Karatu a Tehran University of Medical Sciences (dake cikin garin Tehran) kasantuwar ta ɗaya daga cikin jami’o’in gwamnati na Iran, da kuma matsayinta a harkar ilimi idan an kwantanta da sauran jami’o’i, yana ƙara kwaɗaitar da mutane duƙufa wajen neman sanin tarihin wannan jami’a da kuma bayanai akanta. Wannan jami’a tana ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya, jinya da karatun likitanci; ku cigaba da bibiyarmu.
Gabatarwa
Tehran University of Medical Sciences na ɗaya daga cikin jami’o’in gwamnati kuma tana ƙarƙashin kulawar hukumar kiwon lafiya, jinya da karatun likitanci a lardin Tehran, kuma ta samo asali ne daga makarantar likitanci ta Daral-Funun, sannan ana kallonta a matsayin cibiyar ilimin likitanci mafi tsufa a Iran.
Tun bayan assasa ta, zuwa yanzu an canja ma jami’ar wuri sau biyu, daga bisani a shekarar 1937 aka dawo da ita muhallinta na yanzu. A shekarar 1940 aka assasa wannan jami’a kuma shugabancinta yana hannun Dr. Ali Jaafariyan. A shekarar 1986 a bisa sabon umarnin gwamnati aka raba kwalejojin ilimin likitanci da junansu, hakan ya basu damar tattaruwa suka zama jami’ar Tehran University of Medical Sciences and Health Services.
A halin yanzu wannan jami’a tana da ɗalibai 13300 da malamai 1650. Bincike ya nuna cewa wannan jami’ar ta buga maƙaloli 9718 na ilimin kimiyya a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, mawallafiyar mujalloli 31 na musamman, ta shirya taruka 56 kuma ta fitar da tantattacciyar maƙala ta ƙasa da ƙasa guda 74356.
Matsayin Tehran University of Medical Sciences
Bisa rahoton hulɗa da jama’a na mataimakin shugaban ƙasa da ƙasa, tsarin Shanghai na ɗaya daga cikin manyan tsare-tsare uku da aka amince da su a duniya, inji sakamakon da Jami’ar Shanghai Jiaotong ta fitar. Tehran University of Medical Sciences ita da Sharif University of Technology na matsayi na 601 zuwa 800, waɗannan jami’o’in biyu sun samu nasarar lashe matsayi na 2 a tare.
Makarantu
_Makarantar Public Health
_Makarantar Pharmacy
_Makarantar Medicine
_Makarantar Dentistry
_Makarantar Rehabilitation
_Makarantar Nursing & Midwifery
_Makarantar Allied Medical Sciences
_Makarantar Persian Medicine
_Makarantar Advanced Technologies in Medicine
_Makarantar Nutritional Sciences & Dietetics
_Virtual School
Asibitoci
Tehran University of Medical Sciences (TUMS) nada jimillar asibitocin koyarwa guda 16 ɗauke da gadajen asibiti guda 4000, asibitocin sun haɗa da:
_Asibitin mata ta Arash
_Asibitin Imam Khomeini
_Asibitin Amir A’alam
_Cibiyar Cancer
_Asibitin Baharloo
_Asibitin yara na Bahrami
_Asibitin Razi
_Asibitin Rozbeh
_Asibitin mata na Yas
_Asibitin Sina
_Asibitin Shariati
_Asibitin Ziya’eyan
_Asibitin Farabi
_Cibiyar Kiwon Lafiya ta yara
_Cibiyar zuciya Tehran
_Asibitin Vali-Asr
Cibiyoyin Bincike
_Cibiyar Bincike da Horarwa akan cututtukan fata da kuturta
_Cibiyar Bincike ta Ilimin Kimiyya da Fasaha a likitanci
_Cibiyar Binciken Hematology- Oncology and Stem Cell Transplantation
_Cibiyar Binciken Immunology, Asthma, and Allergy
_Cibiyar Binciken Trauma and Surgery
_Cibiyar Binciken Reproductive Health ta Vali-Asr
_Cibiyar Binciken Sports Medicine
_Cibiyar Binciken Pharmaceutical Sciences
_Cibiyar Bincike akan Muhalli
_Cibiyar Binciken akan Cancer
_Cibiyar Binciken Ilimin Kimiyya ta Ɗalibai
_Cibiyar Bincike akan Haƙori
_Cibiyar Bincike akan tiyata da dashen zuciya
_Cibiyar Binciken Endocrinology and Metabolism
_Cibiyar Binciken Rheumatology
_Cibiyar Binciken Brain and Nervous Diseases
