Jami’ar Mazhabobin Addinin Musulunci (International University of Islamic Denominations) jami’a ce mai alaƙa da dandalin “World Forum for Proximity of Islamic Schools of Thought”, wadda aka assasa bisa umarnin kai tsaye na jagoran jamhuriyar musulunci ta Iran Sayyed Ali Khamene’i domin koyar da fiƙihu da shari’a. Bisa ƙudurin majalisar ƙoli ta juyin juya hali na al’adu a shekarar 2022 dangane da gyara tsarin dokokin jami’ar, an cire kalmar “Non-profit” daga sunan jami’ar sannan aka ƙara “International”. Baya ga haka, da yiwuwar a assasa rassan wannan jami’ar a wasu ƙasashen duba da wannan ƙuduri na majalisa.
Gabatarwa
Jami’ar Mazhabobin Addinin Musulunci ta Ƙasa da Ƙasa jami’a ce ta gwamnati a birnin Tehran. An assasa ta ne a shekarar 1992 domin samar da malaman musulunci da masu bincike, da kuma tarbiyyantar da muballigai daga aƙidu daban-daban domin ayyukan ciki da wajen ƙasar Iran. Ita kaɗai ce jami’ar da ke gabatar da fannonin fiƙihu da shari’a mai karɓar ɗalibai daga kowace mazhaba daga mabambantan ƙasashen duniya.
Yanzu haka jami’ar na da sassa huɗu a faɗin ƙasar Iran, ɗauke da ɗalibai masu karatu sama da 2,500 da malamai 200. Zuwa yanzu an jami’ar ta wallafa maƙalolin ilimi na cikin gida da na ISI guda 159, a mujallu da tarukan ciki da wajen ƙasa.
A wannan jami’a, mutane daga mabambantan mazhabobin musulunci na karatu a tare. Duba da hadafinta, jami’ar ta sauƙaƙa tattaunawa tsakanin malaman addini daga mazhabobi mabambanta, wanda hakan ya ba su damar warware rashin fahimtar addini da na mazhaba da ke tsakaninsu, ta haka za a samu haɗin kai da ɗunkewar musulmi.
Nasarorin Ilimi
Da taimakon Allah Maɗaukaki tare da ƙoƙarin masu tafiyar da makarantar, malamai da ɗalibanta, kimanin kashi 60 bisa ɗari na ɗaliban da suka kammala karatunsu a jami’ar, sun samu karɓuwa a matakin postgraduate (master’s da phd) a sauran jami’o’i da manyan cibiyoyin ilimi. Yanzu haka wasunsu sun ci gaba da aiki a fagen koyarwa da cibiyoyin bincike da ƙungiyoyin addini da na al’ada.
Kuɗin Makaranta a International University of Islamic Denominations
Makarantu
Makarantar Islamic Denominations Jurisprudence and Law
Bachelor’s:
- Islamic Jurisprudence and Law of Imamiyah
- Islamic Jurisprudence and Law of Shafi’i
- Islamic Jurisprudence and Law of Hanafi
Master’s:
- Comparative Jurisprudence and Private Law
- Comparative Jurisprudence and Public Law
- Comparative Jurisprudence and Criminal Law
Doctoral:
- Jurisprudence and Foundations of Islamic Law
Makarantar Quran and Hadith
Bachelor’s:
- Quranic Sciences and Hadith
- History of Islam
- Arabic Language and Literature
Master’s:
- Quranic Sciences and Hadith
- History of Islam
Doctoral:
- Quranic Sciences and Hadith
- History of Islam
Makarantar Philosophy, Theology, and Islamic Mysticism
Bachelor’s:
- Islamic Philosophy and Mysticism
- Religions and Islamic Denominations
Master’s:
- Islamic Philosophy
- Abrahamic Religions
- Islamic Mysticism
Kayan Aikin Jami’a
Domin tabbatar da gogewar ɗalibai a harshen larabci da turanci, jami’ar kan shirya musu daurorin sharar fage na kyauta. Hakazalika jami’ar kan shirya wa zakarun ɗalibanta daga kowane mataki tafiye-tafiyen bincike zuwa wata ƙasa a cikin ƙasashen musulunci.
A matakin master’s da phd kuma, waɗanda suka yi aikin theses mai inganci, akan basu kyaututtuka sannan kuma a basu damar wallafa shi a wallafe-wallafen jami’ar.
Har ila yau, jami’ar na bada wuraren kwana, tallafin karatu (scholarship), da bashin karatu har zuwa ƙarshen karatunsu bisa dokokin kwamitin walwala, akwai kuma laburaruka, kafteriyoyi, kayan wasanni, da muhalli mai inganci da kwanciyar hankali.
Wallafe-Wallafen Ɗalibai
1. Quarterly Educational and Research Journal of the Light of Unity (na malaman Shia da Sunna, ɗalibai, da gwanaye)
2. Specialized Student Quarterly Journal of Justice (Scientific Association of Comparative Jurisprudence and Law)
3. Al-Judi (Scientific Association of Shafi’i Jurisprudence and Law)
4. Traveler Newsletter (Student Basij)
5. Hamraz (General Department of Student Affairs)
6. Al Qalam (English Language Educational Group and Students)
Yanayin Muhalli
Jami’ar na nan a unguwar Palestine-Inqilab a cikin birnin Tehran, titin Ravanmehr. Ita ɗaya ce daga cikin jami’o’i 12 da ke wannan unguwar. A kusa da ita akwai wasu muhimman wurare kamar Asibitin Modain, Negin Amir Akram Shopping Complex, Borazandeh Banquet Hall, Aburayhan Specialty and Super Specialty Clinic, Borazandeh Restaurant, da ofishin Ƙungiyar masu sayar da abinci ta Tehran.
mazaheb.ac.ir, shi ne adireshin shafin yanar gizo na jami’ar mazhabobin addinin musulunci ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Tehran. A nan za ku iya samun bayanai dangane da kwasa-kwasan jami’ar, labarai, membobin faculty, da sauran muhimman bayanai.