Garin Isfahan ɗaya ne daga cikin manyan garuruwa kuma masu ɗimbin tarihi na Iran, wanda ke tsakiyar ƙasar ta Iran sannan kuma a tsakiyar lardin Isfahan. Isfahan, gari wanda yake kusa da teku sannan gari mai ɗauke da abubuwan tarihi na UNESCO har guda 3, tsohon tsarin gini irin na musulunci, gari na uku mafi yawan jama’a a Iran bayan Tehran da Mashhad, kuma gari na 165 a duniya, sannan kuma na 9 a yammacin Asia. Karatu a wannan gari shi ne burin da yawa cikin ɗalibai.
Gabatarwa
Jami’ar Isfahan, jami’a ta farko a yankin tsakiya da kudancin ƙasar Iran, ɗaya ce daga cikin jami’o’i 4 na gwamnati a garin na Isfahan. Ta fuskar daɗewa da fannonin karatu ita ce jami’a mafi girma a yankin; ɗaya ce daga fitattun jami’o’i 5 na Iran, ɗaya daga cikin 10 na duniya. Jami’ar na kusa da ƙofar Shiraz sannan tana da girman hekta 300 Jami’ar na da makarantu 13 (department 45).
A halin yanzu akwai ɗalibai 13920 da malamai 580 a jami’ar. Bincike ya nuna cewa jami’ar Isfahan ta wallafa maƙalar kimiyya guda 24804 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida zuwa yanzu, ta kuma wallafa maƙala 15863 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar ta mallaki lambar yabo sannan ta wallafa keɓantattun mujalla 44, kuma ta shirya taruka 41 zuwa yanzu. Mafi yawan maƙalolin da aka wallafa a wannan jami’ar a shekarar 2023 suna ɗauke da kalmomin “students” da “security” a matsayin muhimman kalmomin maƙala.
Martabar Jami’a
Matsayi na 360 a jami’o’in duniya a tsarin ranking na Greenmetrics (shekarar 2023)
Matsayi na 701 a jami’o’in duniya a tsarin ranking na Round (shekarar 2023)
Matsayi na 1000+ a duniya a tsarin ranking na TIMES (2023)
Matsayi na 18 a jami’o’in Iran a tsarin ranking na Webometrics (2023)
Matsayi na 8 a jami’o’in Iran, da matsayi na 14 a tsakanin jami’o’in fasaha na Iran, a ranking na ISI (2022)
Matsayi na 831 a duniya da matsayi na 20 a tsakanin jami’o’in Iran a tsarin ranking na Leiden (2021)
Karatu a Jami’ar Isfahan
Degrees | field | Tuition fees | Limit of academic years |
---|---|---|---|
Bacholar | Humanities | Rial160,000,000 | 4 years |
Bacholar | Science | Rial188,000,000 | 4 years |
Bacholar | Engineering | Rial210,000,000 | 4 years |
Masters | Humanities | Rial420,000,000 | 2 years |
Masters | Science | Rial462,000,000 | 2 years |
Masters | Engineering | Rial546,000,000 | 2 years |
PhD | Humanities | Rial504,000,000 | 4 years |
PhD | Science | Rial546,000,000 | 4 years |
PhD | Engineering | Rial620,000,000 | 4 years |
Makarantu
- Faculty of Administrative Sciences and Economics
- Faculty of Literature and Humanities
- Faculty of Sports Sciences
- Faculty of Foreign Languages
- Faculty of Technical Engineering
- Faculty of Civil Engineering and Transportation
- Faculty of Theology and Education
- Faculty of Biological Sciences and Technologies
- School of Chemistry
- Faculty of Education and Psychology
- Faculty of Mathematics and Statistics
- Faculty of Computer Engineering
- Faculty of Physics
- Faculty of Geographical Sciences and Planning
Cibiyoyin bincike da ginshiƙan kimiyya
- Economics Research Institute
- Energy Research Institute
- Ala Research Institute (endowment and charity studies)
- Research Institute of Geographical Sciences
- Environmental Research Institute
- Institute of Management
- Intelligent Processing and Systems Research Center
- Industrial and Organizational Psychology Research Center
- Natural and Biological Medicinal Products Research Center
- Research Center for Expressive Communication Technology
- Process Engineering Research Group
- Process Engineering Research Group
- Rasta Research Group
- The Research Group of Manuscript Research and Text Correction
- The Scientific Pole of Plant Antioxidants
- The Scientific Pole of Banach Algebra
- Scientific Pole of Geography and Urban-Regional Planning
- The Scientific Pole of Shiite Culture and Civilization Studies in the Safavid era
- The Scientific Pole of Fundamental and Applied Studies of Mystical Literature
- The Scientific Pole of the Psychology of Spirituality and Happiness
- Scientific Pole of International Economy
- Scientific Pole of Environmental Pollutants
- Scientific Hub of Economy and Urban Planning
- Future Research Think Tank
Kwasa-Kwasai
New Sciences and Technologies
- Nuclear Engineering (Masters da PhD)
- Biotechnology (Masters da PhD)
- Nano Engineering (Master’s Degree)
- Energy Engineering (Masters)
Educational Science
- Curriculum (Ph.D.)
