[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Manyan laburarukan ƙasar Iran

Manyan laburarukan ƙasar Iran

Loading

Ƙasar Iran mai tarihin ilimi, kimiyya, al’ada, na da laburaruka masu ɗauke da taskokin da ba kasafai ake iya samunsu a sauran ƙasashe ba. Ƙasarmu ta tanadar muku waɗannan resources ɗin domin taimaka muku wurin cimma hadafinku.
Manufarmu ita ce sauƙaƙa muku karatu a Iran ta hanyar sauƙaƙa muku zaɓen gari da jami’a da kuke son ku yi karatu a ciki. A gaba kaɗan za mu kawo muku bayanai a kan laburaruka da resources masu inganci na ƙasar Iran. Idan kuna sha’awar karatu ko gabatar da ayyukan research a ƙasar Iran, ku kasance tare da mu har zuwa ƙarshen wannan rubutun.

Manyan laburarukan ƙasar Iran

1- Laburaren Melli

2- Laburaren Jundi Shapur (Iran Mall Complex)

3- Babban laburaren Sharif University of Technology

4- Babban Laburaren University of Tehran

5- Sansanin laburarukan gama-gari na garin Tehran

6- Laburaren Tibyan

7- Noor Digital Library

8- Babban Laburaren Hakim Sabzevari University

9- Babban Laburaren Research Institute of Humanities and Cultural Studies

10- Babban Laburaren Islamic Azad university

1– Laburaren Melli

Laburaren Melli na Iran ya fara aiki a shekarar 1937 a hukumance, a shekarar 2002 bisa amincewar majalisar tafiyarwa ta ƙoli, an haɗe laburaren na melli da ma’aikatar taskace bayanai ta ƙasa, yanzu haka su biyun sun ci gaba da aiki amma a rarrabe. Laburaren Melli (National Library) na nan a babbar hanyar Shahid Haghani, ita kuma ma’aikatar taskace bayanai ta ƙasa na nan a titin Mirdamad a garin Tehran. Ofishin membership da ma’aikatar taskace bayanai su ke da alhakin bibiya da tantance maziyarta laburaren, hakazalika akwai katin shaida na membership mai matakai daban-daban da ake ba maziyartan domin su samu isa ga littafan musamman.

Laburaren Melli ɗaya ne daga cikin manyan laburarukan ƙasar Iran yana da girman murabba’in mita 9,700 a wani gini mai hawa 8, sannan mafi yawan littafai da taskokin ƙasa na fannin adabi, falsafa da irfani, fiƙihu da usul, litikanci da ilimin taurari, tarihi da wani rukunin fassarar farko na littafan aro waɗanda aka rubuta a harsunan ƙasashen waje (zuwa yaren farsi).

2- Laburaren Jundishapur Iran Mall Complex

Za a iya cewa laburaren Jundishapur da ke Iran Mall a garin Tehran shi ne mafi salo da ƙawa a cikin manyan laburare guda goma na Iran da muka ambata. Laburaren yana da kyan kallo saboda tsarin gininsa na musamman wanda ya yi kama da irin ginin laburare na ƙasashen turai na da, laburaren na ɗaukar hankalin maziyarta ta yadda har wasu na zuwa laburaren musamman dan shaƙatawa da ɗaukar hotunan selfie. Yawan masu zuwa yawon buɗe ido har ya zarce na masu zuwa karatu. Laburaren Jundishapur shi ne na biyu ta kowace fuska, daga Laburaren Melli sai shi. Yana da girman murabba’in mita 3,300.

3- Babban Laburaren Sharif University of Technology

Laburaren jami’ar fashaha ta Sharif ya fara aiki ne a shekarar 1965 a fannin Science and Engineering. Wannan laburare shi ne laburare na 3 a cikin manyan laburarukan ƙasar Iran kuma yana nan a ginin Mujtahidi mai girman murabba’in mita 6000 a hawa 6. Babban laburaren jami’ar fasaha ta Sharif na da ɓangarori daban-daban kamar haka: Sashen management, sashen accounting da scientific information consultancy, media and documents provision, sashen aro, thesis, da sashen wallafe-wallafe da order.

4- Babban laburaren University of Tehran

Babban laburaren jami’ar Tehran shi ne laburare mafi girma a tsakanin laburarukan jami’o’in Iran kuma ɗaya ne daga cikin laburare goma na ƙasar. Laburaren ya ƙunshi taskoki masu yawa na litattafai a fannoni daban-daban na kimiyya da adabi. An samar da sashen asali na laburaren a shekarar 1949 ta hanyar wasu littafan sadaukarwa na Sayyed Muhammad Mashkouh malami a jami’ar, wanda sun kai kwafi 1329 na litattafai rubutun hannu.

