Yazd University da ke garin Yazd, ɗaya ce daga cikin jami’o’i masu muhimmanci a Iran. Tana da wadatattun kayan aiki na karatu da na bincike, sannan tana da kimtsatssen muhalli wanda ya dace da ɗaliban ciki da wajen ƙasar Iran.
Karatu a Yazd University
A shekarar 1987 aka assasa jami’ar Yazd a ɗaya daga cikin garuruwa mafi jan hankali na ƙasar Iran, wato garin Yazd, kuma a lokacin ana yi mata kallon jami’ar Iran mafi kammaluwa. Yanzu haka jami’ar Yazd na da ɗalibai 12,000 masu karatu a makarantunta 14. A shekarun farko-farko na bayan juyin juya halin musulunci, Sayyed Ruhullah Khatami da Muhammad Sadoughi sun kasance daga cikin mutanen da suka fara yunƙurin assasa babbar cibiyar koyarwa a garin na Yazd.
Ƙarshe a shekarar 1986, shirin assasa jami’a a garin Yazd ya samu karɓuwa inda aka ɗora tubalin ginin a shekarar 1987 a wata ziyarar fira minista na lokacin Mir Hossein Mousavi, ta hannun Muhamman Sadoughi a wani fili mai girman hekta 300. A watan Mayun shekarar 1987, Dr. Jalil Shahi ya shugabanci buɗa jami’ar Yazd. A 1991, an haɗe jami’ar da tsohuwar cibiyar horar da malamai wuri ɗaya, inda jami’ar ta Yazd ta ci gaba da aiki a matsayin jami’ar gwamnati, kusa da maƙabartar Zoroastrian a ƙauyen Taqiabad, sannan ta ci gaba da ayyukanta
Martabar Yazd University
Jami’ar Yazd ta samu matsayi na 1001 – 1200 a shekarar 2024, a tsarin ranking na Times. Hakan ya nuna cigabanta idan aka kwatanta da shekaru biyu baya, lokacin da take matsayi na 1201 – 1500. Tsarin Times ya fara aikinsa na ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin ilimi na duniya tun a shekarar 2010, sannan jami’ar Yazd ta yi nasarar shiga tsarin na times tun a shekarar 2017.
Harabobi da Makarantu
Social Humanities Campus
- Makarantar Social Sciences
- Makarantar Theology
- Makarantar Psychology & Educational Sciences
- Makarantar Economics
- Makarantar Management & Accounting
- Makarantar Language & Literature
- Sashen Law & Political Science
- Sashen Geography
Engineering Technical Campus
- Makarantar Electrical Engineering
- Makarantar Mining and Metallurgy Engineering
- Makarantar Civil Engineering
- Makarantar engineering faculty
- Sashen Industrial Engineering
- Sashen Textile Engineering
- Sashen Chemical and Polymer Engineering
- Sashen computer engineering
Science Campus
- Makarantar Mathematical Sciences.
- Makarantar Chemistry
- Makarantar Physics
- Sashen Biology
- Sashen Geology
Makarantu masu zaman kansu
- Urban Planning
- Architecture
- Painting
Kayan Aikin Jami’a
Jami’ar Yazd na da wadatattun abubuwan more rayuwa da kayan aiki irin su laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, hostel, da kayan wasanni. Bayan wannan, jami’ar na da tsarin musayar ɗalibai da wasu daga cikin manyan jami’o’in sauran ƙasashen duniya wanda hakan babbar dama ce ga ɗalibai.
Alfanun karatu a Yazd
Karatu a garin Yazd na da alfanoni da dama. Akwai sauƙin tsadar rayuwa a garin Yazd idan an kwatanta da sauran manyan bireanen ƙasar Iran. Na biyu, garin Yazd a natse yake kuma cike da aminci, hakan dama ce ga ɗaliban da basu cika son hayaniya ba. Hakazalika akwai tarin al’adu da tarihi mai zurfi a garin Yazd wanda zai iya ƙara wa ɗalibai tajarubar rayuwa.
