[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Arak University of Medical Sciences

Karatu a Arak University of Medical Sciences

Loading

Jami’ar likitanci ta Arak (Arak University of Medical Sciences) ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati dake lardin tsakiyar Iran wadda take cikin garin Arak, jami’ar na ɗaya daga cikin jami’o’in da ke ƙarƙashin hukumar lafiya, kuma ita ke da alhakin gabatar da ayyukan kiwon lafiya da jinya a lardin, da gudanar da bincike a kan abubuwan da suka shafi likitanci, tare da horar da ma’aikatan kiwon lafiya.

Gabatar da Arak University of Medical Sciences

An karɓi lasisin assasa jami’ar ne a shekarar 1986 bisa ƙoƙarin shugaban hukumar kula da lafiya da magani na lardin, da wakilin mutanen Arak a majalisar ƙoli ta musulunci na lokacin, a watan January na shekarar 1988, da taimakon jami’ar likitanci ta Shahid Beheshti aka haɗe kwalejin likitanci
da makarantar jinya, aka samar da babbar makarantar likitanci
wadda ta fara aiki da ɗalibai 60 a fannin likitanci, a wani muhalli na haya.

Ta fara cin gashin kanta a shekarar 1989; a shekarar 1990 kuma aka maida ita jami’ar likitanci. An sanya mata sunan Arak University of Medical Sciences ne a shekarar 1995 inda aka haɗe ta da cibiyar kiwon lafiya ta yankin, sannan ta karɓi ragamar ayyukan kiwon lafiya da magani na lardin.

A halin yanzu jami’ar na da ɗalibai 3471 da malamai 229. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu, wannan jami’a ta wallafa maƙalar ilimi guda 862 a wallafe-wallafe da taruka na cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo, ta wallafa mujalla 3, sannan ta shirya taro 1 zuwa yanzu.

Arak University of Medical Sciences

Martabar Jami’a

Arak University of Medical Sciences ta yi nasarar samun matsayi na 401-500 a tsarin ranking na Times, a shekarar 2023.

Makarantu

_ School of Medicine
_ School of Dentistry
_ Faculty of Rehabilitation
_ School of Nursing
_ School of Paramedicine
_ School of Health
_ Shazand School of Nursing
_ Arak Higher Education Health Complex

Wurare da Cibiyoyin Bincike

_ Traditional and Complementary Medicine Research Center
_ Medical and Molecular Research Center
_ Infectious Diseases Research Center

Asibitocin da cibiyoyin jinya na koyarwa

_ Hazrat Waliasr (AS) Educational and Therapeutic Center
_ Amirkabir Educational and Treatment Center
_ Amirul Munin Educational and Medical Center
_ Ayatollah Khansari Educational and Therapeutic Center
_ Ayatollah Taleghani Educational and Therapeutic Center
_ Special Clinics
_ Asibitin Walfajr Tafaresh
_ Asibitin Imam Ali (AS), Kamijan
_ Asibitin Imam Sajjad (AS), Ashtian
_ Asibitin Imam Sadiq (AS), Dilijan
_ Asibitin Imam Khomeini (R), Mahalat
_ Asibitin Farhang Khosravani
_ Asibitin Mehr Khandab

Sansanonin Kiwon Lafiya

_ Health Center of Arak City
_ Shazand Health and Treatment Network
_ Tafaresh Health and Treatment Network
_ Ashtian Health and Treatment Network
_ Dilijan Health and Treatment Network
_ Kamijan Health and Treatment Network
_ Mahalat Health and Treatment Network
_ Farahan Health and Treatment Network
_ Khandab Health and Treatment Network

Kuɗin makarantar Arak University of Medical Sciences

Wannan shi ne jadawalin kuɗin makarantar Arak University of Medical Sciences tare da rangwamen

