Ita dai wannan jami’a ta Shahed jami’a ce ta gwamnati kuma ingantatta a garin Tehran wadda ta fara aiki a shekarar 1990 a ƙarƙashin kulawar Bonyade Shahid. Jami’ar Shahed na karɓar ɗalibai a matakin digiri, masters, da PhD. Ba shakka za ku samu ribar yin karatu a wannan jami’a ta Shahed.
Gabatarwa
Jami’ar Shahed ta fara aiki ne bayan umarnin Imam Khomeini (QS) da ya bayar a ranar 26 ga watan March na shekarar 1986 na cewa lazim ne a samar da tsarin kula da al’amuran al’adu da karatun ‘ya’yan shahidai, shahidai masu rai, da mafƙudan juyin musulunci na Iran da yaƙin kare ƙasa, a sannan ne aka shiga faɗi-tashi na samar da tsarin karatu mai zurfi da bincike inda tsarin ya fara aiki da karɓar ɗalibai 165 a fannoni 7, a watan September na shekarar 1990. Wannan jami’a ta Shahed ita kaɗai ce jami’a ɗaya tilo a cikin jami’o’in da suka cika sharuɗa wadda ke ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya da ma’aikatar ilimi a lokaci guda, kuma take ɗaukar ɗalibai ta hanyar la’akari da wasu abubuwa daban baya ga jarabawar shiga ta ƙasa.
A halin yanzu akwai ɗalibai 5000 da malamai 325 a wannan jami’a ta Shahed. Bayanai sun tabbatar da cewa jami’ar ta wallafa maƙalar kimiyya guda 7139 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, tare da maƙala 5052 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan ta wallafa mujalla 13 na musamman, ta kuma shirya taruka 4 zuwa yanzu. A shekarar 2023, mawallafan wannan jami’ar sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu da kalmomin “students” da “self-motivation” a matsayin muhimman kalmomin maƙala.
Martabar Jami’a
Tsarin ranking na Scimago ya fi maida hankali wurin ranking ɗin jami’o’in America, China, da Japan, amma saboda matsayin ilimi na wannan jami’ar ta Shahed, ita ma ta samu shiga wannan tsari. Jami’ar Shahed ta Tehran ta samu matsayi na 36 a tsakanin jami’o’in Iran, da matsayi na 2793 a tsakanin fitattun jami’o’i na duniya.
A tsarin ranking na Times wanda yana ɗaya daga cikin sanannu kuma ingantattun tsarukan ranking na duniya, sakamakon da wannan tsarin ya fitar na shekarar 2022 ya tantance jami’o’i 1396 a matsayin waɗanda suka yi fice daga ƙasashe 92 na duniya. Tsarin ya yi la’akari ne da abubuwa 5 kamar haka; ingancin karatu, bincike, taskace bayanai, daraja a idon duniya, da kuɗin shiga daga masana’antu. Jami’ar Shahed ta samu matsayi na 1000+ a wannan ranking.
Kuɗin Makarantar Jami’ar Shahed
Makarantu
Faculty of Technical Engineering
Kwalejin Technical Engineering ya fara aiki ne a shekarar 1994 da nufin horar da ƙwararrun ma’aikata da ake buƙata a ɓangaren Electrical Engineering, Computer Engineering, da Medical Engineering, bayan samun lasisin ma’aikatar ilimi. Zuwa yanzu wannan kwalejin ya ƙarɓi ɗalibai a zango 13 na karatu, sannan ya yaye ɗalibai a zango 8.
School of Basic Sciences
Makarantar Basic Sciences ta jami’ar Shahed ta fara aiki a hukumance a shekarar 1990 da nufin horar da masana a sashen Mathematics bayan samun lasisin ma’aikatar ilimi. A shekarar 1993 wannan makarantar ta faɗaɗa ayyukanta na koyarwa a matakin digiri ta hanyar samar da department ɗin Biology, da department ɗin Physics a shekarar 2000. Daga nan kuma a shekarar 2006 ta fara karɓar ɗalibai a fannin Applied Mathematics da Animal Science – reshen physiology a matakin masters, da Microbiology a matakin PhD.