_Cibiyar Bincike akan Ɗabi’u da Tarihin Likitanci
_Cibiyar Binciken Cerebrospinal Lesion Repair
_Cibiyar Bincike akan Kunne, Hanci da Maƙogwaro
_Cibiyar Bincike akan Tsirrai masu magani
_Cibiyar Binciken Psychiatry daPsychology
_Cibiyar Binciken Urology
_Cibiyar kula da Zuciya ta Tehran
_Cibiyar Binciken Gastrointestinal and Liver Diseases
_Cibiyar Bincike akan Ido
_Cibiyar Bincike akan Girma da Cigaban Yara Ƙanana
_Cibiyar Bincike akan HIV/AIDS ta Iran
_Cibiyar Binciken Nanotechnology
_Cibiyar Binciken Nuclear Medicine
_Cibiyar Binciken Health Information Management
_Tushen Binciken Demographic
_Cibiyar Binciken Pediatric Urology
_Cibiyar Bincike akan Immunology
_Cibiyar Binciken Pediatric Infectious Diseases
_Cibiyar Bincike akan Qur’an, Hadith da Likitanci
_Laser Research Center of Dentistry
_Cibiyar Binciken Autoimmune Bullous Diseases
_Cibiyar Binciken Electrophysiology
_Cibiyar Binciken Advanced Diagnostic and Interventional Radiology
_Cibiyar Bincike akan Growth and Development
_Cibiyar Bincike akan Biotechnology
_Cibiyar Bincike akan Drug Design and Development
_Cibiyar Binciken Nephrology
_Maternal, Fetal, and Neonatal Research Center
_Cibiyar Binciken Occupational Medicine
_Cibiyar Binciken Health Knowledge Exploitation
_Cibiyar Bincike akan Magungunan Gargajiya na Iran
_Cibiyar Binciken Nursing and Midwifery Care
_Cibiyar Bincike akan Molecular and Cellular Imaging
_Cibiyar Bincike akan Islamic and Complementary Medicine
_Razi Institute for Drug Research
_Cibiyar Binciken ENT, Head and Neck
_Cibiyar Bincike akan Immunology
_Cibiyar Bincike akan Ido ta Asibitin Rasulul Akram
_Center for Nursing Care Research
_Cibiyar Bincike akan Lafiyar Ƙwaƙwalwa
_Rehabilitation Research Center
_Cibiyar Bincike akan Pathology da Cancer
_Occupational Research Center
_Cibiyar Bincike akan Digestive Diseases
_Cibiyar Bincike akan ƙuna
_Cibiyar Bincike akan Physiology
_Cibiyar Bincike akan Pediatric Infectious Diseases
_Cibiyar Bincike ta Occupational Health
_Center for Educational Research in Medical Sciences
_Cibiyar Bincike akan Antimicrobial Resistance
_Cibiyar Bincike akan Endocrine
_Cibiyar Bincike akan Shayarwa
_Iranian National Center for Addiction Studies
Jadawalin kuɗin makakarantar Tehran University of Medical Sciences
Kuɗin makarantar shekara na Kwasa-Kwasan likitanci (a dala) | Kwas | Farashi a dala |
---|---|---|
Doctor of Medicine(M.D.) | $6000 | |
Bachelor of Medicine and Bachelor of Surgery(M.B.B.S.) | $6000 | |
Doctor of Dental Surgery (D.D.S) | $3750 | |
Bachelor of Dental Sciences (B.D.S) | $3500 | |
Doctor of Pharmacy (pharm.D) | $3000 | |
Master of Pharmacy (M.pharm) | $3000 | |
Bachelor of Science (B.Sc) | $2000 | |
B.Sc in Life Science | $2000 | |
Kwasa-Kwasan Masters da M.SC | $3000 | |
Kwasa-Kwasan Ph.D | $5000 | |
Speciality | $5000 | |
Subspeciality | 5000$ | |
Fellowship | $5000 |
Kuɗin Makarantar karatun Dental | Kwas | Farashi a dala | |||
---|---|---|---|---|---|
M.Sc | Ph.D | Specialty | Fellowship | ||
Orthodontics | $19500 | – | $13000 | – | |
Periodontics | $1500 | – | $11000 | $6000 | |
Restorative Dentistry | $1500 | – | $11000 | – | |
Endodontics | $1500 | – | $11000 | – | |
Prosthodontics | $1500 | – | $11000 | $6000 | |
Oral & Maxillofacial Surgery | – | – | $11000 | $6000 | |
Dental Biomaterials | – | $13000 | – | – | |
Pediatric Dentistry | $11250 | $7000 | $6000 | ||
Oral & Maxillofacial Pathology | $11250 | $7000 | – | ||