TitleAnnual Tuition ( in Dollars )Annual Tuition Discount ( in Dollars )
M.D.4,030$2,821$
MBBS4,030$2,821$
Specialized residency courses4,510$2,710$
D.D.S4,330$2,821$
Ph.D.3,750$2,250$
M.Sc2,465$1,480$
B.Sc1,940$1,165$
Pharmacy4,320$2,376$
Accommodation500$500$
Insurance25$25$
Food (Per Month)74$74$
Farsi Class460$460$

Sassan koyarwa (Departments)

School of Medicine: Clinical Departments:
_ Internal Department
_ Department of Neurosurgery
_ Department of Gynecology and Obstetrics
_ Department of Orthopedics
_ Anesthesia Department
_ Department of Dermatology
_ Department of General Surgery
_ Eye Department
_ Internal Department of Brain and Nerves
_ Department of Radiology
_ Department of Psychiatry
_ Department of Emergency Medicine
_ Cardiovascular
_ Infectious
_ Children
_ Ear, Throat and Nose
_ Social and Family Medicine
_ Poisonings

Basic Sciences Departments:
_ Anatomical Sciences
_ Parasitology
_ Biostatistics
_ Bacteriology
_ Medical Immunology
_ Biochemistry and Genetics
_ Medical Biotechnology and Molecular Medicine
_ Iranian Medicine
_ Pharmacology
_ Physiology and Medical Physics
_ Midwifery Department
_ Islamic Teachings
_ Department of History of Medical Sciences

Dental College: Clinical Departments:
_ Department of Restorative and Cosmetic Dentistry
_ Diseases of Mouth, jaw and face
_ Department of Oral, jaw and facial surgery
_ Department of Periodontics
_ Children’s Dentistry Department
_ Department of Dental Prostheses
_ Department of Oral, Jaw and Facial Radiology
_ Department of Endodontics
_ Department of Orthodontics

Faculty of Rehabilitation:
_ Department of Audiology
_ Educational Department of Occupational Therapy
_ Educational Department of Speech Therapy

School of Nursing: Educational Departments (Masters):
_ Internal-Surgical Nursing
_ Children’s Nursing

Educational Departments (Undergraduate):
_ Internal-surgical Nursing Department
_ Department of Community Health Nursing, Nursing Management, Psychiatric Nursing
_ Nursing Department for Children, Mothers and Babies
_ Department of Medical Emergency

School of Paramedicine:
_ Laboratory Sciences
_ Anesthesia
_ Radiation Therapy Technology
_ Radiology Technology
_ Surgery Room

School of Health:
_ Educational Department of Health and Health Promotion
_ Senior Department of Environmental Engineering
_ Department of Epidemiology
_ Department of Occupational Health and Safety Engineering
_ Department of Environmental Health Engineering
_ Department of Public health
_ Department of Nutrition
_ Health Management Services

Shazand School of Nursing:
_ Educational Department of Nursing

Arak Health Higher Education Complex:
_ Fighting Diseases (BSc)
_ Family Health (BSc)

Arak University of Medical Sciences

Abubuwan more rayuwa na Arak University of Medical Sciences

Wurin kwana: Hostel shi ne gida na biyu a wurin ɗalibai, kuma ya na da muhimmanci sosan gaske wurin samarwa ɗalibai da salama, kwanciyar hankali, daidaiton tunani, nishaɗi, yana kuma ƙara ingancin karatunsu. Saboda haka ne sashen kula da masaukan ɗalibai na wannan jami’a ya yi ƙoƙarin sauƙaƙa da inganta yanayin rayuwar ɗalibai a hostel, tare da kiyaye haƙƙoƙin ɗaiɗaiku da kuma ilahirin ɗalibai, ƙarfafa ruhin mas’uliyya da kuma yarda da kai, samar musu da tsaro, da sauransu a cikin tsarin dokoki da ƙa’idoji na hukumar lafiya karatun likitanci.

Wannan jami’a na da hostel 5 ( 3 na maza 2 na mata), sannan tana kan gina wasu guda 2.

