Jami’ar Fasahar Zane-Zane ta Iran (Iran University of Art) ita ce makarantar gaba da sakandare mafi girma a fannonin da suka shafi art a birnin Tehran. An samar da ita ne ta hanyar haɗe makarantu biyar na art na gabanin juyin musulunci na Iran (makarantun Farabi University, Decorative Arts College, Dramatic Arts College, Higher Music School, da National Music Academy). A wannan rubutun, mu kawo muku wadataccen bayani game da yanayin karatu a wannan jami’a mai suna Iran University of Art.
Gabatarwa
Iran University of Art jami’a ce da ta keɓanci fannonin zane-zane wato art. An assasa ta a shekarar 1979 bayan haɗe makarantu guda biyar na art kamar haka; Farabi University, Decorative Arts Academy, Dramatic Arts College, Higher Music School, and National Music Academy.
Daga cikin waɗannan makarantun da aka haɗe, Higher Music School ita ce mafi daɗewa. Ta tsaya da ƙafafuwanta ne bayan an ware ta daga Darul Funun a shekarar 1918 a matsayin ajin koyar da waƙe. Gholamreza Minbashian, shi ne wanda ya ci gaba da tafiyar da ita tare da taimakon ɗansa Nasr al-Sultan a ƙarƙashin kulawar ma’aikatariIlimi, shi ne ya sanya mata suna “Music School”.
Bayan nasarar juyin musulunci, domin cimma manufofin al’adu da na fasahar zane-zane na al’ummar musulmi da bunƙasa fasahohin zane musamman na musulunci da na gargajiya, tare da ilmantar da waɗannan ƙwararrun game da tsofaffin al’adun Iran, musulunci, da na duniya, kafa wata cibiya ta karatun gaba da sakandare a fannin art ya shiga cikin ƙudurin ma’aikatara ilimin kimiyya. A domin haka haɗe waɗannan makarantun guda 5 na kafin juyin juya hali, aka assasa wannan jami’a ta fasahar zane-zane a shekarar 1979, inda ta fara aiki a hukumance shekarar 1983.
atu
Kuɗin Makarantar Iran University of Art
Makarantu
Makarantar Applied Arts
An kafa wannan kwalejin a shekarar 1960 ta hannun majalisar al’adu da fasaha ta lokacin. Asasin karatu a kwalejin ya ginu ne a kan manufar muhimmantar da ilimin fasahar zane-zane tare da la’akari da al’adun ƙasar. Saboda haka ne aka fi bada ƙarfi a fannoni irin su textile weaving and printing, decorative painting, ceramics (pottery), visual communication, interior architecture, da sauransu. Tun bayan canja sunan jami’ar zuwa “Iran University of Art”, kwalejin na Applied Arts ya ci gaba da gudanar da ayyukansa da kwasa-kwasai guda uku na Industrial Design, Handicrafts, da Music, a matakin Bachelor’s Degree.
Kwalejin Visual Arts
Wannan kwalejin na Visual Arts an assasa shi ne a shekarar 1978 a cikin kamfushin jami’ar ta Iran University of Art, sannan aka dawo da wasu sassan koyarwa da ke ƙarƙashin kwalejin Decorative Arts na jami’ar Farabi zuwa wannan kwalejin. A shekarar 1982, kwalejin ya fara karɓar ɗaliban makarantun da aka haɗe aka assasa wannan jami’a, waɗanda suka saura da abunda bai wuce unit 25 su kammala karatunsu ba. Tun daga shekarar 1983 wannan kwalejin ya ci gaba da koyar da kwasa-kwasai uku na Photography, Painting, da Visual Communication a matakin undergraduate.
Kwalejin Cinema and Theater
A shekarar 1957 ne daraktan ƙoli na Fine Arts ya bayar da lasisin assasa department ɗin Dramatic Arts. An assasa makarantar ta Dramatic Arts a shekarar 1964 bayan amincewar majalisar al’adu da fasahar zane ta ƙasa. Manufar wannan makaranta ita ce horar da mutane masu basira a duka fannonin Theater, fannonin da suka haɗa da rubutu, bada umarni, wasan kwaikwayo, kwalliya, da shirya dandali. A hankali aka shigar da sassan koyarwa na Cinema da Television a wannan kwalejin, a shekarar 1970 kuma aka canja masa suna zuwa “Kwalejin Dramatic Arts” inda ya ci gaba da gudanar da ayyukansa.
Kwalejin Music
Bayan haɗe waɗannan manyan makarantun, ciki har da Music High School (1959) da Music Academy (1971) inda aka samar da jami’ar fasahar zane ta Iran, an fara kwas ɗin Music ne a shekarar 1989 a ƙarƙashin kwalejin Applied Arts. Bayan samun izini daga majalisar bunƙasa karatun gaba da sakandare a shekarar 1994 ne aka buɗe kwalejin Music a matsayin kwaleji na farko (da ke ƙarƙashin jami’a) a ƙasar Iran, inda aka fara da kwas biyu na Music da Military Music, a matakin undergraduate. Kwalejin na nan cikin harabar Karaj ta jami’ar.
Makarantar Architecture and Urban Planning
Kwalejin Architecture da Urban Planning ta Iran University of Art ta fara ayyukanta a shekarar 1999 ta hanyar karɓar ɗaliban undergraduate a fannin Urban Planning, sannan a shekarar 2000 a fannin Architecture. Kwalejin tana da yalwar murabba’in mita 2,600 a harabar Karaj. Bayan bunƙasar kwalejin, an fara karɓar ɗaliban graduate a fannin Architecture, a shekarar 2004 kenan, sai kuma Interior Architecture a shekarar 2005.
