University of Sistan and Baluchestan, wata jami’a ce ta gwamnati a garin Zahedan da ke lardin Sistan-Baluchestan. An assasa ta a shekarar 1974 a matsayin kwalejin Engineering inda ta fara ayyukanta. A shekarar 2005, jami’ar Sistan-Baluchestan ta yi fice a matsayin babbar jami’ar lardin, sannan ta cike duka sharuɗan da ake buƙata domin shiga cikin sahun jami’o’in ƙasar waɗanda suka ci gaba. An bayyana ta a matsayin jami’a mai babbar daraja a Iran. Karatu a jami’ar Sistan-Baluchestan kan iya zama da dama ta musamman ga ɗalibai.
Gabatarwa
Jami’ar Sistan-Baluchestan tana cikin jami’o’i cikakku kuma ita ce dandalin kimiyya a yankin kudu maso gabacin ƙasar Iran. A halin yanzu akwai kwaleji 12 a ƙarƙashin wannan jami’a tare da international campus, da cibiyoyin bincike guda 4, sannan akwai ɗalibai sama da 22,000 ke karatu tare da malamai 385 a cikinta. Zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙalolin kimiyya guda 17,210 na cikin gida tare da maƙalar ISI, a taruka da mujallun ciki da wajen ƙasar Iran.
Jami’ar ta fara aiki da suna “University of Baluchestan” a shekarar 1974 da kwas ɗin Civil Engineering a matsayin wani sashe na kwalejin Engineering a garin Zahedan. Daga baya a shekarar 1977, aka buɗa kwalejin Maritime and Marine Sciences a garin Chabarar, daga baya kuma a 1986 da 1989, aka buɗa kwalejin Basic Sciences da na Agriculture a garin Zabol.
Daga ƙarshe a shekarar 1991, bisa ƙudurin majalisar bunƙasa ilimin gaba da sakandare a kan yin majar jami’o’in horar da malamai da sauran jami’o’i, an haɗe jami’ar horar da malamai ta Zahedan mai ɗauke da ɗalibai 2,000 masu karanta mabambantan kwasa-kwasai guda 9, da jami’ar Sistan-Baluchestan, sannan fannonin Basic Sciences na jami’ar horar da malamai suka dawo ƙarƙashin kwalejin Sciences na jami’ar Sistan Baluchestan.
Martabar University of Sistan and Baluchestan
A sakamakon ƙarshe da tsarin ranking na ISC ya fitar, jami’ar ta shiga sahun jami’o’i 12 na farko na ƙasar Iran. A shekarar 2005, bisa ma’aunai 26 da ma’aikatar ilimin kimiyya ta ayyana, jami’ar ta samu ƙarin daraja daga jami’o’i “masu ƙoƙarin ci gaba” zuwa jami’o’in da “suka ci gaba“, hakan ya ƙara ɗaga ranking ɗinta. Yanzu haka, Jami’ar Sistan-Baluchestan na cikin jami’o’in ƙasar Iran masu daraja ta farko (jami’o’in rukunin [A] ).
Kuɗin Makarantar Jami’ar Sistan Baluchestan
Makarantu
Jami’ar na da makarantu 12, cibiyar koyarwa 1, cibiyoyin bincike 5, da rukunin koyara guda 1 kamar haka:
- Shahid Nikbakht Faculty of Engineering
- Faculty of Basic Sciences – Central Administration
- Faculty of Literature and Humanities – Former Teacher Training
- Faculty of Economics and Administrative Sciences – Basat Building
- Faculty of Art and Architecture
- Faculty of Educational Sciences and Psychology – Kamal Building
- Faculty of Physical Education
- Faculty of Electrical and Computer Engineering
- Faculty of Geography and Environmental Planning – Kamal Building, Third Floor
- Faculty of Agriculture and Natural Resources (Saravan)
- Faculty of Theology
- Faculty of Mathematics
- Faculty of Industry and Mining (Khash)
Cibiyoyin Bincike
- Research Institute of Earth Sciences and Geography
- Research Institute of Subcontinent and South Asian Studies
- Research Institute of Mining (Under Construction)
- Research Institute of Nanotechnology
- Research Center for Fuzzy Systems
Kwasa-Kwasan Karatu
- Archaeology
- History
- English Language and Literature
- English Language Translation
- Teaching English Language
- Arabic Language and Literature
- Persian Language and Literature
- Social Sciences – Sociology
- Social Sciences – Anthropology
- Theology and Islamic Knowledge
- Religions and Mysticism
- Quranic Sciences and Hadith
- Islamic Jurisprudence and Legal Foundations
- Philosophy and Islamic Wisdom
- Geography and Planning
- Environmental Geography
- History – Ancient Iran
- History – Islamic Iran
- Hadith Sciences – Exegesis
- Hadith Sciences – Nahj al-Balagha
- Climatology – Environmental Climatology
- Geomorphology – Theoretical Geomorphology
- Urban Geography and Planning
- Environmental Hazards
- Rural Geography and Planning
- Spatial Planning
- Urban Geography and Planning – Urban Development
- Geography and Tourism Planning
- Rural Geography and Planning
- Climatology
- Geomorphology
- Agricultural Economics – Policy and Agricultural Development
- Agricultural Economics – Production Economics
- Agricultural Unit Management
- Agricultural Economics – Natural Resources and Environmental Economics
- Agricultural Economics – Agricultural Product Marketing
And so on …
Kayan Aikin Jami’a
Girman jami’ar Sistan Baluchestan ya kai kimanin hekta 194, wanda hekta 80 daga ciki cike suke da ɗabi’a. Ɗalibai na amfani da waɗannan koren filayen na ɗabi’a wajen tattaunawar karatu, hutawa da shan iska, wanda wannan na taimaka ma kuzarinsu da tare da sama musu da nishaɗi. Sauran abubuwan wannan jami’a sun haɗa da:
- Parks
- Wuraren shan iska
- Ɗakunan tattaunawa da tarukan al’adu, addini, da na wasanni
- Ingantattun kayan wasanni da zaurukan gina jiki
- Zaurukan taron kimiyya da tarukan addini
- Ingantattun laburaruka na zamani
- Assasa data center na jami’a wanda zai iya ɗauke na’urorin server guda 300
- Buɗa cibiyar cyber security ta musamman wadda ita ce ta farko kuma ɗaya tilo a kaf lardin
- Sadar da layin sadarwa na fiber optic na jami’ar zuwa network na ƙasa
- Ƙara saurin internet na jami’ar zuwa 600 Mbps
- Laburare mafi girma a kudu maso gabacin ƙasar Iran
Wuraren Kwana
Jami’ar na da ɗalibai masu yawa daga sassa daban na ƙasar Iran, saboda haka ta yi tanadin hostel ɗauke da abubuwan buƙata. Jami’ar ta kammala duka tsare-tsaren da suka dace na hidimta wa ɗalibanta maza da mata a farfajiyar hostel. Rukunin wuraren kwana na wannan jami’a na ɗauke da sama da block 35 na hostel a ciki da wajen jami’ar, waɗanda aka tanada don sauke ɗalibai.
Akwai hostel 29 a cikin harabar jami’ar, tare da wasu 6 a cikin gari. Wuraren kwanan da ke wajen makaranta suna aiki a ƙashin kansu. Biyar daga cikinsu na ɗalibai mata ne, 1 kuma na maza. Saboda haka ɗalibai mata ba su da wata damuwa dangane da wurin kwana, za su iya karatunsu cikin kwanciyar hankali a jami’a mafi kyau ta kudu maso gabacin ƙasar Iran.