[gtranslate]
Mashhad, Meidane Shari'ati, kafin a ƙarasa layin Ahmad 1, Block na 15
Search

Karatu a Iran: Mahangar wasu ɗaliban ƙasashen waje masu karatu a Iran

Karatu a Iran: Mahangar wasu ɗaliban ƙasashen waje masu karatu a Iran

Loading

Yanayin Rayuwa da Karatu a Iran: Daga bakunan ɗaliban ƙasashen waje

Ga ɗaliban ƙasashen waje, karatu a Iran na nufin farawa ko shiga wata sabuwar duniya wadda ba su sani ba a baya. Saɓanin yadda da yawan mutane su ke kallon ƙasar Iran, rayuwa a Iran kan iya zamewa dama ta musamman ga baƙin ɗalibai wajen sanin tarin al’adun ƙasar da kuma morar tsarin karatunsu na musamman, tare da ƙulla alaƙoƙi masu amfani da mutane.

Ƙasar Iran ta tattara ingantattun makarantu, tarihi mai zurfi, da muhalli mai cike da damarmaki hakazalika ƙalubale. Iran ta zama ƙasa mai jan hankalin mutanen da ke sha’awar bunƙasa tajarubarsu ta rayuwa fiye da iyakokin ƙasashensu. A wannan rubutun mun yi ƙoƙarin kawo muku labarai daga bakin ɗalibai masu karatu a ƙasar Iran waɗanda suka ganewa idanunsu zahiri na yanayin rayuwa da karatu a Iran ba ta kafafen zamani ko kuma irin labarai da kuka saba ji da gani ba.

Karatu a Iran: Yanayin rayuwa a Iran
Yanayin Rayuwa da karatu a Iran: Daga bakunan ɗaliban ƙasashen waje

Dalilan zaɓen Iran a matsayin ƙasar zuwa karatu

Ɗalibai da ke zuwa Iran karatu daga mabambantan ƙasashe, kowanen su na da nasa dalilin da ya sa ya zaɓi Iran:

Ingancin Karatu da Manyan Jami’o’i

Jami’o’in Iran irin su University of Tehran, Sharif University of Technology, da Tehran University of Medical Sciences, sun yi fice sosai kuma suna da kima a idon duniya. Da yawan ɗalibai na zuwa Iran karatu ne domin samun ilimi mai zurfi a fannoni irin medicine, engineering, da humanities.

Tarihi da Al’ada

A matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi daɗewa a duniya, Iran na da ɗimbin tarihi da al’adu masu jan hankalin ɗalibai zuwa sanin tarihinsu da irin al’adunsu.

Sauƙin Rayuwa

Ɗaya daga cikin manyan fa’idojin da baƙin ɗalibai za su samu a Iran shi ne sauƙin kuɗin karatu da rashin tsadar rayuwa idan an kwatanta da sauran ƙasashen. Wannan ya na jan hankalin ɗalibai da yawa wajen zaɓar Iran a matsayin ƙasar da su ke son zuwa yin karatu.

 

Ƙalubale da Gaskiyar Yanayin Rayuwa a Iran

Ɗaliban ƙasashen waje na fuskantar waɗansu ƙalubale da wahalhalu waɗanda ke yin tasiri a zaman nasu.

Koyon Yaren Farsi

Ƙalubale na farko da akasarin ɗalibai ke fuskanta shi ne yaren Farsi. Akan iya samun jami’o’i masu karantarwa da turanci, amma duk da haka iya wannan yaren na da matuƙar muhimmanci aƙalla wurin mu’amalantar mutane da tafiyar da rayuwar yau da kullum.

Dokoki da Bambancin Al’adu

Ƙasar Iran na da nata dokoki da al’adu daban. Ɗaliban da ke zuwa daga ƙasashen yamma ko sauran ƙasashen da suke da sakakken ‘yanci kan iya shan wahala wurin sabawa da wasu dokokin irin na sa hijabi da sauran iyakokin al’adu.

Tsare-Tsaren Gudanarwa masu Wahala

Wasu ɗaliban na iya shan wahala wajen kai-komo don yin ayyukansu ofis, tun daga kan biza har zuwa registration da muhallin zama. Kamfaninmu ya sauƙaƙe muku ayyukan bibiyar admission a kowace jami’a da fanni da kuke ra’ayi. Za ku iya tuntuɓarmu ta WhatsApp domin samun ƙarin bayani.