_ Wurin kwana na Imam Reza (na maza)
_ Wurin kwana na Ikhwat (na maza)
_ Wurin kwana na Sahid Mashayihki (na maza)
_ Wurin kwana na Hazrat Ma’asumeh (na mata)
_ Wurin kwana na Narges (na mata)
_ Wurin kwana na Parvin Etesami (ana kan gina shi)
_ Wurin kwana na Shahid Solaimani (ana kan gina shi)

Abinci: Sashen kula da abinci na jami’ar likitanci ta Arak, ɗaya daga cikin sassan jami’ar mafi muhimmanci, wanda ke da alhakin tafiyarwa, tsarawa da sa ido a madafun abinci da ɗakunan cin abinci. Hakazalika daga cikin ayyukan wannan sashe akwai shiryawa, sanyawa, da gyara kayayyakin da ke cikin ɗakunan cin abinci, tattara kayan abinci, kula da inganci da yawan kayan abinci da ake buƙata wurin dafawa da raba kusan plate 3000 na abinci ga ɗalibai (na safe, na rana, da na dare) a kowace rana, kusan plate 400000 kenan a shekara. Haka kuma sashen na abinci ya na ƙoƙarin ganin cewa ya bibiyi ra’ayoyin ɗalibai a kan abincin domin inganta ɗanɗanonsa.

Sashen kula da jin daɗin ɗalibai: Sashen kula da walwala da taimakon ɗalibai ma ɗaya ne daga cikin sassa da dama da ake da su na tafiyar da harkokin ɗalibai, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da wani ɓangare na abubuwan buƙatu na ɗalibai ta hanyar basu damar cin gajiyar kayan aiki da asusun jin daɗin ɗalibai wanda hukumar lafiya da jami’ar suka samar. Sashen jindadin ɗalibai tamkar wata gada ce tsakanin jami’ar da asusun jin daɗin dalibai na hukumar lafiya. Daga cikin lamunin da wannan sashe yake ba ma ɗalibai akwai ( lamunin tallafin karatu, rahan na gidaje ga ɗaliban da suke zaune a wajen hostel ɗin ɗalibai, lamunin aure).

Motsa jiki: Sashen motsa jiki na da manufofin inganta ayyukan wasanni, samar da kuzari da lafiyar jiki, da kuma haɓaka ruhin wasanni a tsakanin ɗalibai, shi ke da alhakin shirya azuzuwan da suka shafi karatun motsa jiki 1 da 2, samar da wasanni na gasa ga ɗalibai a cikin da wajen jami’a domin cike lokutan faragarsu, da kuma bunƙasa wasanni na gama-gari da keɓantattu ga ɗalibai.

Yanayin Wuri

Arak University of Medical Sciences tana nan cikin garin Arak, a unguwar Shahrak Mostafa Khomeini, titin Qods, titin Allameh Ja’afari. Jami’ar na kusa da wurare kamar shagon Refah, cibiyar rigakafi ta zauren wasanni na Shahid Saki, cibiyar kasuwanci da ma’adanai ta lardin Markazi, pharmacy, da kuma asibitin Ayatollah Khansari.

Saduwa da Arak University of Medical Sciences

Adireshi: Arak – titin Shahid Shirudi – titin Alamol Hoda
Shafin jami’a: www.arakmu.ac.ir/fa

Tambayoyin da ake yawan yi game da Arak University of Medical Sciences

Ko wannan jami’a na bada rangwamen kuɗin makaranta ga ɗaliban waje?

Eh, jami’ar tana rangwamen kaso 30 a kwas ɗin M.D, kaso 34.84 a kwas ɗin D.D.S, sauran kwasa-kwasai kuma kaso 40 bisa ɗari.

Ko akwai wasu ƙarin kuɗaɗe da ake buƙatar ɗalibai su biya?

Eh, ɗalibai na biyan dala 5 na inshora a kowane wata.

Ko wannan jami’a na bada masauki ga ɗaliban ƙasashen waje?

Eh, jami’ar na da hostel 3 na ɗalibai maza, 2 kuma na ɗalibai mata. Hakazalika tana kan samar da ƙarin wasu guda 2.

Related Posts
Leave a Reply