Oral & Maxillofacial Radiology | $11250 | $7000 | – | ||
Oral & Maxillofacial Medicine | $11250 | $7000 | – | ||
Community Oral Health | $6000 | $5000 | – | – |
Sauran kuɗaɗen da ake biya | Kuɗin | Farashi a dala | Lokacin biya |
---|---|---|---|
Kuɗin Registration | $50 | Lokaci ɗaya ake biya | |
Jigila daga filin jirgin Tehran zuwa makaranta (idan ana buƙata) | $25 | Lokaci ɗaya ake biya | |
Masauki mai kayayyakin amfani (idan ana buƙata) | $70-$100 | Duk wata | |
Inshorar iyalin Ɗalibi (lafiya) | $10 | Akan kowane mutum ɗaya ba tare da la’akari da bambancin shekaru ba | |
Inshorar Ɗalibi | $20 | Akan kowane mutum ɗaya ba tare da la’akari da bambancin shekaru ba | |
Visa (izinin zama na shekara 1) | $6 | Duk shekara | |
Visa (shigowar ɗalibi) | $50 | Lokaci ɗaya ake biya | |
Jarabawar farko ta gwajin gogewa a yaren farsi | $15 | Lokaci ɗaya ake biya | |
Azuzuwan koyon farsi (idan akwai buƙata) | $400 | Zama 160 | |
Jarabawar farko ta gwajin gogewa a harshen turanci | $15 | Lokaci ɗaya ake biya | |
Azuzuwan koyon turanci (idan akwai buƙata) | $475 | Zama 150 |
Kuɗin koyon turanci | Mataki | Lokaci | Farashi (Dala) | Farashi (Euro) |
---|---|---|---|---|
Beginner | 60 | $757 | 631 | |
Elementary 1 | 40 | $505 | 421 | |
Elementary 2 | 40 | $505 | 421 | |
Pre IELTS 1 | 55 | $694 | 578 | |
Pre IELTS 2 | 55 | $694 | 578 | |
Kuɗin koyon farsi | Matakin farko | 80 | $495 | 413 |
Mataki na 2 | 80 | $495 | 413 | |
Mataki na 3 | 80 | $495 | 413 | |
Gama Gari | 80 | $495 | 413 | |
Matakin Gama Gari | 20 | $100 | 83 | |
Tattaunawa | 20 | $100 | 83 | |
Ajin ƙarfafa Farsi saboda project (bisa zaɓi) | Mafarin rubutu | 20 | $100 | 83 |
Rubutu da gina jumla | 20 | $100 | 83 | |
Rubutu a sauƙaƙe | 20 | $100 | 83 |
Jarabawar yaren farsi | Sunan Jarabawa | Farashi (Dala) | Farashi (Euro) |
---|---|---|---|
Jarabawar ayyana aji | $15 | 13 | |
Sake jarabawar ayyana aji | $50 | 42 | |
English & Persian | $50 | 42 |
Kwasa-Kwasan karatu a Tehran University of Medical Sciences
A Tehran University of Medical Sciences ana samun Kwasa-Kwasan karatu kamar haka:
_Ergonomics
_Immunology
_Epidemiology
_Midwifery
_Psychiatric Nursing
_Biomedical Engineering
_Occupational Therapy
_Speech Therapy
_Nursing
_Medical Biotechnology
_Librarianship and Medical Information
_Bacteriology
_Cardiac anesthesia
_Kidney transplant
_Cancer Surgery
_Heart Failure
_Pediatric Surgery
_Vascular Surgery
_Infants
_Da sauransu
Ku sauke wannan fayil domin samun cikakken bayani game da kwasa-kwasan karatu da kuma yiwuwar karatu a matakin da kuke so.
Cibiyoyin Bincike
_Endocrine Clinical Sciences Research Institute
_Pharmaceutical Sciences Research Institute
_Institute of Neurological Research
_Digestive Diseases Research Institute
_Research Institute of Cardiovascular Diseases
_Research Institute for Reducing Risky Behavior
_Cancer Institute
_Environmental Research Institute
_Endocrine Demographic Sciences Research Institute
_Research Institute of Advanced Medical Technologies and Equipment
_Research Institute of Cell and Molecular Sciences of Gland
_Research Institute of Dental Sciences
_Family Health Research Institute
Abubuwan more rayuwa
Hidimomin da ake gabatar wa ɗalibai sun haɗa da; Bada bashin karatu, bashin gida, bashin domin buƙatu, biyan amanar haya, Bashin gidauniyar Alavi, Tabsara 2 (ga ɗalibai masu biyan kuɗin makaranta), Tabsara 2 (sashen ɗaliban waje), inshorar haɗurra, inshorar ƙwararrun ɗalibai da ɗaliban PhD, sauran ayyukan ɗalibai.
