[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a University of Birjand

Karatu a University of Birjand

Loading

Karatu a University of Birjand

Jami’ar Birjand (University of Birjand) jami’ar gwamnati ce a garin Birjand, kudancin lardin Khorasan Razavi wadda aka assasa a shekarar 1975. Karatu a University of Birjand babbar dama ce ga ɗalibai, wadda babbar cibiya ce ta ilimin kimiyya a gabacin ƙasar Iran, sannan cibiyar koyarwa mafi girma kuma mafi daɗewa a kudancin lardin na Khorasan Razavi. Tana da tarihin fiye da shekaru 46 da gogewa a ɓangaren koyarwa, zamantakewa, da al’adu. Ta horar da sama da ƙwararru 30,000.

Gabatarwa

A halin yanzu, akwai kimanin ɗalibai 11,044 masu karatu a jami’ar Birjand tare da malamai 1,040. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙalolin kimiyya guda 11,854 a mujallu da tarukan cikin gida. Jami’ar Birjand ta mallaki mujallu 21 na musamman sannan ta shirya taruka 44 zuwa yanzu. Har ila yau, jami’ar ta wallafa maƙala 2,985 a matakin ƙasa da ƙasa. Akwai makarantu 11 da harabobi 5 na jami’ar Birjand a garuruwan lardin Khorasan Razavi. Ita ce matattarar kimiyya da karatu a gabacin ƙasar Iran.

Karatu a University of Birjand

Martabar Jami’ar Birjand

A cewar tsarin ranking na Times wanda ɗaya ne daga cikin tsarukna ranking masu inganci na duniya, jami’ar Birjand na cikin jami’o’i 1102 na farko a duniya, sannan ita ce mai matsayi na 6 a cikin jami’o’in ƙasar Iran. A tsarin ranking na ma’aikatar ilimin kimiyya ta ƙasar Iran, an saka jami’ar Birjand a jami’o’in mataki na 2 duba da ayyukanta bisa manufar bunƙasa karatu da binciken kimiyya da fasaha, tare da warware wasu matsalolin ƙasa. Shi kuma tsarin ranking ɗin jami’o’i na Green Metric a bayanansa na shekarar 2022, ya saka jami’ar Birjand a sahun “Green Universities” na duniya. 

Kuɗin Makaranta a University of Birjand

ردیفمقطعرشتهمیزان شهریه(ریال)
1کارشناسی(BACHELOR)علوم انسانیRial304,000,000
2کارشناسی ارشد(MASTER)علوم انسانیRial364,800,000
3دکتری(PHD)علوم انسانیRial1,276,800,000

Makarantu da Fannoni

Makarantar Electrical and Computer Engineering

kwalejin Electrical Engineering da Computer Engineering ita ce kwaleji mafi girma a jami’ar Birjand kuma kwaleji mafi ingattattun kayan aiki da na karatu, da keɓantaccen sashen bincike na electrical engineering. Kwalejin na da membobin tsangayar ilimi guda 35 da gungun wasu ƙwararrun injiniyoyi waɗanda ke taimakawa a ayyukan workshop da na laboratoty. yanzu haka akwai ɗalibai kusan 1000 masu karatun digirinsu na farko a fannonin electronics, telecommunications, control, power, software, hardware, da information technology, sai kuma ɗalibai 200 masu karatun master’s da phd. Ga wasu daga cikin kwasa-kwasan da ake yi a wannan kwaleji:

  • Electronic Engineering
  • Telecommunication Systems Engineering
  • Control Engineering
  • Power Engineering
  • Computer Engineering (Bachelor’s and Master’s)
  • Biomedical Engineering (Bachelor’s)

Makarantar Engineering

An assasa makarantar Engineering ta jami’ar Birjand a shekarar 1988 da sunan “Technical School” wato makarantar fasaha, inda ta fara gudanar da ayyukanta a shekarar 1989 da ɗaukar farko na ɗalibanta a matakin associate degree a kwas ɗin electrical electronics. Duba da irin cigaban da jami’ar ta samu a fannin electrical engineering, wannan kwalejin ya tsayu da ƙafafunsa a shekarar 2011 inda aka raba shi biyu zuwa kwalejin electrical and computer engineering da kwalejin engineering (wanda ya ƙunshi fannonin mechanical, civil, da mining engineering).

Sassan koyarwa (departments): Mechanical Engineering, Civil Engineering, and Mining Engineering.

Kwalejin Sciences

Sassan koyarwa: Physics, Chemistry, Geology, and Biology

Ita ce kwaleji ta farko da aka assasa a jami’ar Birjand a shekarar 1975. Ta fara aiki a 1977 ta hanyar karɓar ɗalibai 120 a fannoni uku na Chemistry, Physics, da Mathematics.