Faculty of Humanities
An buɗe wannan kwalejin ne a shekarar 1990 da hadafin horar da ƙwararru a fannonin Human Sciences bayan karɓar lasisin ma’aikatar ilimi.
Faculty of Agricultural Sciences
An assasa kwalejin Agriculture na jami’ar Shahed a shekarar 1991 kuma a halin yanzu a matakin digiri ana yin waɗannan fannonin na Agricultural Engineering a cikinta: Cultivation and Improvement of Plants, Horticultural science, Medical Plants, da Soil Science. A matakin masters kuma ana yin Agriculture, Entomology, da Agricultural Biotechnology.
Faculty of Medicine
Makarantar likitanci ta wannan jami’a ta fara aiki a shekarar 1992 da nufin horar da amintattun likitoci kuma ta fara aiki ne da ɗalibai 48.
Wannan kwalejin na da membobin tsangayar ilimi 78. 36 daga cikinsu membobi ne a fannin Basic Sciences, 42 kuma membobin Clinical Sciences. Haka kuma akwai malaman wasu jami’o’in da ake gayyatowa a basu lasisin koyarwa domin a amfana da su a ɓangaren koyarwa da ayyukan bincike. Kwalejin na da cibiyoyin koyarwa na jinya guda biyu kamar haka; Shahid Mostafa Khomeini da Hazrat Zainab (as).
Faculty of Art
Ita kuma ta fara aiki ne a shekarar 1990 bayan samun lasisi daga ma’aikatar ilimi, da nufin horar da ƙwararrun ma’aikata a ɓangaren al’adu bisa la’akari da siyasar jamhuriyar musulunci ta Iran.
Dental College
Wannan kwalejin ya fara aiki a hukumance ne a shekarar 1991 da nufin horar da ɗaliban likitanci na ɓangaren haƙori domin rigakafi da magance matsalolin haƙori da na baki, a matakin PhD bayan samun lasisin hukumar kiwon lafiya.
Bayanai sun nuna cewa ɗaliban da suka karanci wannan fanni a wannan jami’a suna daga cikin ƙwararrun likitocin haƙori da ake ji da su a ƙasar, domin suna gudanar da ayyukansu cikin gogewa da tsantsar ƙwarewa a ciki da wajen ƙasar Iran. A halin yanzu ana yin kwas 7 a cikin wannan kwalejin.
School of Nursing and Midwifery
An buɗa school of nursing ta jami’ar Shahed a shekarar 1990 da nufin horar da malaman jinya da ungozoma bayan samun lasisi daga hukumar lafiya. Tsawon lokacin karatu a wannan makarantar zango 8 ne.
Ƙungiyoyi da Cibiyoyin Bincike
- New Science and Technologies Research Institute
- Immune Response Regulation Research Center
- Neurophysiology Research Center
- Molecular Microbiology Research Center
- Traditional Medicine Research Center
- Medicinal Plants Research Center
- Geriatric Care Research Center
- Acoustic Research Group
- Family Health Research Group
Kwasa-Kwasai
- Pharmacology
- Iranian Traditional Medicine
- Medicine
- Health Economics
- Immunology
- History of Medical Sciences
- Medical Physiology
- Bacteriology
- Geriatric Nursing
- Special Care Nursing
- Surgery Room
- Nursing
- Dental
- Specialized Assistance
- Oral and Maxillofacial Diseases and Dental Prostheses
- Pediatric Dentistry
- Periodontics
- Dentistry – endodontics
- Orthodontics Dentistry
- Restorative Dentistry
- Clinical Psychology
- Law
- Information Science and Epistemology
- Social Sciences
- Educational Science
- Political Science
- Islamic Jurisprudence
- Librarianship
- Business Management
- Industrial Management
- Physical Education – physical education and sports science
- Theology and Islamic Sciences
- Agricultural Biotechnology (Masters)
- Agricultural – Ecological Engineering (Agroecology)
- Agricultural Engineering – Plant Breeding (Masters)
- Agricultural Engineering – Seed Technology (Masters)
- Agricultural Engineering – soil science
- Entomological Agricultural Engineering (Masters)
- Agricultural Engineering – Horticultural Sciences – fruit work
- Agricultural Engineering (Masters)
- Agricultural Engineering – Entomology- ecology and biological control
- Agricultural engineering – Entomology – toxicology
- Agricultural Engineering – Entomology-systematics of insects
- Agricultural Engineering – Entomology-entomology
- Electrical Engineering
- Electrical Engineering – Control
- Electrical Engineering – Electronics
- Electrical Engineering – Power
- Electrical Engineering – Telecommunications
- Medical Engineering – Bioelectricity
- Civil Engineering
- Computer Engineering (hardware)
- Mathematics and Applications
- Computer Science
- Cell and Molecular Biology (genetic and biotechnology trends)
- Animal Life
- Public Life
- Solid State Physics
- Pure Mathematics
- Art Research (P.H.D)
- Comparative and Analytical History of Islamic Art (P.H.D.)