Kwalejin Dramatic Arts
Ganin muhimmancin fasahar kwaikwayo (dramatic arts) a wajen gina tunanin matasa, tushen al’adu da zamantakewar al’umma, da kuma buƙatar ci gaban gaggawa a fannin wasan kwaikwayo, fina-finai, talabijin, da rediyo, tsohuwar Ma’aikatar Al’adu da Fasaha ta kafa babbar makaranta domin horar da ‘yan wasan kwaikwayo da masu bincike a waɗannan fannoni. An kafa Sashen Dramatic Arts a shekarar 1957 ta hannun Hukumar Kula da Fasaha ta Fine Arts, ƙarƙashin jagorancin Dr. Mehdi Forough.
Kwalejin Decorative Arts
An kafa wannan kwalejin ne a shekarar 1960 lokacin da aka ƙirƙiri makarantar Fine Arts Academy, ƙarƙashin Ma’aikatar Al’adu da Fasaha. An kafa makarantar ne a matsayin tanadi ga buƙatun ilimi na ɗaliban fasaha da sauran waɗanda ke sha’awar ci gaba da karatu a fannin na fasaha, da kuma taskacewa da haɓaka sauran fasahohi masu alaƙa da fannin.
Makarantar Conservation and Restoration
An fara karatun digirin master’s a fannin Kula da Gine-gine da Kayan Tarihi (Conservation of Historic Buildings and Cultural Objects) a jami’ar Iran University of Art a shekarar 1976, wanda ya zama wani muhimmin mataki a tarihin karatun gaba da sakandare a wannan fannin a ƙasar Iran. A shekarar 1977, an sanya hannu a yarjejeniyar ilimi tsakanin Dr. Jamshid Behnam, shugaban Farabi University a lokacin, da Nosratollah Mojtabai, daraktan gudanarwa na Hukumar Kula da Kayan Tarihi ta ƙasa, domin samar da ma’aikatan fasaha da ƙwararru. Wannan ne mafarin karɓar ɗalibai a matakin master’s na kwas ɗin Conservation a Farabi University (Iran University of Art ta yanzu).
Makarantar Theoretical Sciences and Advanced Art Studies
Girman da zurfin muhawarorin fasahar zane, da mahimmancinsu a zamanin yanzu tare da ƙarin buƙatar gudanar da bincike da karatu mai zurfi kan fasahar Iran da ta duniya, dangantakar addini, al’adu da fasaha, ƙoƙarin shawo kan ƙalubalen falsafa a fannin fasaha, da kuma rawar da Iran University of Art take takawa a matsayin cibiyar ilimin fasaha mafi girma a Gabas ta Tsakiya, su suka haifar da kafuwar wannan kwalejin na Theoretical Sciences and Advanced Art Studies a watan May na shekarar 2015, tare da shiri wanda ya ƙunshi manufofi, dabaru, da hanyoyin aiki na musamman.
Kwasa-Kwasai
- Islamic Art
- World Music Performance – Guitar
- Iranian Music Performance
- Theater – Directing
- Puppetry
- Theater – Acting
- Painting
- Architecture and Energy
- Architectural Engineering
- Architecture
- Museum Studies
- Restoration of Cultural and Historical Objects
- Project and Construction Management
- Carpet – Restoration and Finishing
- Composition
- Dramatic Literature
- Urban Planning
- Cinema
- Cinema – Editing
- Cinema – Cinematography
Da sauransu…
Abubuwan More Rayuwa
Ana fifita ɗalibai cikakku (full-time) waɗanda ba mazauna Tehran ba wajen raba ɗakunan kwana, sai kuma ɗalibai na wucin gadi (part-time). Ɗaliban da ke harabar makaranta waɗanda ba su sami damar amfani da hostel ɗin makaranta ba za su iya amfani da hostel masu zaman kansu, masu sauƙin farashi. Ana bayar da karin kumallo da abincin dare a hostel, kuma ana rajista ne ta hanyar tsarin abinci da jami’ar ta tanada. Ɗalibai ne ke zaɓar nau’in abincin da suke so, hakazalika akwai isassun kayan more rayuwa a hostel ɗin na makaranta.
A Iran University of Art, an samar da kayan aiki na ilimi ga ɗalibai a fannoni daban-daban. Wannan ya haɗa da ɗakunan karatu da ɗakunan kwamfuta da aka tsara musamman don tallafa wa karatun ɗalibai. Ɗaliban master’s a fannin animation na kwalejin Cinema and Theater suna da damar yin amfani da kayan aikin da suka dace da buƙatun karatunsu. Babban laburaren jami’ar yana da ɗakin karatu mai kyau da kuma tsarin ba da aron littattafai. Har ila yau, ɗalibai suna da damar amfani da fitattun ɗakunan karatu na dijital na duniya, kamar EBSCO. Bugu da ƙari, an samar da intanet mai sauri ga ɗalibai, sannan akwai damar musayar projects tare da jami’o’in ƙetare masu daraja. Ana fifita ɗalibai a irin waɗannan ayyukan bisa cancantarsu, ayyukansu, da kuma ƙwarewarsu a harshen Turanci.