Makarantar Mathematics and Statistics

  • Departments: Mathematics da Statistics
  • Matakan karatu: Bachelor’s zuwa Doctorate

Makarantar Literature and Humanities

An kafa kwalejin literature na jami’ar Birjand a shekarar 1990 inda ya fara aiki da ɗalibai a fannoni biyu na Persian Literature and Educational Sciences tare da zurfafawa a kwas ɗin Curriculum Planning tare da membobin tsangayar ilimi 7. Sannu a hankali, kwalejin ya bunƙasa tare da ƙara yawan kwasa-kwasan Library & Information Science, Physical Education & Sports Sciences, da History.

Kwalejin Agriculture

Departments: Water Engineering, Animal Sciences, Agronomy

Matakan karatu: Bachelor’s zuwa Doctorate

An assasa wannan kwalejin na Agriculture a shekarar 1979 inda ya fara aiki da ɗalibai 33 a matakin diploma a harabar Mohammadieh Agricultural Training Center. Yanzu haka wannan kwalejin yana a harabar Amirabad, kilomita 5 daga hanyar Birjand-Kerman, da muhalli mai girman murabba’in mita 40,000. Kwalejin ya keɓantu da horar da ƙwararru a fannoni daban-daban na agricultural sciences da natural resources.

An ware kwalejin Natural Resources and Environmental Sciences daga wannan kwalejin ne a shekarar 2011, yanzu yana aiki ne da cikakken iko a harabar ta Amirabad.

تحصیل در دانشگاه بیرجند

Kwalejin Natural Resources & Environmental Sciences

Fannoni: Range & Watershed Management, Environmental Sciences
Matakan Karatu: Bachelor’s zuwa Doctorate
Departments: Seed Science da Environmental Technology

Kwalejin Educational Sciences & Psychology

Wannan kwalejin ya samu ƴanci daga kwalejin Literature a shekarar 2009 amma ba a hukumance ba, bisa zartarwar kwamitin daraktocin jami’ar. An buɗa departments uku na wannan kwaleji a wani muhalli mai zaman kansa, departments ɗin sun haɗa da psychology, educational sciences, da library & information science (wanda aka canja ma suna zuwa Department of Information Science and Knowledge Studies). Har zuwa watan Oktoban 2019, wannan kwaleji ya kasance a tsakiyar garin Birjand (a mahaɗar titin Daneshga da titin Hefdah Shahrivar kusa da babban ofishin haraji), amma yanzu tana nan a Harabar Behavioral Sciences (tsohuwar kwalejin Literature).

Departments: Psychology and Counseling, Educational Sciences, and Information Science, Knowledge Studies Library 

Ƙungiyoyin Bincike: Youth Studies

Matakan Karatu:

  • Undergraduate (bachelor’s) – Psychology, Educational Sciences, Information Science, Knowledge Studies 
  • Master’s: Educational Psychology, Curriculum Planning, Educational Management, Information Science, Knowledge Studies
  • Doctoral: Curriculum Planning

Makarantar Physical Education & Sports Sciences

An assasa kwalejin physical education na jami’ar Birjand a shekarar 1995 da izinin majalisar bunƙasa karatun gaba da sakandare, tare da ɗalibai 30 da aka zaɓo daga kwalejin literature. A shekarar 2009 ne aka raba wannan kwalejin da kwalejin literature.

Kwalejin Arts

Adadin malamai membobin faculty: 15
Matakan karatu: Associate Degree, Bachelor’s Degree, Master’s Degree
Departments: Archaeology, Carpet, Handicrafts, Islamic Art
Laboratories da Workshops: 10

Kayan Aikin Birjand University

Jimillar faɗin wuraren karatu na jami’ar Birjand zai kai murabba’in mita 53,000, mita 113,000 kuma na wuraren wasanni da al’amuran more rayuwa bisa la’akari da manufarta ta karatu da kimiyya. Jami’ar na da babbar laboratory ɗauke da kayan aiki na zamani.

Jami’ar ta yi tanadin abubuwan karatu da kayan aiki na musamman don amfanin ɗalibanta. Daga ciki akwai:

  • Laburare
  • Self-service
  • Health & Treatment Center
  • Counseling & Treatment Center
  • Zauren wasanni, swimming pool, filin wasannin basketball, volleyball, football

تحصیل در دانشگاه بیرجند

 

Yanayin Muhalli

Lardin Khorasan Junubi na daga cikin yankunan sahara masu kyau a ƙasar Iran wanda garin Birjand ne cibiyarsa, ana iya sanin wannan garin ta hanyar sunan wannan jami’a. Jami’ar na nan a ƙarshen titin Daneshga – Harabar Shokatabad – Babbar harabar jami’ar Birjand. Garin Birjand shi ne na farko idan ana magana akan samar da ruwa ga al’ummar ƙasar Iran kasantuwar cewa yana da nasa hanyoyin samar da ruwa da duka kayan aikin da ake buƙata.

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *