuwa ku buƙaci karɓar wannan nau’in biza ɗin wato transit visa.
 • Tourist Visa: Idan za ku shiga wata ƙasa ku ɗan kwana biyu domin yawatawa, za ku buƙaci wannan nau’in biza ne.
 • Work Visa: Ana iya karɓar bizar aiki ne kawai idan mutum ya samu gayyatar aiki daga ƙasar da yake son zuwa.
 • Medical Visa: Ana bayar da ita ne domin marasa lafiyan da za su yi jinya a asibitocin wata ƙasa.

Domin karbar izinin shiga ƙasa na gajeren lokaci, kawai ana buƙatar ka zaɓi lokacin da za ka tafi embassy ɗin ƙasar tare da tarjamar takardun da ake buƙata. Daga nan ka shigar da buƙatar neman biza, da zaran ka karɓi bizar shikenan ka samu izinin shiga ƙasar da kake son zuwa.

Amma idan za ka jima a ƙasar ko kuma za ka zauna can ne gabaɗaya a madadin tafiyar gajeren zango, dole ne ka zaɓi bizar dogon zango sannan baya ga abubuwan da muka ambata a sama, dole a nemi ƙarin wasu mihimman takardu.

Misali, idan kana son tafiya karatu na dogon zango ne a ƙasashe irin Canada, kafin biza dole ne ka fara neman takardar makaranta (admission letter) tare da sauran takardun da ke da alaƙa dahadafin tafiyarka irinsu cv, transcript, language certificate, da sauransu wanda za a nuna a embassy da makarantar da za a je.

Ta yaya za mu karɓi biza?

Dole ne a tura buƙatar karɓar biza da farko kafin a yi maganan karɓa. Ana iya neman biza ta hanyar zuwa embassy ko ta hanyar aike, hatta ta online a wasu lokutan. Ana buga biza a matsayin stika ko stamp a jikin fasfo. Ana kuma iya bada ita a matsayin takarda mai zaman kanta ko kuma a tura ta na’ura, amma idan ta na’ura ne dole a yi printing a riƙe a hannu yayin shiga ƙasar da za a tafi.

Wasu ƙasashe (irin ƙasashen da ke yankin Schengen) na da yarjejeniya a tsakaninsu cewa za su ba ƴan ƙasarsu damar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba. Majalisar kula da yawon buɗe ido ta duniya ta sanar da cewa yawan masu yawon buɗe ido da ke buƙatar biza kafin tafiya zai ragu sannu a hankali nan da ƴan shekaru masu zuwa.

Minene sharuɗan karɓar biza?

Wata bizar ba ta buƙatar sai mutum ya je da kansa, wata kuma mutum ya tafi ofishin immigration ko ofishin jakadancin ƙasar da za shi kafin lokacin tafiyarsa. Wanann ya sa da yawan mutane ke damƙa process ɗin karɓar bizarsu a hannun kamfanonin da ke da ƙwarewa a wannan fannin. Waɗannan kamfanoni na da lasisin yi ma matafiya biza daga ofisoshin jakadancin ƙasashe.

Wasu irin mutane ake hana ma biza?

Wasu ƙasashe kan hana biza ga mutanen da ke ɗauke da wasu nau’o’in cuta na musamman irin cutar ƙanjamau, dukda shi ma wannan ya dogara da nau’in bizar da ake son karɓa. Hakazalika masu bada biza suna duba record ɗin wanda za a bawa idan bai taɓa aikata laifuka a baya ba, ko kuma idan bai taɓa yin mu’amalolin da suka saɓa doka ba kafin su bari ya shiga ƙasarsu. Haka kuma akwai ƙasashen da ke hana biza ga mutanen da suka zo daga ƙasar da suke da rashin jituwa ko ƙiyayya da ita.

Matakan karɓar biza

Matakai da dokokin karɓar biza sun dogara ne da ƙasar da mutum zai tafi. Akwai ƙasashen da basu da ofishin jakadanci a Iran. Wannan ya sa dole sai an je wata maƙociyar ƙasa domin yin wasu ayyukan da suka shafi karɓar biza irin thumbprint da sauransu. Ana iya bin matakan karɓar biza na ƙasashe da yawa irinsu Canada, Schengen, Australia, England, da sauransu a shafin yanar gizo na visaland.

Me yasa sai an zabi lokacin zuwa embassy?

Bisa la’akari da nau’in bizar da kuke so, dole ku bada takardun da ake buƙata a embassy sannan ku yi interview da ma’aikatan. Bayan bayar da takardu ana komawa domin yin thumbprint. Amma sakamakon yawan masu zuwa neman biza, wasu ofisoshin jakadancin na yin wani tsari na ayyana lokacin da kowa zai dawo domin gujewa cinkoson jama’a.

Farashin karɓar biza

Kuɗin biza sun dogara da ƙasa da kuma nau’in bizar da ake so a karɓa. Kuɗin sun ƙunshi kuɗaɗen duka ayyukan da ake yi na bizar a dunƙule, ayyuka irinsu thubmprint, tantance takardu, da sauransu. Kuɗin biza sun bambanta tsakanin ƙasashe, ta yiwu ma ba sai an biya kuɗin wasu abubuwan ba a wata ƙasar.

Adireshin shafukan ofisoshin jakadanci na wasu ƙasashe:

Shafin ofisoshin jakadancin ƙasar Iran

Shafin ofisoshin jakadancin ƙasar Iraq

Shafin ofishin harkokin waje na ƙasar Afghanistan

Shafin ofishin harkokin waje na ƙasar Pakistan

Shafin ofisoshin jakadancin ƙasar Yemen

Related Posts
Leave a Reply