Minene bizar karatu? Cikakken bayani da matakan samun biza. Bizar karatu ko bizar ɗalibi tana nufin izinin da ke ba ma ɗalibi damar yin karatu a wata ƙasa da ba ƙasarsa ba. Akan buga wannan biza ne na tsawon lokacin karatu a makarantar da aka tantance, kenan bizar na ba ɗalibai damar zama a ƙasar har zuwa lokacin da za su kammala karatunsu. Ashe kenan bizar ɗalibai dama ce a gare su ta haɗuwa da sabbin mutane da sanin sabbin al’adu da sabbin tajarubobin rayuwa.
Minene bizar karatu? Cikakken bayani a kan yadda ake samun bizar karatu ta Iran da matakan da ake bi.
Domin samun bizar karatu, da farko ana buƙatar admission letter wato wasiƙar samun karɓuwa daga ɗaya daga cikin jami’o’in ƙasar waɗanda aka aminta da su, sai kuma cike form ɗin biza da biyan kuɗi. Lazim ne a bayar da takardu ko shaidun da za su nuna cewa mutum na da ƙarfin da zai iya ɗaukar nauyin karatunsa da rayuwarsa. A ƙarshe, sai zuwa ofishin jakadancin ƙasar domin gabatar da interview da bayar da takardun da ake buƙata. Takardu irin su fasfo, hoto, form ɗin biza, takardun karatu, admission letter, da sauransu.
Dole ne takardun su kammala kuma su zama babu kuskure don gujewa samun cikas. Shirya ma iterview da amsa tambayoyi daga ma’aikatan ofishin jakadanci na da muhimmanci. Bizar karatu ita ke ba wa ɗalibai damar karatu a wata ƙasa tare da mu’amalantar sabbin al’adu da samun gogewar rayuwa a sabon muhalli. Saboda haka samun biza muhimmin mataki ne a sha’anin karatun ɗalibai a wasu ƙasashen. Za mu yi bayanin waɗannan matakan tare da wasu shawarwari a ƙasa:
Matakan neman bizar karatu:
- Samun karɓuwa daga amintacciyar jami’a ko cibiyar ilimi: Da fari kuna buƙatar ku samu admission a makaranta daga cikin makarantun ƙasar da za ku je. Ana bada wannan admission ne a rubuce a matsayin wasiƙa.
- Cike form ɗin neman biza: Za ku cike form ko ta online ko kuma a fili da hannunku. Form ɗin zai ƙunshi bayanan da suka shafe ku, bayanan karatunku, da tattalin arzikinku.
- Biyan kuɗin biza: Za ku biya kuɗin da aka ayyana na biza (tare da kuɗin SEVIS ga waɗanda za su je ƙasar Amerika).
- Gabatar da takardun tattalin arziki: Bayar da takardun da za su tabbatar da kuna iya ɗaukar nauyin karatu da rayuwarku a ƙasar da za ku je.
- Zuwa interview a ofishin jakadanci: Sai kuma zuwa ofishin jakadancin ƙasar mafi kusa da ku domin amsa tambayoyi da bayar da takardunku.
Takardun da ake buƙata wurin neman bizar karatu:
- Fasfo: Ya zama cewa fasfo ɗinku na da aƙalla sauran wata shida bayan shigarku ƙasar kafin ya yi expiring.
- Form ɗin neman biza: Akan cike wannan form ɗin ne online.
- Ƙaramin hoto: Hoto wanda ya cike sharuɗan da ofishin jakadanci suka sanya.
- Takardun shaidar mu’amalar kuɗi: Takardu irin bayanan banki, wasiƙun tallafin kuɗi, ko na tallafin karatu (scholarship).
- Takardun karatu: Takardun da ke gwada tarihin karatunku irinsu trascripts, certificate na kammala matakan karatu da suka gabata, recommendation letter, da kuma watakila shaidar jarabawar yare irinsu TOEFL, IELTS, GRE, da sauransu.
- SoP: Dalilanku na zaɓen jami’a da fannin karatun da kuka zaɓa, tare da shirin da kuke da shi na cimma hadafofinku.
- Wasiƙar samun karɓuwa: Wasiƙa daga jami’a ko makarantar da suka karɓe ku:
Kuɗin bizar karatu a Iran
Kuɗin bizar karatu a Iran ya bambanta tsakanin matakan karatu. Ga ɗaliban undergraduate, dala 70 ne kuɗin biza, ga ɗaliban master’s dala 80, ɗaliban PhD kuma dala 90 ne. Kuɗin sun ƙunshi kuɗin acceptance, miƙa takardu zuwa ga ofishin jakadanci, da shirye-shiryen iterview.
Scholarships
Scholarship da tallafin karatu na nufin kuɗin da jami’a, gwamnati, gidauniyoyi, ko ƙungiyoyi masu zaman kansu ke ba wa ɗalibai. Akan bada wannan tallafin ne bayan ɗalibai sun cika wasu sharuɗa sannan ba bashi ba ne da za su biya daga baya. Scholarship kan shafi kuɗin makaranta, alawus, litattafai, da sauran abubuwan da suka shafi karatu.
Shawarwari 5 masu muhimmanci:
- Takardun mu’amalar kuɗi: Ku tabbatar da takardunku na mu’amalar kuɗi sun cika.
- Bibiyar application ɗinku: Ku bibiyi halin da application ɗinku yake ciki akai-akai.
- Bincike: Kafin neman biza yana da kyau ku yi bincike game da jami’ar da za ku je.
- Shirya ma interview: Ku shirya zuwa interview a ofishin jakadancin ƙasar da za ku je domin amsa tambayoyi.
- Gabatar da Interview: Zuwa ofishin jakadancin domin gabatar da interview da miƙa takardu.
Tambayoyin da aka fi yi:
Minene dalilin karatu a Iran? Cikakken bayani a kan bizar karatu + Jadawalin kwasa-kwasan karatu a Iran ga ɗaliban ƙasashe 20
Kuɗin karatu a Iran: Biza, Masauki, da muhimman shawarwari