[gtranslate]
تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Jami'ar Shahrekord

Karatu a Jami’ar Shahrekord

Loading

Jami’ar Shahrekord Wata jami’a ce ta gwamnati a garin Shahrekord, cibiyar lardin Chaharmahal-o Bakhtiari wadda ita ma ana lissafa ta cikin jerin fitattun jami’o’in ƙasar Iran. Wannan gari shi ne cibiyar lardi mafi tsayi a Iran wanda hakan ya sa ake masa laƙabi da “rufin Iran”. Yanayin garin a lokacin zafi yanayi ne madaidaici wato ba tsananin zafi, amma a lokacin sanyi akwai sanyi sosai. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan yanayin karatu a wannan jami’a ta Shahrekord.

Gabatarwa

An yi yunƙurin farko na samar da jami’a a wannan garin na Shahrekord ne a shekarar 1977 inda aka assasa kwalejin Animal Husbandry a garin, a wani gini na haya a Meidane Daneshga. Bayan juyin juya hali na al’adu da sake buɗe jami’o’i a shekarar 1983, an sauya wannan kwalejin na Animal Husbandry zuwa kwalejin Agriculture aka kuma maida shi ƙarƙashin jami’ar fasaha ta Isfahan inda ya cigaba da ayyukansa ta hanyar karɓar ɗalibai 30 a kwas biyu na Agricultural Affairs da Livestock Affairs a matakin diploma.

A shekarar 1988 ne aka bunƙasa kwalejin na Agriculture zuwa babban rukunin koyarwa sannan aka maida wannan rukunin koyarwar zuwa “Jami’ar Shahrekord” bisa amincewar majalisar bunƙasa karatun gaba da sakandare a shekarar 1991. Yanzu haka a wannan jami’a akwai ɗalibai 8200 masu karatu tare da malamai 321.

Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu wannan jami’a ta yi nasarar wallafa maƙalolin ilimi guda 9522 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan kuma ta wallafa mujalla 8 na musamman, kuma ta shirya taruka 26 zuwa yanzu. Har ila yau, jami’ar Shahrekord ta wallafa maƙala 7326 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, mafi yawan maƙalolin da aka wallafa a wannan jami’ar suna ɗauke da kalmomin “Iran” da “comparison” a matsayin muhimman kalmomin maƙala.

Karatu a Jami'ar Shahrekord

Martabar Jami’a

Jami’ar Shahrekord A shekarar 2017, jami’ar ta samu shiga sahun jami’o’in kashi na farko (1%) na duniya da kuma jerin jami’o’i masu tasiri a duniyar engineering na duniya, sannan bisa la’akari da wallafa maƙaloli mafi yawa na ISI, a tsakanin jami’o’in Iran ta samu matsayi na 18. A sabon sakamakon da tsarin ranking na TIMES ya fitar na shekarar 2023, jami’ar Shahrekord ta samu shiga wannan tsarin karo na 4 kenan a jere inda ta zo a matsayi na 1001 – 1200 a tsakanin jami’o’i 1799 na duniya waɗanda suka cika sharuɗan da wannan tsarin ke buƙata.

Daga cikin abubuwan alfahari na wannan jami’ar akwai samun lambar zinare a bukin farko mai take “Inventions and Innovations of Superior Ideas”, samun matsayi na biyu a bukin Sheikh Bha’ei, samun matsayi na 3 a bukin “Iranian National Youth Festival”, samun lambar zinare a gasar olympics ta duniya ƙirƙire-ƙirƙiren Nanoelectronics ta ƙasar South Korea, samun matsayi na farko a gasar bukin matasan ƙasar Iran a ɓangaren Agriculture a taron baje koli na Information and Communication Technology mafi girma na duniya (CEBIT) a matsayin ɗaya daga cikin wakilai 3 na ƙasar Iran, wanda sassan growth center technology na jami’ar suka yi nasarar samu.

Kuɗin makarantan jami’ar Shahrekord

Gradeeducational groupAnnual Tuition ( in Dollars )
MastersHumanities$450
MastersOther$550

Makarantu

School of Mathematical Sciences

A wannan kwalejin ana yin kwasa-kwasan Pure Mathematics, Applied Mathematics, da Computer Sciences a matakin digiri, masters, da PhD.

Faculty of Literature and Humanities

Wannan makarantar ta karɓi ɗalibai a matakin masters na kwas ɗin Persian Language and Literature a shekarar 2002. A 2003 kuma ta karɓi ɗaliban digiri a kwasa-kwasan Language Translator da Archaeology. A tsakanin shekarar 2004 zuwa 2009 an ƙara kwasa-kwasan physical education, physiology, sports, fiction, da corrective movements. Daga shekarar 2011 zuwa yanzu kuma an ƙara kwasa-kwasan law, archaeology, religions, mysticism, da pure literature.

School of Veterinary Medicine

Kodayake kwalejin ya fara ayyukansa a matakin PhD ne ta hanyar ɗaukar ɗaliban Veterinary Medicine, amma yanzu yana aiki a matakin PhD fiye da can baya. Jami’ar na da kwasa-kwasai kamar haka a matakin masters

  • Food Health
  • Veterinary Parasitology
  • Bacteriology
  • A matakin PhD akwai kwasa-kwasai kamar haka
  • Veterinary Medicine
  • Obstetrics and Reproductive Diseases of Livestock,
  • Internal Diseases of Large Livestock

Poultry Health and Diseases a ƙarƙashin kwasa-kwasan Food Health, da Bacteriology.