Laburaren na da girman sama da murabba’in mita 22000 a hawa 9. Hawa biyu a ƙarƙashin ƙasa, ground floor, hawa na 1, da sauran hawa 5 waɗanda ke ɗauke da litattafai da sanadodi. Laburaren na da membobi sama da dubu 50 kuma a kowace rana yana samun maziyarta aƙalla 4,500 na daga ɗliban jami’ar da na wasu jami’o’in da cibiyoyi da mu’assasoshin koyarwa da na bincike, na ciki da wajen ƙasr Iran.

5- Sansanin laburarukan gama-gari na garin Tehran

Tun daga shekarar 1978 ma’aikatar al’adu da fasaha ta fara assasa laburarukan gari da gidajen karatu da nufin bunƙasa al’adu da fasaha da mutanen gari tare da inganta al’adar zaman gari tsakanin al’umar ƙasar Iran. Tare da assasa laburaruka da samar da kayan aiki a cikinsu, ma’aikatar ta bazama neman ma’aikata masu kula da laburaren don kaiwa ga natija. Wannan Sansanin na da laburare 82 da ƙwararrun ma’aikata 229 daga cibiyoyin al’adu masu inganci.

6-Laburaren Tibyan

Laburaren Tibyan shi ne laburaren na’ura (digital library) mafi kyau a Iran sannan ya cika duka sharuɗan ƙasa da ƙasa kuma an assasa shi ne a shekarar 2003 bayan gudanar da binciken da ya dace game da laburaren na’ura. Laburaren na’ura na Tibyan na da jadawalin resources kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada, kuma yana da ‘therasus’ na Farsi da Islamic Science da aka karkasa zuwa yaruka 3; English, Arabic, da Farsi.

A cikin Digital Library na Tibyan ana gabatar da ayyuka mabambanta kamar tambayar masu kula da litattafai, tura resources, duba index, sharing resources, shigar da ƙorafi, jotting, da sauransu. Ga shafin laburaren kamar haka: library.tebyan.net

7-Noor Digital Library

Laburaren na’ura na Noor yana gudanar da ayyukansa ne a fannin Islamic Science da Human Science kuma ya fara aiki ne a shekarar 2006. Yana ɗaya daga cikin manyan laburaruka goma na ƙasar Iran kuma zuwa yanzu ya samar da taken litattafai sama da dubu 8 da kwafin litattafai sama da dubu 16 a fannin Islamic Science a maudu’ai kamar haka: Ulumul Qur’an da Tafsir, Hadith, Addu’o’i da Ziyarori, Nahjul Balagah, Kalam da Falsafa, Geography, Tarihi da Sirah, Fiqhu, Usul, Akhlaq da Irfan, Adabi da Manɗiq, da Mazhabobin Addinin Musulunci.

8-Babban Laburaren Jami’ar Hakim Sabzevari

An assasa babban laburaren jami’ar Hakim Sabzevari a shekarar 1987 a tsohon ginin Tarbiat Moallem inda ya fara aiki da kwafin litattafai dubu 2. Bayan shuɗewar shekaru tare da ƙaruwar yawan kwasa-kwasan da ake yi a wannan jami’a, shi ma wannan laburaren ya ci gaba da bunƙasa inda ya tashi daga ƙaramin laburare zuwa babba har ya samu shiga sahun manyan lanuraruka na ƙasar inda yake ɗauke da sama da kwafin litattafai dubu 80 da sauran resources waɗanda ake tafiyarwa da manhajar ‘simorgh’. An buɗe sabon muhallin laburaren a wani gini mai girman murabba’in mita 3,000 inda za a cigaba da tafiyarda da ayyukan maziyarta laburaren.

9-Babban Laburaren Research Institute of Humanities and Cultural Studies

Wannan laburare yana cikin manyan laburaruka goma na ƙasar Iran a fannin Human Science. An assasa shi a shekarar 1977 a cibiyar nazarin al’adu ta Iran. An kafa hedikwatar laburaren a shekarar 1982 ta hanyar haɗe laburarukan wasu ma’aikatu da cibiyoyin bincike irin su Academy of Literature and Art, Research Institute of Communication Sciences and Development of Iran, Iranian Culture Foundation, Shahnameh Ferdowsi Foundation, da Iranian Center for the Study of Cultures.

Akwai litattafan fannoni kamar haka: Persian literature, linguistics, religious philosophy, ancient culture and languages, history of Iran (and other nations), da social science.

Rufewa

An zaɓo waɗannan laburaruka ne bisa ma’aunai mafi muhimmanci ga ɗalibai da masu bincike. Ana iya samun resources masu muhimmanci daga taskokin ilimi ta hanyar waɗannan laburarukan cikin sauƙi. A kowace ilimi na ƙaruwa ta hanyar bincike-binciken da ake yi.

Related Posts
Leave a Reply