Jami’ra Shahid Chamran ta Ahvaz wadda aka fi sani da suna Jami’ar Jundishapur, jami’a ce da ke ƙarƙashin ma’aikatar ilimi kuma ɗaya daga cikin jami’o’i mafi kyau na ƙasar Iran. Tarihin jami’ar Jundishapur yana komawa ga ƙarni na 4 ko 5 na miladiyya, a tsawon ƙarni 6 ta kasance cibiyar ilimi inda ake yin mabambantan kwasa-kwasai. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai a kan yanayin karatu a wannan jami’a ta Shahid Chamran.
Gabatarwa
An buɗa jami’a mai suna Jami’ar “Gandishapur” a ranar Lahadi daidai da 25 ga watan September, shekara ta 1955 a garin Ahvaz. Jim kaɗan aka canja sunan zuwa “Jundishapur.” An gina jami’ar a kusa da gulbin Karun, a wani fili kusa da lambun Garmsiri. Jami’ar na da tsarin gini na musamman irin yawan makarantu da gine-gine da ke cikinta wanda ƙwararrun masana zanen gini irinsu Kamran Diba da Andre Godard suka zana.
Kwalejin Agriculture ita ce kwaleji ta farko da aka fara kafawa a jami’ar. Kwas ɗin Agriculture, Literature, Mathematics, da Medicine kuma su ne kwasa-kwasan farko da aka fara yi a wannan jami’ar ta Jundishapur. A ranar Lahadi 15 ga watan June, 1958 ne aka yaye rukunin ɗaliban farko na wannan kwaleji na Agriculture tare da basu shaidar kammalawa a wani buki da aka shirya. Bayan wani lokaci, kwaljein Medicine na jami’ar ya koma jami’a mai zaman kanta wadda aka sa ma sunan “Jundishapur University of Medical Sciences”. Bayan aukuwar juyin musulunci na Iran, a lokacin yaƙin kare-kai ne jami’ar ta koma ɗaya daga cikin manyan sansanonin mayaƙan musulunci, kuma babbar cibiyar Shahid Dr. Chamran. Kaɗan bayan shahadarsa ne aka sauya sunan jami’ar daga Jundishapur zuwa Jami’ar Shahid Chamran.
A halin yanzu jami’ar na da ɗalibai 15292 da malamai 1568. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙalar kimiyya 21042 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan kuma ta wallafa mujalla 23 na musamman, sannan ta karɓi baƙuncin taruka 67. Har ila yau, jami’ar ta wallafa maƙala 6011 a matakin ƙasa da ƙasa.
Martabar Jami’a
A sabon sakamakon tantancewa da martaba jami’o’i da cibiyoyin koyarwa na tsarin ISC (Islamic World Science Citation Center) na shekarar 2020/2021, jami’ar Shahid Chamran ta samu matsayi na 15 a tsakanin jami’o’in ƙasar Iran. A tsarin ranking na TIMES kuma ta samu matsayi na 1200-1500 a tsakanin jami’o’in duniya.
Makarantu da cibiyoyi
- Faculty of Science
- Faculty of Engineering
- Faculty of Literature and Humanities
- Faculty of Agriculture
- School of Veterinary Medicine
- Faculty of Educational and Sports Sciences
- Faculty of Education and Psychology
- Faculty of Mathematical Sciences and Statistics
- Faculty of Water and Environment
- Faculty of Theology and Islamic Studies
- Faculty of Economics and Social Sciences
- Faculty of Environment and Natural Resources
- Shushtar Faculty of Art
- Faculty of Earth Sciences
- Faculty of Archeology, Susa
Wuraren bincike
- Laser and Plasma Research Center
- Drilling Research Center
- Gas Supply Network Research Center
- Geology and Biological Sciences Research Center
- Azfa Center
- Computer Awareness, Support and Assistance Center
- Fast Processing Center
- Scientific Pole of Network Improvement and Maintenance
Kwasa-Kwasai
- Chemistry
- Physics
- Biology
- Genetics
- Department of Mechanical Engineering
- Department of Electrical Engineering
- Department of Computer Engineering
- Department of Metallurgical Engineering
- Department of Chemical Engineering
- Department of Architecture
- Department of Civil Engineering
- Department of Persian Language and Literature
- Department of English Language and Literature
- Department of French Language and Literature
- Department of History
- Department of Agriculture
- Department of Agricultural Machinery
