Daga cikin abubuwan da ɗalibai da matafiya masu yawon buɗe ido a Iran ke muhimmantarwa akwai yanayin tsadar rayuwa ko farashin rayuwa a Iran bayan farashin karatu ko yawonsu. Ƙasar Iran na daga cikin ƙasashe masu arhar karatu da yawon buɗe ido ga ɗaliban waje, kuɗin makaranta na da sauƙi sosai bisa ga sauran ƙasashe. Wannan ya haɗa da ɓangaren karatu, jinya, abinci, zirga-zirga, da walwala. Duba da yadda kuɗin ƙasar Iran suka rasa daraja a ƴan shekarunnan, farashin zama a Iran yana daɗa raguwa ga ƴan waje. Saboda haka wannan dama ce ga mutanen da ke sha’awar yawace-yawace zuwa ƙasashe masu ɗimbin tarihi. Ku kasance tare da mu.
Mun kasa farashin zama a Iran kamar haka:
Farshin karɓar bizar Iran
Kuɗin jirgi zuwa Iran
Farashin masauki a Iran
Farashin zirga-zirga
Kuɗin Abinci da tufafi
Natija
Ku kasance tare da mu domin sanin kuɗin bizar karatu a Iran
Farshin karɓar bizar Iran
Domin karɓar bizar karatu ta Iran, ana biyan kuɗi wanda wannan kuɗin ya danganta da nau’in bizar, ƙasar wanda ke son bizar, da kuma siyasoshi irin na jakadanci. A taƙaice, farashin ya ƙunshi kuɗin bizar ita kanta, da ƙarin wasu kuɗaɗe a wasu lokutan, kamar kuɗin inshorar tafiya ko kuma kuɗin ayyukan post. Hakazalika, mai yiwuwa a samu wata yarjejeniya tsakanin ƙasar Iran da wata ƙasa wanda hakan na iya yin tasiri a kan farashin biza. Lallai ne ku nemi ingantaccen bayani game da farashi da kuma takardun da ake buƙata daga ofishin jakadancin Iran a ƙasashenku, ko kuma a amintattun shafukan yanar gizo.
Kuɗin jirgi zuwa Iran
Kuɗin jirgi zuwa Iran sun fara daga dala 240 zuwa dala 3400 wanda ƙaruwa ko raguwar farashin ya dogara da abubuwa kamar haka:
- Garin da za a baro: Yaya nisan garin da za a tashi zuwa Iran?
- Lokaci: A wane lokaci na shekara ake son a yi tafiyar?
- Kamfanin jirgin sama: Da wane kamfanin jirgin sama za ayi tafiyar?
- Lokacin sayen tikiti: Kwana nawa kafin tafiyar za a sayi tikiti?
- Yanayin tikiti: Tikitin business ne, ko economy, ko first class
Waɗannan abubuwan da muka ambata su kan canza a mabambantan lokuta wanda ke haifar da hawa ko saukar farashin tafiyar. A taƙaice wannan farashin ƙiyasi ne.
Farashin masauki a Iran
Farashin hotel a garuruwan Iran yana kamawa tsakanin dala 10 zuwa dala 150 duk kwana ɗaya wanda shi ma ya dogara da abubuwa daban-daban kamar tsawon lokacin haya, yanayin wurin, gari, da kuma walwalarsa. Kamar yadda kuka sani a mafi yawan hotal na duniya ciki har da Iran, ana kama ɗaki ne daga ƙarfe 2 na rana zuwa sama, lokacin haya kuma na ƙarewa ne ƙarfe 12 na rana. Duk da haka akan iya samun wasu hotal ɗin wanda tsarinsu ya bambanta da na sauran. Saboda haka ku lura sosai da awanni wurin kama hotel; sai dai idan kun gani a list ɗin hidimomin hotel ɗin an rubuta cewa ana karɓar mutane awa 24 ba. Ɗalibai na iya amfani da hostel ɗin jami’a domin samun sauƙi. Yanzu jami’o’in Iran na da hostel masu tsari na zamani.
Farashin zirga-zirga
A muddar zamanmu a Iran dole ne mu buƙaci kai-komo daga wani wuri zuwa wani wurin ko kuma ɗaukar kaya zuwa wani wuri kuma dole za mu biya kuɗi a kan hakan. Wannan kuɗin ya bambanta tsakanin ƙasashe saboda akwai abubuwa da yawa masu ɗagawa ko sauke kuɗin zirga-zirga. Haka farashin jigilar kaya yana tasiri a kan farashin kayan. Maganar gaskiya ita ce bayyana lokaci da kuma abubuwan da za su iya faruwa a hanya ba abu ne mai sauƙi ba, hakan ne ya sa mafi yawa sai bayan kayan sun isa ake iya kimantasu. Kuɗaɗe kamar na; faɗuwar farashin abun hawa, ishora, haraji, a ƙasa Irin Iran wanda ke yawan hawa da sauka, na iya yin tasiri sosai a kan farashin zirga-zirga. Sufuri kaɗai ya na cinye ɗaya bisa uku na kuɗaɗen logistics.
Kamar dai yadda muka ambata a baya, akwai abubuwa da dama masu sanya hawa ko saukar farashin zirga-zirga a wata ƙasa ko yanki. Yana da kyau ku san cewa komai ƙanƙantar ƙarin kuɗin ɗaukar kaya kai-tsaye kuma zaunannen ƙari, ya kan yi tsairi a farashin kayan. Yanzu za mu yi muku bayani a kan abubuwan da ke tantance farashin zirga-zirga.
