[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Sajjad University

Karatu a Sajjad University

Loading

Jami’ar Fasaha ta Sajjad (Sajjad University of Technology) jami’a ce mai zaman kanta a birnin Mashhad da ke lardin Khorasan Razavi, an assasa ta a shekarar 1995. Zuwa yanzu akwai ɗalibai 4100 da malamai 61 a wannan jami’a. Mun tattara muku muhimman bayanai game da yanayin karatu a wannan jami’a ta Sajjad, ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

Jami’ar Sajjad ta fara ayyukanta a fagen koyarwa a shekarar 1995 da sunan “Sajjad Higher Education Institute”. Bayan samun izini daga majalisar bunƙasa karatun gaba da sakandare na ma’aikatar ilimin kimiyya a Mashhad. Jami’ar ta jima a sahun fitattun jami’o’in firabet na ƙasar a ranking ɗin ma’aikatar ilimin kimiyya. Bayanan ƙididdiga na ƙungiyar gwajin karatu ta ƙasa ya nuna cewa jami’ar Sajjad na da ɗalibai sama da 3,500 da suka yi nasara a jarabawar shiga matakin Mastas tsawon shekaru biyar da suka gabata. Hakazalika daga cikin nasarorin jami’ar Sajjad, akwai shigar ɗaliban da ta yaye ɓangarori daban-daban na masana’antu.

A Sajjad University of Technology, ana yin kwasa-kwasai daban-daban a duka matakan karatu: digiri, mastas, da phd. Bayanan ƙididdiga na jami’ar sun nuna cewa ita ce jami’a ta biyu (Bayan Jami’ar Ferdowsi) da ɗalibai suka fi zaɓa a tsakanin jami’o’in da ke birnin Mashhad. Bincike ya nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalolin kimiyya guda 981 a mujallu da taruka daban-daban na cikin gida. Har ila yau, jami’ar Sajjad ta wallafa maƙala 65 a matakin ƙasa da ƙasa, sannan ta karɓi baƙuncin taruka 8 zuwa yanzu.

Sajjad University

Martabar Sajjad University

A cewar ofishin hulɗa da jama’a na ƙungiyar Islamic World Science Citation Database (ISC), bayan ƙungiyar ta ISC ta tantance jami’o’i 115 na gwamnati da 17 na firabet da ke ƙasar Iran bisa la’akari da wasu ma’aunai da ƙa’idoji, inda jami’ar Sajjad ta zo a matsayi na 3. Ƙungiyar ta yi ranking ɗin manyan makarantu daban da na jami’o’i.

Kuɗin Makarantar Sajjad University

Makarantu

  • Makarantar Civil Engineering, Architecture, and Urban Planning
  • Makarantar Industrial and Mechanical Engineering
  • Makarantar Electrical Engineering and Biomedical Engineering
  • Makarantar Computer Science and Information Technology
  • Makarantar Humanities

Faculties at Sajjad University

Kwasa-Kwasan Karatu

  • Computer Engineering (Software)
  • Computer Engineering (Artificial Intelligence and Robotics)
  • Computer Engineering (Security Engineering)
  • Computer Engineering (Computer Networks)
  • Civil Engineering (Geotechnics)
  • Civil Engineering (Structures)
  • Civil Engineering (Construction Management)
  • Civil Engineering (Earthquake)
  • Architectural Engineering
  • Urban Planning
  • Electrical Engineering (Control)
  • Electrical Engineering (Integrated Electronic Circuits)
  • Electrical Engineering (Power Systems)
  • Electrical Engineering (Telecommunication Systems)
  • Electrical Engineering (Digital Electronic Systems)
  • Electrical Engineering (Planning and Management of Electric Power Systems)
  • Biomedical Engineering (Bio-Electric)
  • Industrial Engineering (Production and Service Systems)
  • Industrial Engineering (Systems Modeling and Data Analysis)
  • Mechanical Engineering (Energy Conversion)
  • Materials and Metallurgical Engineering (Materials Characterization and Selection)
  • Electrical Engineering
  • Biomedical Engineering
  • Civil Engineering
  • Architecture Engineering
  • Urban Engineering
  • Energy Engineering
  • Materials and Metallurgical Engineering
  • Industrial Engineering
  • Mechanical Engineering
  • Computer Engineering
  • Computer Science
  • Industrial Management
  • Sports Science
  • Law
  • Psychology
  • English Language Teaching
  • Electrical Engineering (Electronics)
  • Electrical Engineering (Telecommunication Systems)

تحصیل در دانشگاه سجاد

Kayan Aikin Sajjad University

Laburaren jami’ar Sajjad na ɗauke da adadi mai yawa na litattafan Farsi da na Latin, maƙalolin kimiyya, da mabambantan mujallu waɗanda ake ƙarowa akai-akai. Hakazalika laburaren na da ɓangaren e-library (wato laburaren na’ura), wanda ke ba ɗalibai damar su sauke abubuwan karatu ta yanar gizo. Ga abubuwan da ke cikin wannan laburare a ƙididdige kamar haka:

– Wallafaffun litattafai 19,067 a harshen Farsi.
– Litattafan na’ura (e-book) guda 38,000
– Wallafaffin litattafai na Latin a mabambantan fannoni kamar architecture, biomedical engineering, industrial engineering, civil engineering, computer engineering, electrical engineering, da sauransu.

Akwai mujallun wata-wata a cikin laburaren irin su; Nano Technology Monthly, Electric, Superior Waves, Construction, Casting Industry Monthly, Architect Bi-monthly, and Amir Kabir Civil Mechanical Engineering Quarterly. Har ila yau, jami’ar na da dining hall, da wuraren kwana na zamani.

Yanayin Muhalli

Jami’ar na nan a unguwar Shahid Razavi na birnin Mashhad, a titin Ghasemi na 65. A kusa da jami’ar Sajjad akwai Gidan Tausa na Mah, Kafteriya, Gidan Biredi, wurin shaƙatawa na Parvaneh, da supermarket. Ga adireshin yanar gizo na shafin jami’ar Sajjad kamar haka: sadjad.ac.ir.

Related Posts
Leave a Reply

Your email address will not be published.Required fields are marked *