[gtranslate]
تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences

Karatu a University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences

Loading

University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences (tsohon sunanta: University of Rehabilitation Sciences and Social Welfare) jami’ar gwamnati ce wadda ke ƙarƙashin hukumar kiwon lafiya a garin Tehran. Jami’ar tana nan a wani yanki na musamman, sannan kuma ita kaɗai ce take bada horarwa ta musamman a kan al’amuran da suka shafi rehabilitation da lafiyar zamantakewa. Ku kasance tare da mu, watakila ku yi sha’awar yin karatu a wannan jami’a.

Gabatarwa

An kafa Jami’ar bisa amincewar Majalisar mataimakan shugabannin Hukumar Lafiya, Jinya da karatun Likitanci game da kafa wata jami’a wadda za ta zurfafa a fannin rehabilitation, zamantakewa da lafiyar kwakwalwa. An kafa dokokin jami’ar a hukumance a ranar 31/10/1992 tare da amincewar majalisar bunƙasa Jami’o’in karatun likitanci na ƙasar.

Ayyukan jami’ar sun fara ne da kafa ƙungiyar horarda ma’aikatan agaji na zamantakewa, wanda ya bunƙasa a hankali har ta kai cewa a halin yanzu tana da departments wato sassan koyarwa guda 23, cibiyoyin bincike guda 8, haziƙan membobin tsangayar ilimi sama da 150 da ke aikin koyar da ɗalibai 1,700 waɗanda kaso 65 daga cikinsu suna karatu ne a matakin postgraduate. Wannan jami’a na ɗaya daga cikin jami’o’in ilimin kiwon lafiya mafi inganci a ƙasar Iran.

A halin yanzu, akwai ɗalibai 1,776 da malamai 158 a wannan makaranta. Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu, jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi guda 2051 a taruka da wallafe-wallafenta na cikin gida. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan kuma ta wallafa mujalla 4 na musamman. Har ila yau, jami’ar ta shirya taruka 12 zuwa yanzu. Hakazalika, jami’ar ta yi nasarar wallafa maƙala 3863 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, manazarta da masu bincike na wannan jami’a sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu da kalmomin “IRAN” da “ایران” a matsayin muhimman kalmomi.

Karatu a University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences

Martabar Jami’a

Jami’ar University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences ta yi nasarar samun matsayi na 54 a tsakanin ƙananan jami’o’in duniya waɗanda yawan ɗalibansu bai wuce dubu biyar ba. Idan aka koma tsarin ranking na TIMES kuma, a shekarar 2023 jami’ar ta yi nasarar samun matsayi na farko a tsakanin ƙananan jami’o’in ƙasar Iran bayan la’akari da abubuwa guda 13 wanda tsarin ya yi amfani da su wurin tantance makarantu.

Kuɗin makarantar University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences

 

Makarantu

Faculty of Rehabilitation Sciences
Faculty of Behavioral Sciences and Mental Health
Faculty of Social Health

Departments

  • Educational Department of Genetics (Master’s and PhD)
  • Educational Department of Rehabilitation Management (Master’s Degree)
  • Educational Department of Occupational Therapy (Bachelor’s, Master’s, Doctorate)
  • Educational Department of Physiotherapy(Bachelor’s, Master’s, PhD)
  • Educational Department of Orthotics and Prosthetics (Artificial Limb) (Bachelor, Master, Doctor)
  • Department of Speech Therapy (Bachelor’s, Master’s, PhD )
  • Department of Clinical Sciences
  • Educational Department of Ergonomics (Master’s Degree)
  • Educational Department of Basic Sciences (Master’s Degree)
  • Department of Audiology (Master’s Degree)
  • Department of Psychiatry (Medical Specialty Course)
  • Educational Department of Psychology of Exceptional Children (Master’s Degree)
  • Department of Clinical Psychology (Bachelor’s, Master’s, PhD)
  • Department of Counseling (Master’s, PhD)
  • Department of Preschool (Bachelor’s Degree)
  • Department of Nursing (Master’s, PhD)
  • Educational Department of Social Welfare (Master’s Degree and Doctorate in Health and Social Welfare)
  • Department of Social Work (bachelor’s, master’s, doctorate)
  • Department of Biostatistics and Epidemiology (Master’s Degree)
  • Educational Department of Geriatric (Master’s Degree)
  • Health Education Department in Accidents and Disasters (Master’s and PhD)
  • Department of Health, Safety and Environment Management (Master’s Degree)
  • Educational Department of Islamic Education (Master’s Degree)

Ƙungiyoyi da Cibiyoyin Bincike

  • Social Health Research Institute
  • Social Welfare Management Research Center
  • Research Center for Social Factors Affecting Health
  • Center for Substance Abuse and Dependence Research
  • Center for Health Research in Accidents and Disasters
  • Children’s Neurological Rehabilitation Research Center
  • Aging Research Center
  • Genetic Research Center
  • Psychosis Research Center

Karatu a University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences

Cibiyoyin Magani

  • Razi Psychiatry Training Center
  • Rafidah Rehabilitation Hospital
  • Asma Rehabilitation Center
  • Nizam Mafi Specialized Treatment and Rehabilitation Clinic

Ayyukan kiwon lafiya

Har ila yau, University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences tana gudanar da ayyukan kiwon lafiya. Misali, jami’ar tana da ikon tallafawa al’ummomin da wata matsala ta shafa. Tana yin hakan ne ta hanyar aiki tare da asibitoci da cibiyoyi daban-daban. Daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya da jinya na jami’ar akwai cibiyar koyarda psychiatry ta Razi, Asibitin Rehabilitation ta Rufaideh, cibiyar rehabilitation ta Asma, da kuma clinic ɗin musamman na jinya da murmurewa na Nizam Mafi.

Mujallu

  • Social Welfare Quarterly
  • Specialized journal of physiotherapy
  • Scientific Research Quarterly of Rehabilitation
  • Specialized Journal of Clinical Psychology
  • Social Work Quarterly
  • Scientific Research Quarterly Journal of Aging in Iran
  • Health in Emergencies & Disasters Quarterly (HDQ)
  • Iranian Rehabilitation Journal

Ababen More Rayuwa

  • Laburare
  • Zaurukan wasanni
  • Amphitheater
  • Restaurant
  • Kafteria, da sauransu

 

Karatu a University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences

Yanayin Wuri

University of Social Welfare and Rehabilitation Sciences na nan a unguwar Velenjak a garin Tehran, Avin, titin Daneshjo, Kodakyar. Jami’ar na kusa da muhimman wurare kamar cibiyar sayayya ta Galleria, asibitin Ayatollah Taleghani, gidan cin abinci na Shandiz Galleria, cibiyar sayayya ta Valenjak, da kuma kwalejin kiwon lafiya na jami’ar karatun likitanci ta Shahid Behesti. Tashar bas mafi kusa da wannan jami’ar ita ce tashar bas ta Shahid Beheshti, hakan ya sauƙaƙe zirga-zirga zuwa wannan jami’a ga ma’aikata da ɗaliban da ba su da ababen hawa na kansu.

Adireshi

  • Tehran, Avin, Titin Daneshjo, Kodakyar

Shafin jami’a: http://www.uswr.ac.ir

Related Posts
Leave a Reply