Damarmakin da ake samu na Rayuwa a Iran

Dammammakin karatu a Iran
Damarmakin musamman na rayuwa da karatu a Iran

Duk da waɗannan ƙalubalen, baƙin ɗalibai da ke karatu a Iran kan iya samun damammaki da yawa kamar:

Karatun manyan fannoni: Iran ta ci gaba sosai a fannoni daban-daban irin su nanotechnology, engineering, da medicine. Ɗalibai za su iya amfana da ingantattun kayan aiki da kuma tajarubar gogaggun malamai.

Sanin Al’adu: Ɗalibai na da kyakkyawar damar sanin al’adu da tarihin Iran, bukukuwa irin Nowruz da wuraren tarihi irinsu Persepolis da sauransu. Da yawan ɗalibai na ƙulla abota da Iraniyawa wanda hakan na taimaka musu sosai wurin sanin waɗannan abubuwan.

Damar tafiye-tafiye da yawon buɗe ido: Iran faffaɗar ƙasa ce mai cike da wurare na ɗabi’a. Ɗalibai kan yi tafiye-tafiye zuwa garuruwan Isfahan, Shiraz, Mashhad, da sauransu domin gane wa idonsu muhimman abubuwa na ƙasar.

Labaran wasu ɗaliban waje masu karatu a Iran

Watakila ku yi sha’awar jin ra’ayoyin ɗaliban ƙasashen waje da ke karatu a Iran. A wannan rubutun mun kawo muku labarin Karim daga ƙasar Nigeria, Anna ‘yar ƙasar Russia, da Mohamman ɗan ƙasar Malaysia da irin abubuwan da suka gani a zamansu na karatu a Iran.

Karim daga Nigeria – Mai karatu a Tehran University of Medical Sciences

Karim ɗalibin likitanci ne a jami’ar likitanci ta Tehran. Ga labarinsa dangane da karatu a Iran kamar haka:

“Karatu a Iran yana da inganci. Kodayake yaren farsinnan yana da wahala, na samu taimako sosai daga abokanai na Iraniyawa. Iran ƙasa ce wadda ta cancanci a bata dama; akwai mutanen kirki da tarin al’adu masu burgewa, Iran na da abubuwan koyo da yawa”.

Anna daga Russia – Mai karanta fannin Iranian Architecture a garin Isfahan

Anna, mai karatun architecture a jami’ar University of Art Isfahan ta ce:

Garin Isfahan na da tsarin gine-gine mai jan hankali, na samu damar fahimtar salon gini irin na Iran da na musulunci a aikace. Malamaina sun taimaka sosai, na samu aminci da kwanciyar hankali mai yawa a wannan garin.”

 

Mohammad ɗan ƙasar Malaysia – Mai karatu a Sharif University of Technology

Mohammad ya zo daga ƙasar Malaysia, inda ya ke karanta electrical engineering a jami’ar Sharif University of Technology, ga ta bakinsa kamar haka:

“Jami’ar Sharif University of Technology ɗaya ce daga cikin jami’o’in fasaha mafi inganci a nahiyar Asia. Karatu a jami’ar ya bani damar aiki tare da abokan karatu da malamai masu ƙwazo. Zama a birnin Tehran na da wahala ta wata fuskar saboda yawan cinkoson ababen hawa da gurɓatacciyar iska. Amma dai a taƙaice, na samu tajaruba mai kyau”.

 

Rufewa

Ɗaliban ƙasashen waje su san cewa karatu a Iran ya tattara damammaki hakazalika ƙalubale. Dukda bambancin al’adu da wasu yanayukan, da yawan ɗalibai na kallon zama a Iran a matsayin dama ta ganin sabbin al’adu, koyon abubuwa da dama, tare da gina alaƙoƙi masu amfani. Labaran waɗannan ɗaliban ya nuna cewa karatu a Iran ya zarce kawai halartar azuzuwa; yana bada damar samun tajarubobin daɗaɗɗun al’adu.

 

Related Posts
Leave a Reply