[gtranslate]
تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Bushehr

Karatu a Bushehr

Loading

Bushehr gari ne a iyakar ƙasar Iran kuma shi ne cibiyar lardin Bushehr. Me yiwuwa karatu a Bushehr ya keɓantu da wasu abubuwa na musamman. Ku kasance tare da mu.

Karatu a Bushehr

Bushehr

An samu kimanin mutane 223,504 a garin Bushehr a aikin ƙidaya da aka yi a shekarar 2016, shi ne gari mafi yawan jama’a a lardin Bushehr kuma shi ne gari na 4 mafi yawan mutane a kudancin ƙasar Iran. Da yake garin Bushehr tsibiri ne, yana da hanya ta tudu ne kawai ta gabacinsa. Garin Bushehr na da tsayin mita 18 daga saman teku kuma yana da yanayi kusan irin na hamada.

Garin Bushehr na da tsufan kusan shekara dubu biyar kuma ya kasance daga cikin muhimman wurare a mabambantan dauloli. A zamanin daular khalifa na biyu (Umar), musulmi sun ci garin Reyshahr (Bushehr ta da) a wani yaƙi mai suna “Waƙi’ar Reyshahr”. Abu Mohayari ɗa a wurin Sheikh Nasirkhan Ale Mazkour, shi ne ya kafa garin Bushehr na yanzu a shekarar 1735. Tun ƙarnonin da suka shuɗe saboda muhimmancin wannan garin, an samar da abubuwa da yawa a cikinsa. Misali; cibiyar wallafa ta dutse, masana’antun lantarki, gidan ƙanƙara, da layin wayar tarho.

A littafai da sanadodin tarihi, an sajjala sunaye mabambantan sunaye na wannan gari. Sunaye irinsu; Ram Ardashir, Abushahr, Bukht Ardsshir, Liyan, da Reyshahr.
Da yawan mutanen garin Bushehr suna magana ne da harshen farisanci da lahajar ‘Bushehri’. Saboda abubuwa irin kamun kifi (Su), sansanin makamashin nukiliya, ƙera jiragen ruwa, sufuri, da sauransu, an samu haɓakar tattalin arziki da yawa ta dalilin wannan iyakar ta ruwa.

Karatu a Bushehr

Zirga-Zirga

Filin jirgi

An samar da filin jirgin ƙasa da ƙasa na garin Bushehr a shekarar 1919 wanda kenan yanzu ya cika ƙarni guda da assasawa. A baya wannan filin jirgin ya kasance ɗaya daga cikin jiga-jigan filayen jirgin Iran guda biyu, ta yadda a nan jiragen wasu manyan kamfanonin jirage na duniya irinsu British Airways na ƙasar England da KLM Holand ke sauka a Iran. An ce a nan aka sauke jiragen sama na farko da aka sayawa sojojin ƙasar Iran a shekarar 1924, daga nan kuma aka aika su zuwa sauran sassan ƙasar.

Daga wannan filin jirgi na Bushehr, jirage na zuwa ƙasashen Iraq, Syria, Saudi Arabia, da ƙasashen yankin persian gulf irin su UAE.

Jiragen cikin gida kuma sun haɗa da jiragen Tehran, Shiraz, Isfahan, Mashhad, Tabriz, Kharg, Rasht, Bandar Abbas, da Kish.

Tafiya da yawon buɗe ido ta ruwa

Garin Bushehr na da wata tashar ruwa ta ƙasa da ƙasa wadda kuma ana amfani da ita a matsayin tashar Bushehr – Kharg. Hakazalika mas’ulan wannan lardin na Bushehr na kan bibiyar yadda za a samar da hanyar ruwa daga Busher zuwa Qatar, kodayake har yanzu ba su kai ga natija ba.

Layin dogo

A wuraren shekarar 1919, turawan Ingila sun samar da wata hanyar jirgin ƙasa daga Bushehr zuwa Borazjan saboda wasu manufofin soji. Turawan sun yi wani tayi ga hukumomin lardin Bushehr cewa suna so su sayar da wannan hanyar ta jirgin ƙasa; amma kasantuwar cewa hukumomin ba su da yanayin da za su iya sayen hanyar, turawan suka kwashe kayan wannan layin jirgin ƙasan suka kai su Basara ta Iraq.