Laburaren Yazd University
Shekaru biyu bayan assasa jami’ar Yazd, 1989 kenan, aka buɗa laburaren jami’ar. Laburaren na cikin campus ɗin gabas, kusa da kafteriya. A shekarar 2007 aka maida laburaren daga wannan kamfus ɗin zuwa babban kamfus ɗin jami’ar.
Hawan farko na jami’ar ya keɓanci bada aron littafai, litattafan references, da ofisoshin gudanarwa, hawa na biyu kuma a nan ake taskace jaridu da theses na ɗalibai. Yanzu haka, akwai laburare biyu a kamfus ɗin Art and Architecture da na Mehriz, waɗanda ke ƙarƙashin kulawar babban laburaren. Laburaren ya ƙunshi sama da kwafi 227,000 na litattafan farsi da na latin, tare da damar amfani da kundin bayanai (database) sama da 40, tare da kimanin theses 13,600 na ɗalibai da sauran litattafan reference. Laburaren ya bunƙasa da tarin waɗannan resources waɗanda ake amfani da su a sassan koyarwa daban-daban na jami’ar, irin su engineering, humanities, architecture, basic sciences, da sauransu.
Da wa Jami’ar Yazd ta dace?
Jami’ar Yazd ta dace da ɗaliban da ke sha’awar karatunsu a natsatstsen muhalli mai kwanciyar hankali inda babu yawan hayaniya. Hakazalika, jami’ar ta dace da ɗalibai masu sha’awar sanin tarihi da al’adun ƙasar Iran. Har ila yau, ɗaliban ƙasashen waje za su iya amfanuwa da tsarin musayar ɗalibai na jami’ar ko scholarship.
Yanayin Rayuwar Ɗalibai a garin Yazd
Ɗalibai za su iya amfani da zauren wasanni ko musharaka a tarukan al’adu da sauran kayan aikin jami’ar Yazd. Hakazalika, akwai wuraren nishaɗi da dama a Yazd tare da kasuwannin gargajiya, wuraren cin abinci, da zafafan cafe.
Jerin Wuraren Kwanan Ɗalibai na Jami’ar Yazd
Wurin Kwana na Hazrat Ali Akbar:
- Adireshi: Yazd, Molla Farajollah, Titin Talaghani, layi na 13.
Wurin Kwanan Mata na Touba:
- Adireshi: Yazd, Yazd University, Fazilat Blv, Titin Ferdowsi.
Wurin Kwanan Mata na Hojjati:
- Adireshi: Yazd, Safaieh, Kashani, Titin Senbal.
Wurin Kwnann Maza na Pardis 2:
- Adireshi: Yazd, Yazd University, titin Golestan, Montazir Faraj.
Wurin Kwana na Yas:
- Adireshi: Yazd, Yazd University, randabawul na Alam, Titin Shohada-e Gomnam.
Wurin Kwana na Mollasadra
- Adireshi: Titin Bostan, Shahidan Ashraf, Safia, Yazd.
Wurin Kwana na Maryam 1 :
- Adireshi: Yazd, Imam Shahr, Titin Sheikh Kalini, randabawul na Fazel Lankarani, Shahid Hashminejad St.
Wurin Kwana na Maryam 2:
- Adireshi: Yazd, randabawul na Abu Zar, titin Sanbal
Wurin Kwana na Hrandi:
- Adireshi: Yazd, titin Pajohes.
Wuraren shan iska
- Shadi Park: Ɗaya daga cikin manyan shahararrun wuraren shaƙatawa a Yazd.
- Starland Amusement Park: Amusement park ne babba kuma na zamani, a tsakiyar garin Yazd wanda ke yawan jan hankalin mutane, yara da manya.
- Booz Spring Recreational Tourism Complex: Wurin hutawa ɗauke da kayan aiki daban-daban.
Karatu a Yazd University na iya samar wa ɗalibai dama ta musamman da tajaribobi. Jami’ar ta tanadi muhalli mai cike da aminci da natsuwa wanda ya dace sosai da karatu da bincike, ɗauke da ingantattun kayan aiki. Garin Yazd kuma cike yake da abubuwan tarihi da al’adu wanda za su iya ƙara armashi ga rayuwar ɗalibai.