[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Karatu a Shahid Rajaee University

Karatu a Shahid Rajaee University

Loading

Jami’ar Shahid Rajaee jami’ar gwamnati ce a garin Tehranwadda ke ƙarƙashin ma’aikatar ilimi. Jami’a ce mai muhimmanci kuma ɗaya tilo a ƙasar wadda ke da alhakin samar da ma’aikatan fasaha na conservatory. Ba shakka wannan rubutun zai amfane ku idan kuna da nufin karatu a wannan jami’a, ku kasance tare da mu.

Gabatarwa

Jami’ar ta fara aiki a shekarar 1974 kafin ta koma ƙarƙashin ofishin kula da makarantun fasaha da sana’a na ma’aikatar ilimi a shekarar 1980. A tsakanin shekarar 1982 zuwa 1984, cibiyar horar da malamai ta Shahid Andarazgu wadda ke koyarda kwasa-kwasan addini da harshen larabci a matakin diploma a ƙarƙashin wannan jami’a.

Bayan wannan ne aka canja sunan zuwa “Islamic Revolution Center for Higher Technical Education” kuma aka ƙara kwas biyu na Technician Training da Technical Teacher a matakin Associate Degree, tare da karɓar lasisin yin kwas ɗin Technical Secretary a matakin Degree. A shekarar 1993 kuma, an assasa ofishin bunƙasa karatun gaba da sakandare a jami’ar bayan samun izini.

Bisa la’akari da kayan aiki da ƙwarewa ta wannan cibiyar, a shekarar 1997 aka karɓi izinin haɗe sassanta daga majalisar al’adu aka kuma nemi amincewar majalisar ƙoli ta sauyin al’adu, inda aka maida ita jami’a guda aka sanya mata suna Shahid Rajaee University sannan ta ci gaba da aiki a ƙarƙashin ma’aikatar ilimi.

Bincike ya nuna cewa jami’ar Shahid Rajaee ta wallafa maƙalar ilimi guda 6905 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, tare da maƙala 2154 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan ta wallafa mujalla 11 na musamman. Jami’ar Shahid Rajaee ta shirya taruka 31.

Karatu a Jami'ar Shahid Rajaee

Martabar Jami’a

Jami’ar Shahid Rajaee ta samu shiga jerin makarantun da tsarin ranking na TIMES ya tantance ne a shekarar 2020 inda ta zo a matsayi na 1000+ kuma tana da wasu ma’aunai na daban abun a duba. Misali ta samu matsayi na 1390 a ɓangaren ayyukan koyarwa, matsayi na 702 a ayyukan bincike, matsayi na 1400 a kima, da matsayi na 186 a kuɗin shiga (daga masana’antu).

Hakazalika a ranking ɗin jami’o’in cikin ƙasar Iran na shekarar 2021 wanda ya ƙunshi jami’o’in gwamnati guda 139, jami’ar Shahid Rajaee ta zo a matsayi na 31.

Kuɗin makarantar Jami’ar Shahid Rajaee

 

Makarantu

  • Faculty of Electrical Engineering
  • Faculty of Computer Engineering
  • Faculty of Civil Engineering
  • Faculty of Materials Engineering and Interdisciplinary Sciences
  • Faculty of Mechanical Engineering
  • Faculty of Architectural Engineering and Urban Planning
  • Faculty of Humanities
  • Faculty of Sports Sciences
  • School of Basic Sciences

Kwasa-Kwasai

  • Electronic Engineering
  • Power Engineering
  • Telecommunication Engineering
  • Control Engineering
  • Computer Architecture
  • Software and Information Technology
  • Artificial Intelligence
  • Civil Engineering – Structure and Earthquake
  • Civil Engineering – water
  • Geotechnic
  • Civil Engineering
  • Mapping Tendency
  • Biotechnology, Material Engineering
  • Wood Industry Engineering
  • Automotive Engineering
  • Solid Mechanics Engineering
  • Fluid Mechanics Engineering
  • Manufacturing Engineering
  • Architectural Engineering
  • Urban
  • Urban Design
  • Video Connection
  • Graphics
  • Education and Theology
  • English Language
  • Persian Literature
  • Educational Science
  • Sport Physiology
  • Movement Behavior
  • Sport Managment
  • Mathematics
  • Physics
  • Chemistry

Karatu a Shahid Rajaee University

Ƙungiyoyi da Cibiyoyin Bincike

  • Science and Engineering Education Research Center
  • New Technologies Research Institute
  • Scientific Association of Environmental Education
  • Specialized Science Education Library

Wasu daga cikin ɗakunan gwaje-gwaje:

  • Process Control Laboratory
  • Microelectronics Laboratory
  • Data Analysis Laboratory
  • Power Electronics and New Energy Laboratory
  • Research and Development Laboratory of Software Systems
  • Fuel Cell Laboratory
  • Laboratory of Neurological and Cognitive Sciences
  • Laboratory of New Technologies
  • Advanced Nanocomputing Laboratory
  • Geotechnical Engineering Laboratory
  • Structural Engineering and Earthquake Laboratory

Ababen More Rayuwa

  • Amphitheater
  • Buffet
  • Restaurant
  • Cibiyar Wallafa
  • Swimming Pool
  • Zauren wasanni
  • Banki
  • Laburare
  • Filin wasa mai haki
  • Filin wasan tennis
  • Ɗakin gwaje-gwaje (laboratory)

Wuraren kwana

  • Wurin kwana na Harvey (na mata)
  • Wurin kwana na Mubarakabad (na mata)
  • Wurin kwana na Azgol (na maza)
  • Wurin kwana na Tarasht (na maza)
  • Wurin kwana na Hafez (na maza)
  • Wurin kwana na Shahid Madani (na maza)
  • Wurin kwana na Ikhtiyarie (na mata)

Karatu a Shahid Rajaee University

Yanayin Wuri

Jami’ar na nan a unguwar Lavizan, arewa maso gabacin garin Tehran. Adireshi: Tehran – Lavizan – Titin Shahid Sha’abanloo – Shahid Rajaee University. Ana iya amfani da metro, autobus, ko taxi wurin zirga-zirga zuwa jami’ar.

  • Tashar Metro ta Shahid Rajaee: Tashar metro ta Hoseinabad wadda ke layin dogo na 3, ita ce tashar metro mafi kusa da jami’ar wadda tazarar ta da jami’ar bai wuce tafiyar kilomita 2 ba.
  • Tashar bus ta Jami’ar Rajaee: Za mu iya cewa amfani da autobus ya fi sauƙi ga ɗalibai da malamai. Idan kuka sauka a tashar bus ta Chaharsad Dastgah Lavizan, nisan da ya rage zuwa ƙarasawa jami’a bai wuce mita 300 ba.

Idan kuma kuna da abun hawa na kanku ne to zai fi sauƙi ku bi ta babban titin Imam Ali (arewa). Idan kuna buƙatar taswirar jami’ar Shahid Rajaee, za ku iya sauke wannan manhaja ta hanyar danna link ɗinnan na ƙasa. ga lambar wayar jami’ar idan kuna da buƙatar kiransu kai-tsaye.

Adireshi: Tehran – Lavizan – Titin Shahid Shaaban loo – jami’ar Shahid Rajaee .

Shafin jami’a; https://www.sru.ac.ir

 

 

Related Posts
Leave a Reply