- Educational Planning (Master’s Degree)
- Philosophy of Education (Master’s da Ph.D.)
- Educational Management (Master’s da Doctorate)
- Educational Technology (Bachelor)
Transportation and Traffic
- Transportation and Traffic
- Transportation Engineering (Master’s Degree)
Basic Sciences
- Pure and Applied Mathematics (Bachelor’s, Master’s, da PhD)
- Computer Science (Bachelor’s, Master’s)
- Physics (Bachelor’s, Master’s da PhD)
- Geology (Bachelor’s, Master’s da PhD)
- Chemistry (Bachelor’s, Master’s da Ph.D.)
- Biology with Genetics, Microbiology, Zoology and Botany Trends (Bachelor’s, Master’s da PhD)
- Statistics (bachelor’s, master’s da phd)
Literature and Humanities
- Persian the Literature
- Philosophy
- Sociology
- Theology
- History
- Geography
Engineering Sciences
- Electrical Engineering (electronics, power, telecommunications and control) bachelor’s, master’s da PhD.
- Computer Engineering (software and hardware) bachelor’s, master’s da PhD.
- Chemical Engineering (process) – bachelor’s, master’s da PhD.
- Medical Engineering (bioelectrical and biomechanic) Bachelor’s, Master’s
- Mapping Engineering
- Information Technology Engineering (IT) – Bachelor’s, Master’s da Ph.D.
- Mechanical Engineering (energy conversion and functional design)
- Civil Engineering
- Biotechnology Engineering
Foreign Languages
- English Language Translator (Bachelor’s, Master’s, Ph.D.)
- German Language
- Persian Language
- Arabic Language (bachelor’s, master’s, doctorate)
- English Language and Literature (Bachelor’s, Master’s)
- Armenian Language
- English Language Teaching (Bachelor’s, Master’s, Ph.D.)
- Teaching Chinese (BSc)
- Russian Language Teaching (BSc)
Administrative Sciences, Management and Economics
- MBA Management, Strategy, Operations and Supply Chain, Marketing, Human Resources
- Industrial, Commercial and Government Management
- Theoretical Economics, Commerce
- Political Science
- Law
- Acoounting
Physical Education
- Physical Education
Ababen More Rayuwa
Jami’ar Isfahan tana ɗauke da makarantu 14, ɗaya ce daga cikin manya-manyan jami’o’in ƙasar Iran. Baya ga abubuwa da jami’ar take da su kamar ɗakin taro, wurin cin abinci, azuzuwan karatu, sashen computer, jami’ar ta yi tanadin ɗakunan gwaje-gwaje (laboratories) na karatu da na bincike kusan guda 190, sassan koyarwa (departments), babban laburare tare da ƙananan laburaruka guda 5 a makarantu daban-daban, da kuma ɗakunan karatu guda 4 duk domin amfanuwar ɗalibai.
kasantuwar cewa garin na Isfahan yana tsakiyar ƙasar Iran ne sannan kuma muhallin da jami’ar take a cikin garin Isfahan shi ma wuri ne da yana kusan tsakiyar gari, Jami’ar Isfahan tana da sauƙin zuwa sosan gaske. Ana iya amfani da jirgin ƙasa na cikin gari wato metro, ko motocin autobus wurin kai-komo a wannan jami’ar. Domin shige da fice a garin na Isfahan kuma ɗalibai za su iya amfani da jirgin sama, jirgin ƙasa, ko motoci (kenan ana iya zuwa Isfahan daga wasu ƙasashen ma).