School of Basic Sciences

Da fari kwalejin Basic Sciences ya fara aiki da kwas 2 na Biology da Mathematics. A halin yanzu akwai department 4 na Biology, Genetics, Physics, da Chemistry a wannan kwalejin a matakin digiri, masters, da Phd.

Faculty of Technical Engineering

Wannan kwaleji shi ne kwaleji na 3 da aka assasa a jami’ar. Kwalejin na nan ta ɓargaren yamma a cikin jami’ar. Jami’ar ta Shahrekord na gabatar da waɗannan kwasa-kwasai a matakin digiri, masters, da PhD a wannan kwalejin.

  • Mechanical Engineering
  • Electrical Engineering
  • Materials Engineering
  • Civil Engineering
  • Computer Engineering

Faculty of Agriculture

An kafa ginshiƙin farko na jami’ar Shahrekord ta hannun wannan kwalejin. A wannan kwalejin akwai kayan aiki daban-daban da suka shafi harkokin noma kamar irinsu greenhouse, sashen animal husbandry, sashen computer, da mabambantan ɗakunan gwaje-gwaje. Sannu a hankali wannan kwalejin ya fara aiki da waɗannan kwasa-kwasan:

  • Plant Production Engineering
  • Animal Production Engineering
  • Water Engineering and Agricultural Machinery Engineering
  • BSc. Soil Engineering

Yanzu kuma akwai fiye da kwas 16 waɗanda ake yi a matakin masters, da kwas 15 a matakin PhD.

Faculty of Natural Resources and Earth Sciences

Shi kuma wannan kwaleji ya fara da department 3 na pasture and watershed, forest science, da fisheries. Ɗalibai masu sha’awa za su iya karanta kwasa-kwasan forestry engineering da fisheries a matakin digiri, sai kuma kwas ɗin pasture, watershed, da forestry a matakin masters.

Faculty of Arts, Farsan

Wannan kwalejin ya fara aiki a shekarar 2003 ne da ɗalibai 52 a fannin Visual Arts (AS – BSc), inda suka kammala a zango na biyu na shekarar 2004/2005.
Yanzu haka akwai kwas ɗin Carpet mai rassan design, dyeing, da sauran rassa, da kwas ɗin Handicrafts mai rassan pottery, timber, da miniature. A halin yanzu akwai membobin dindindin na tsangayar ilimi 5 a waɗannan sassan na carpet da handicraft, sannan a kowane zangon karatu akwai malamai 30 da suke koyarwa.

Karatu a Jami'ar Shahrekord

Wuraren bincike

  • Research Institute of Animal Technology
  • Biotechnology Research Institute
  • Research Institute of Common Diseases of Humans and Animals
  • Growth Center
  • Water and Nano Resources Research Center
  • Innovation Acceleration Center and APA Specialized Center

Abubuwan More Rayuwa

Jami’ar Shahrekord ta yi tanadin abubuwan more rayuwa, kayan wasanni da da karatu daban-daban domin sauƙaƙewa ɗalibanta yanayin karatu. Ga wasu daga cikin abubuwan da jami’ar ta yi tanadi:

Laburaren jami’ar Shahrekord a cibiyar taskace bayanai ta samar da wuri mai kyau don karatun ɗalibai da ayyukansu na bincike. Hakazalika kowace makaranta daga cikin makarantun (kwaleji) wannan jami’a na da nata abubuwan irinsu laburare, laboratory, da workshop masu inganci.

Swimming pool, filin wasa mai grass carpet, zaurukan wasanni daban-daban irinsu volleyball, basketball, futsal, da sauransu sun samar da yanayi mai kyau na wasannin ɗalibai. Wasu daga cikin waɗannan kayan na wasanni suna cikin rukunin wuraren kwanan ɗalibai.

Wuraren kwana

Jami’ar Shahrekord ta yi tanadin wuraren kwana 4 na ɗalibai mata, 4 na ɗalibai maza. Yana da kyau ku san cewa ba ina ake samun irin waɗannan hostel masu inganci a makarantun Iran ba.

  • Wurin kwanan ɗalibai mata
  • Wurin kwana na Velayat (na maza)
  • Wurin kwana na Shahid Raja’ei
  • Wurin kwanan ɗalibai mata
  • Wurin kwanan ɗalibai na Molavi
  • Wurin kwanan ɗalibai na Meraj
  • Wurin kwanan ɗalibai masu iyali na Yas
  • Wurin kwanan ɗalibai mata na Sadr

Karatu a Jami'ar Shahrekord

Yanayin Wuri

Jami’ar Shahrekord na nan a lardin Chaharmahal-o Bakhtiari, garin Shahrekord da Shahid Hoseinali Turki, titin Rahbar. Jami’ar na kusa da cibiyar sayayya ta Shahrekord da tashar bus ta titin Rahbar. Hakazalika, wannan jami’a na ɗaya daga cikin jami’o’i masu inganci na wannan yanki. Akwai gidajen abinci a kusa da jami’ar irinsu Taha Restaurant, Self na maza, inda ɗalibai za su iya zuwa don su ci abinci.

Adireshi: Lardin Chaharmahal-o Bakhtiari, Shahid Hoseinali Turki, titin Rahbar

Shafin jami’a: https://www.sku.ac.ir

 

Related Posts
Leave a Reply