- Department of Gardening
- Department of Herbal Medicine
- Department of Soil Science
- Department of Basic Sciences
- Department of Pathobiology
- Department of Food Hhygiene
- Department of Animal Nutrition and Breeding
- Department of Clinical Sciences
- Department of Educational Sciences
- Department of Psychology
- Depratment of Library and Information
- Department of Mathematical Sciences
- Department of Computer Science
- Department of Statistics
- Department of Hydrology and Water Resources
- Department of Water Structures
- Department of Irrigation and Drainage
- Department of Civil Engineering – Environment
- Department of Quran and Hadith Sciences
- Department of Fiqh and Islamic Law
- Department of Arabic Language and Literature
- Department of Economics
- Department of Business Administration
- Department of Accounting
- Department of Social Sciences
- Department of Law
- Department of Political Science
- Department of Painting
- Graphic Department
- Department of Geology
- Department of Geography and Urban Planning
Kuɗin makaranatra jami’ar Shahid Chamran
educational group | Grade | Annual tuition fee (Rials) |
---|---|---|
human | Masters | 327,600,000 |
human | PhD | 391,129,376 |
Engineering | Masters | 393,300,000 |
Engineering | PhD | 541,563,750 |
Science | Masters | 393,300,000 |
Science | PhD | 541,563,750 |
agriculture | Masters | 393,300,000 |
agriculture | PhD | 541,563,750 |
Mathematics | Masters | 327,600,000 |
Mathematics | PhD | 515,775,000 |
veterinary medicine | professional PhD | 300,868,750 |
veterinary medicine | PhD | 541,563,750 |
veterinary medicine | professional PhD | 661,911,250 |
Abubuwan more rayuwa na jami’ar
Jami’ar na da babban laburare mai ɗauke da fiye da taken littafai 20000 na musamman da na gama-gari a mabambantan kwasa-kwasai domin amfanin ɗalibai da malamai.
Jami’ar ta kuma yi tanadin abubuwa kamar hostel, wuraren wasanni, asusun tallafi, wuraren cin abinci, da sauransu duk domin samar wa ɗalibai walwala.
Kowace daga cikin makarantun jami’ar na da nata kayan aiki a keɓe domin sauƙaƙe shirya daurorin koyarwa da sauran tsare-tsare ga kowacensu.
Wuraren kwanan jami’ar
Jami’ar Ahvaz na da sassa biyu; ɗaya ita ce Jundishapur University of Medical Sciences wadda ta keɓanci ɗaliban likitanci, sai kuma Shahid Chamran University ta ɗaliban sauran fannoni. Jami’ar Shahid Chamran ta yi tanadin manyan hostel domin ɗalibanta maza da na mata.
Duka hostel ɗin suna wajen jami’ar ne amma wurin da suke kusa da jami’a ne sosai, akwai kuma motocin makaranta waɗanda ke jigilar ɗalibai zuwa hostel cikin sauƙi. Kodayake gine-ginen hostel ɗin sun tsufa, amma har yanzu suna da haske kuma a koyaushe cikin kula da tsaftarsu ake. Hostel ɗin suna da kusan cikakkun kayan aiki irin zauren wasanni, filin wasa, ƙaramar kasuwa, da gidan wanki. Hostel ɗin sun haɗa da hostel ɗin Alamul Huda, hostel ɗin Shohada, da hostel ɗin ɗaliban da suka kammala karatu (maza).
Yanayin Wuri
Jami’ar na unguwar Kuye Ostadan ta garin Ahvaz, a titin Saheli Gharbi. Jami’ar na kusa da wurare kamar Majid Icecream, Soma Fastfood, da Jundishapur University of Medical Sciences, da asibitin Golestan. Akwai tashar metro a bakin jami’ar wanda hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga ga waɗanda basu mallaki abun hawa ba.
Saduwa da Jami’a
Adireshi: Ahvaz, Bolvare Golestan, Shahid Chamran University of Ahvaz
Shafin jami’a: https://scu.ac.ir
Tambayoyi
- Wasu irin kayan aiki jami’ar Shahid Chamran take da su?
Jami’ar na da hostel, wuraren cin abinci, laburare, da sauransu. Mun yi cikakken bayani a cikin rubutunmu. - Miye alfanun karatu a wannan jami’a?
Tana da ranking mai kyau sannan kuma tana daga cikin jami’o’i masu daraja ta ɗaya. Za ku iya samun ƙarin bayani a cikin rubutunmu.