Masauki:Ga ɗaliban da suke wajen Tehran, jami’ar ta yi tanadin da ya dace domin masaukinsu wanda wannan alhakin yana wuyan sashen tafiyar da al’amuran da suka shafi al’adun ɗalibai. Wuraren kwanan ɗalibai suna cikin harabar jami’ar, suna ɗauke da masaukai da dama na ɗalibai (domin ɗalibai a dukan matakan karatu). Akwai wuraren walwala da sauran wurare kamar Ɗakin karatu,shagon litattafai, masallaci, ɗakin taro, ɗakin wasanni, sinama da sauransu. An tanadi Hostell 11 domin amfanin maza, 6 domin amfanin mata da kuma ɗaya saboda masu iyali. Hostel ɗin mata yana ɗaukar mutum 1450, na maza kuma yana ɗaukar mutum 1860. Wurin kwanan masu aure kuma yana ɗaukar iyali 130. Motar jigilar ɗalibai daga ƙofar ko wane hostel zuwa harabar makaranta, kwalejoji da asibitoci daban-daban, ta baiwa ɗalibai damar zirga-zirga cikin sauri kuma cikin sauƙi.
Abinci: Wuraren cin abinci na jami’ar wanda ke akwai a kwalejoji da asibitoci, sun samar da abinci mai inganci a farashi mai sauƙi ga ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shagunan kayan abinci na cikin jami’ar suma suna ƙoƙarin samarwa ɗalibai kayan abinci a tsawon ranaku.
Physical health of students – The Student Health Center: This center provides health and treatment services to students with the use of experienced university professors in the form of general and specialized clinics, dental clinics and vaccination services.It provides emergency medical services to students living in the university.
Lafiyar ƙwaƙwalwa da tunanin ɗalibai_Cibiyar shawarwari da jagorancin ɗalibai: Wannan cibiya tana ƙoƙari a fagage mabambanta tare da taimakon ƙwararru daban-daban, ciki har da Psychologists, Neuropsychologists, da sauransu. Daga cikin ayyukan wannan cibiya akwai bada shawara akan matsalolin da suka shafi ƙawa zuci, matsalolin tunani da ɗabi’un ɗalibai, da taimaka musu wurin koyon zama da mutane da yanke shawara mai kyau; shawara akan auratayya da taimakawa wurin magance mastalolin iyali; samarwa ɗalibi da kayan aiki domin magance matsalolin tattalin arziki; shirya tarukan bita da horo akan batutuwa daban-daban kamar ilmantarwa, maida hankali, koyarda dabarun karatu, taimaka musu wajen warware matsalolin karatu; haɗa kai da ahalinsu domin basu shawara, da kuma gabatar musu da laccoci da suka shafi ilmantarwa akan nazarin halayya.
Abubuwan Alfahari
_Nasarar da ƙungiyar kula da tattakin arziki da tafiyar da harkar magunguna ta samu na lashe lambar yabon ƙungiyar International Association of Medicine and Economics(ISPOR)
_Tehran University of Medical Sciences ta lashe lambar zinare ta tsarin RUR International Ranking System.
_Bayyana malaman sashen kiwon lafiya a matsayin masu bincike na kwarai a bikin Bincike da Fasaha karo na 29 na jami’ar Tehran.
_An bada lambar yabon taron ƙasa mai taken “Mata da Kimiyya” karo na uku (Kyautar Maryam Mirzakhani) ga Tehran University of Medical Sciences.
Muhallin Tehran University of Medical Sciences
Wannan jami’a tana na a titin Poorsina. Sannan tana kusa da muhimman wurare kamar asibitin Arya, Gidan tarihi na Gurbe, Mohr va Plastiksazi Javidan, Westland Fast food, Bolvar Hotel, Cafe Panjare, Gidan cin abinci na Bolvar Hotel, da Masallacin Tehran University.
Magana da Tehran University of Medical Science
Adireshi: Tehran University of Medical Sciences Headquarters, Qods St, Keshavarz Blvd, Tehran, Iran.
Tambayoyin da ake yawan yi game da Tehran University of Medical Science
- Wasu irin takardu ake buƙata domin yin rajista a Tehran University of Medical Science?
Passport, hoto, script na results, results, CV, Motivation letter, Recommendation letter. - Ya ake biyan kuɗin makaranta?
A wannan jami’a ana biyan kuɗin makaranta da kuɗaɗen ƙasar waje ne. - Shin sai da bizar karatu za’a iya shiga aji?
Eh, lazim ne ɗalibin da zai shiga aji ya zama yana da bizar karatu.
[neshan-map id=”6″]