Laburaren Jami’ar Isfahan
Labureren na Jami’ar Isfahan yana ɗaya daga cikin manya-manyan laburarukan ƙasar Iran masu ɗauke da littafai da resources na ilimi masu yawan gaske. Ɗaliban jami’ar ta Isfahan za su iya amfanuwa da duka resources ɗin da ke cikin laburaren ta bayan sun nuna katinsu na makaranta. Hakazalika tsarin laburaren yana bada damar amfanuwa da waɗannan resources da articles ta online ga ɗalibai da sauran masu amfani da laburaren. Babban laburaren Jami’ar Isfahan na da sassa uku:
- Ma’ajiyar littafan farsi da na latin
- Ma’ajiyar bayanai da rubututtukan hannu
- Zauren littafan reference, theses, da mujallu
Baya ga wannan babban laburaren wanda shi ne hedikwatar sauran laburarukan, jami’ar na da laburare a Faculty of Literature and Humanities, akwai ɗaya a Faculty of Foreign Languages and Physical Education, akwai wani laburaren Azadegan wanda ya keɓanci kwasa-kwasan Economics, Engineering, da Technical, sai kuma laburaren hostel ɗin mata da na hostel ɗin maza.
Wurin kwanan ɗalibai
Kasantuwar cewa jami’ar na da ɗalibai masu yawan gaske, ta yi tanadin hostel guda 12 waɗanda suka haɗa da na mata da na maza, kuma waɗanda za su iya ɗauke mutum 4500. Baya ga masaukin ɗalibai, jami’ar ta yi tanadin cibiyar bada shawara, wurin cin abinci, filaye da kayan wasanni daban-daban, zauren gina jiki, da sauransu. Duka ɗaliban jami’ar za su iya amfani da sabis ɗin abinci na self wanda jami’ar ta tanada, akwai kuma gidajen cin abinci (restaurant) masu zaman kansu a cikin jami’ar waɗanda ke sayar wa ɗalibai da abinci a farashi mai sauƙi.
Abubuwan hostel
- Gidan cin abinci na Yas 2
- Raba abincin ɗalibai a cikin hostel
- Cibiyar kula da lafiya ɗauke da motar ambulance tare da direbobi 3
- Cibiyar tsaro da agaji
- Shagunan sayayya, wuraren gyaran gashi, shagunan photocopy da typing, shagunan ɗunki, duk a kusa da hostel ɗin ɗalibai
- Ofishin cibiyar makafi ta jami’ar a cikin hostel
- Gym
- Filin wasa na haki
- Filayen wasanni masu kwalta Filin basketball, volleyball, da sauransu
- Zauren wasan dart, kwallon hannu, chess, da table tennis
- Ɗakunan karatu da masallatai
- Tashoshin bus masu yawo cikin jami’ar
- Workshop na walda, kafinta, kayan lantarki, da sauransu
- Masaukin baƙi na ɗaliban da ba ‘yan hostel ba da kuma sauke baƙin ɗalibai daga wasu jami’o’in idan ana yin wani taro
Yanayin Wuri
Jami’ar na nan a garin Isfahan, titin Daneshga. A kusa da jami’ar akwai Cibiyar kasuwanci ta Sepher da wurin cin abinci na Wezara. Jami’ar Isfahan na ɗaya daga cikin jami’o’i masu kyau wannan yanki. Har ila yau, a kusa da jami’ar akwai tashar metro ta Azadi, cikin sauƙi ɗalibai da ma’aikatan jami’ar waɗanda ba su da ababen hawa za su iya zirga-zirga a jami’ar. Haka kuma amfani da irin waɗannan ababen hawa na jama’a yana taimakawa wurin rage gurɓacewar iska.
Adireshi: Isfahan, Meidane Azadi, University of Isfahan
Shafin jami’ar: https://www.ui.ac.ir