Bus da motocin Taxi na cikin gari

A halin yanzu akwai tashar bus guda ɗaya a kudu maso gabacin garin Bushehr wadda ake amfani da ita saboda zirga-zirgar ciki da wajen gari, a hanyar Borazjan – Bushehr. Akwai kamfanoni 11 da motocin bus 120 da taksi 110 masu aikin jigilar fasinjoji a wannan tashar. A shekarar 2022 aka fara aikin gina hanyar jirgin ƙasa ta Shiraz – Bushehr da sharaɗin cewa duka aikin hanyar jirgin ƙasa ta Shiraz – Bushehr – Asaluyeh yana buƙatar bashin kimanin Toman Biliyan 40, wanda za a biya daga asusun mahaƙar mai a cikin shekaru 3.

Bus da Taxi na cikin gari

A halin yanzu dukda ɓarkewar cutar Corona, akwai motocin bus na cikin gari guda 30 masu yawo a hanyoyi 11. Hakazalika akwai motocin taksi kusan 400 na cikin gari, kodayake guda 200 kawai ke aiki yanzu. Har ila yau akwai tsarin online taksi a garin Bushehr.

Karatu a Bushehr

Manyan cibiyoyin koyarwa da jami’o’i

  • Persian Gulf University
  • Bushehr University of Medical Sciences
  • Al-Zahra University
  • Bushehr University of Applied Sciences
  • Islamic Azad University, Bushehr Alishahr
  • Islamic Azad University Science and Research Branch Bushehr
  • Payame Noor University of Boushehr Branch
  • Boys’ Technical College of Bushehr
  • Bentul Hoda Sadr Tarbiat Moallem Center Bushehr
  • Lian Institute of Higher Education Bushehr
  • Kherad Institute of Higher Education Bushehr
  • Sama Technical and Vocational College Bushehr
  • Allameh Tabatabaei University of Farhangian Bushehr
  • Imam Khomeini Religious Seminary Bushehr
  • Bushehr Applied Scientific University of Culture and Art

Asibitoci

Wasu daga cikin asibitocin Bushehr:

  • Asibitin Shohadae Khalije Fars
  • Asibitin Fatima Zahra (AS)
  • Asibitin Zuciya na Bushehr
  • Asibitin Bintul Huda, Bushehr
  • Asibitin Air Base (Asibitin Amirul Muminin)
  • Asibitin Nuclear Power Plant ta Bushehr
  • Asibitin Salaman Farsi, Bushehr
  • Asibitin yara na Ali Asghar, Bushehr
  • Dey Surgery Center
  • Asibitin Qa’em
  • Asibitin Khatamul Anbiya

Hotel Hotel da masaukai

  • Siraf Hotel (titin Imam Khomeini)
  • Delvar Tourist Hotel : Meidane Rais Ali Delvari
  • Parvaz Hotel: Titin Saheli, daura da Marjan Park
  • Asman Hotel: Bushehr. Titin Hafez Junubi
  • Padargad Hotel: Bushehr. Titin Imam Khomeini
  • Iran Mehmansara: Titin Safawi
  • Sa’adi Mehmansara: Titin Hafez
  • Kasri Mehmansara: Titin Nader
  • Ghasr Talaei Mehmansara: Titin Lian
  • Yas Hotel: Titin Ashouri
  • Jazire Hotel: Koe Bandar
  • Varzesh Hotel: Titin Varzesh
  • Plus Hotel: Mararrabar Kashtirani

Karatu a Bushehr

Abubuwan buɗe ido

  • Reyshahr
  • Rizabuwar ruwa ta Qawwam
  • Gidan Qazi
  • Fadar Dahdashti
  • Makarantar Golestan
  • Bafte Bushehr
  • Fadar Kulah Farangi
  • Gidan Golshan
  • Cocin Aramneh Grigori
  • Maƙabartar turawa
  • Ƙabarin Janaral
  • Gidan Kouti
  • Makarantar Sa’adat
  • Gidan Malek
  • Hubbaren Isfahani
  • Gidan bauta na Khoda Darya
  • Cocin Masih Moghaddas
  • Qal’e Holadiha
  • Majami’ar Yahudawa
  • Gidan Haj Ra’is

Karatu a Bushehr

Kamar yadda muka ambata, akwai manyan jami’o’i masu yawa a wannan gari na Bushehr irinsu Jami’ar Khalije Fars.

Kawai jimillar jami’o’i da cibiyoyin koyarwa 23 a lardin Bushehr. Jami’o’in wannan lardi sun keɓantu da mujallu 5 na musamman na ilimi kuma zuwa yanzu sun wallafa mujalla 130. Lardin Bushehr ya karɓi baƙuncin tarukan ilimi guda 15 zuwa yanzu. Masu bincike na lardin Bushehr sun wallafa maƙalolin ilimi guda 16203 ciki har da maƙalolin mujalla guda 2555 da maƙalolin taro guda 9544 da wani adadi na maƙalolin ƙasa da ƙasa.

 

Related Posts
Leave a Reply