- Nisa: Nisan inda za a je shi ne abu na farko da ke tantance kuɗin tafiya. Farashin kai kaya zuwa wurare masu nisa ya fi yawa. Hakan na faruwa ne saboda man da za a ƙone ya fi yawa, wahalar tafiya, da sauran abubuwa. Kodayake nau’in kayan da kuma ingancin hanyoyin da za a bi kan bambanta. Misali; ƙasashen da suke wurin da babu ruwa (teku), kasantuwar cewa ba za su iya yin sufuri kai-tsaye ta ruwa ba dole sai sun yi zagaye ta hanya mai nisa, dole za su fi kashe kuɗi wurin yin sufurin kaya.
- Kuɗin aiki: zirga-zirga da sufuri suna cinye kusan kashi 25% na makamashin ƙasa. Yana da kyau ku san cewa farashin dillalan makamashi na da tasiri kai tsaye a kan farashin sufuri. Makamashi ke lashe kusan rabin farashin duk hanyoyin sufuri, yayin da sauran abubuwan ke amfani da sauran rabin a tsakaninsu.
- Nau’in kaya: Nau’in abunda ake yin sufuri na da tasiri sosai a farashin sufurin. Misali, ko kun lura da cewa akwai da yawa kayan da sai an yi packaging ɗin su kuma an yi takatsantsan wurin ɗaukarsu, irin wannan kulawar ma na kawo ƙarin kuɗin sufurinsu. Misali gawayi ya fi sauƙin ɗauka a kan kayan marmari da ɗanyun furanni. Yin amfani da mabambantan kwantenoni ko motocin ɗaukar kaya masu ɗakuna ƙira na musamman zai iya warware wannan matsalar. To yanzu kuma idan fasinjoji za a ɗauka fa? Babu shakka dole a samar musu da walwala. Domin samar da wannan kuma ana buƙatar kashe kuɗi, kenan hakan zai yi tasiri a kuɗin da za a karɓa daga garesu.
- Kayan aiki da gine-gine: Inganci da ƙarfin hanyoyin sufuri da tashoshi shi ma yana da tasiri a farashin zirga-zirga. Rashin ingancin kayan aiki da hanyoyi yana haifar da ƙarin farashin sufuri, jinkiri, da mummunar makomar tattalin arziki. Tsarukan sufuri na zamani na cin farashi ƙasa da waɗanda ba su da, saboda sun fi tabbas kuma a haɗe suke da juna sannan sun fi jimirin motsi.
- Haraji: A duka ƙasashen duniya ana karɓar haraji ko haƙƙin hanya daga direbobi wanda ake amfani da shi wajen gyara hanyoyi da kayan aikin sufuri da zirga-zirga. Harajin mai shi ne hanya mafi shahara da ake karɓar haraji daga hannun mutane. Gina tunnel ko manyan gadoji a hanya shi ma yana iya ƙara yawan harajin da ake biya. Haraji kuma wani ɓangare ne na kuɗin zirga-zirga.
- Insurance: Domin samun aminci a matsayin matafiyi, akan yi ishora a tafiye-tafiye. Dama masu ababen hawan sun riga sun biya wannan kuɗin na ishora, su kuma za su karɓa daga fasinjoji a matsayin kuɗin haya daga baya. Haka shi ma sufurin kaya yana ɗauke da wannan farashi na inshora. Domin samarwa masu kaya da kwanciyar hankali game da asarorin da kan iya tasowa da yin rigakafin karyar tattalin arziki ta dalilinsu, akan yi ma kaya inshora wanda kuma babu shakka hakan zai ƙara kuɗin sufuri.
Kuɗin Abinci da tufafi
Babu shakka abinci da tufafi wani ɓangare ne mai muhimmanci na rayuwa. Ana buƙatar sayen kayan abinci domin samar da mizanin abinci na kullum. Shinkafa, alkama, nama, ƴaƴan itace, ƙwai, kayan kiwo, da sauransu na ɗauke da muhimman sinadarai waɗanda muke buƙata a rayuwarmu ta yau da kullum. A cewar cibiyar ƙididdiga, kashi 21% na kuɗin abinci na tafiya ne wurin sayen garin hulawa, burodi, hatsi da taliya. kashi 21 na tafiya wajen sayen fari da jan nama, kashi 19 kuma wajen ƴaƴan itatuwa da kayan marmari. Kashi 11% wajen ƙwai da kayan kiwo, kashi 8% sukari, coffee, shayi, kashi 7% wajen busassun ƴaƴan itatuwa, wake, kashi 6% wajen drinks, fastfood da sigari, kashi 4% kayan ɗanɗano da kayan ƙamshin abinci, sai kashi 3% da ke tafiya wajen mai da kayan maiƙo. Kowa ya san cewa kayan sawa da takalma suna da muhimmanci ga mutane.
A ƙasar Iran ana muhimmantar da tufafi da kashe-kashen tufafi sosai. Gwargwadon muhimmancin da ake ba wa tufafi gwargwadon bunƙasar masana’antun yin tufafin kuma kasuwar tufafi za ta ƙara buɗewa a ƙasar har ma ta iya taka muhimmiyar rawa a kasuwannin duniya. Da wannan za a iya gane matsayin masana’antar tufafi da saƙa a ƙasar Iran wadda tsohuwar masana’anta ce amma ta samu sauye-sauye da yawa. Ana iya duba bayanin ƙididdiga wanda babban banki ya fitar. Bayanan suna nuna ƴan canje-canje da ƙarin farashin rayuwa na iyalai a ƙasar Iran.
Sharhi