- Video Communication (Masters)
- Art Research (Masters)
- Illustration (Masters)
- Painting (Masters)
- Islamic Art – Painting (Masters)
- Writing and Painting
Ababen More Rayuwa
Ɗaya daga cikin abubuwan da ke jan hankalin ɗalibai zuwa wannan jami’a shi ne kayan aiki da yanayi na musamman da jami’ar ta yi tanadi wa ɗalibanta. Hadafin assasa wannan jami’a shi ne samar wa koyarwa da horar da ɗalibai, don haka ne jami’ar ta yio tanadin abubuwa kamar haka:
- Cikakkun kayayyaki da tsarukan karatu kamar shirya keɓantattun daurorin ilimi
- Ɗaga darajar ilimi a matakai daban-daban na karatu domin yaye ɗalibai masu himma
- Amfani da ɗalibai wurin gudanar da ayyukan bincike da gwaje-gwaje na ƙasa domin ƙara musu tajaruba
- Shirya daurorin sake, na online da na dare ga sauran ɗalibai
- Samar da abubuwan wasanni ga ɗaliban da ke sha’awar karantar fannin wasanni ko shiga gasannin yanki ko na ƙasa
- Bada masauki ga ɗalibai (hostel) ɗauke da kayan amfani
- Bayar da ingantacciyar takardar shaida ga waɗanda suka zana jarabawoyin ƙarshe na kwasa-kwasan musamman kuma suka yi nasara
Laburaren Jami’a
Jami’ar ta Shahed ta yi tanadin laburare na musamman don amfanin ɗalibai da malamanta, wanda ta inganta shi da litattafai da resources tare da kayan aiki na zamani. Babban laburaren jami’ar na da duka litattafan da suka shafi kwasa-kwasan da ake yi a jami’ar, sannan ɗalibai na da damar amfani da littafan da ke ciki, ko su karɓi aro. Bayan ɗalibai sun yi rijista da laburaren, suna iya gani ko su karanta ayyukan bincike da sauran ɗalibai suka gabatar a baya.
Hostel
Kamar sauran jami’o’in gwamnati, ita ma jami’ar Shahed tana da hostel ɗauke da kayan aiki wanda ta tanada don amfanin baƙin ɗalibai wanda ɗaliban digiri za su iya zama ciki maƙura shekara 4 wato zangon karatu 8, ɗaliban masters kuma maƙura zango 4 (shekara 2), ɗaliban PhD ko ɗaliban masters masu karatun fannonin likitan haƙori shekara 6, ɗaliban likitanci kuma shekara 7.
Yanayin Wuri
Jami’ar Shahed na nan a unguwar Islamshahr a titin Derakhti. Jami’ar na kusa da wurare kamar Namayeshgah Beynulmelali Shahr Aftab, da Post office na Shahr Aftab. Tashar bus mafi kusa ita ce tashar bus ta Shahr Aftab, hakan zai sauƙaƙe zirga-zirga ga waɗanda ba su da abun hawa.
Adireshi: Tehran, babbar hanyar Khalije Fars daura da haramin Imam Khomeini (R), Shahed University.
Shafin jami’a: https://shahed.ac.ir