[gtranslate]
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Tabriz

Karatu a Tabriz

Loading

Tabriz ɗaya ne daga cikin tsofaffin garuruwan Iran wanda sakamakon samuwar cibiyoyin ilimi kamar: University of Tabriz, Sahand University of Technology, Technical and Vocational University, da Tabriz University of Medical Sciences, gari ne da ya dace da karatun ɗalibai. Ku kasance tare da mu domin samun bayanai idan kuna shirin yin karatu a Tabriz.

Karatu a Tabriz

Tabriz

Babban gari ne a yankin Azarbaijan kuma shi ne cibiyar lardin Azarbaijan Sharqi. Akwai kimanin mutum 1,643,960. Shi ne gari na biyar mafi yawan jama’a.

Mutanen garin na magana ne da yaren turkanci da lahajar Tabrizi. Tabriz na cikin garuruwan duniya waɗanda suka daɗe kuma ya kasance birnin tarayyar ƙasar Iran a dauloli mabambanta, haka shi ne cibiyar ƙasar ta biyu a zamanin mulkin Qajariyawa. Garin ya kasance gari na biyar mafi yawan jama’a a lokacin Safawiyawa da kuma shekara ta 1500 miladiyya, kuma yawan mutanensa ya zo daidai da na Istanbul – birnin tarayya na daular Ottoman.

Bayani a kan Tabriz

Zirga-Zirga

Za ku iya amfani da hanyoyin sama da na ƙasa cikin sauƙi domin zuwa garin Tabriz yawo ko karatu.

Akwai filin jirgi mai suna Tabriz International Airport a tsakiyar garin Tabriz. A wannan filin jirgin akwai jirage masu tashi daga Tabriz zuwa ƙasashen waje; zuwa garuruwan Erzurum, Izmir, Sparta, Istanbul, Hamburg, Baku, Baghdad, Tbilisi, Jeddah, Dubai, Damascus da Madinah.

Layin dogo na Tabriz ɗaya daga cikin hanyoyin jirgin ƙasa na Iran masu muhimmanci, yana ɗauke da hanyar jirgin ƙasa ta ƙasa da ƙasa ta Tabriz – Nakhchivan. Daga cikin hanyoyin jirgin ƙasa na cikin gida akwai layin Tarbiz – Tehran, da Tabriz – Mashhad.

Garin Tabriz na da tashoshin mota guda biyu kamar haka; Tashar Markazi da Tashar Shomal Gharb. Tashar Markazi ita ce tashar farko a ƙasar Iran.

An buɗe layin farko na metro mai zangon kilomita 8 wanda ya fara daga tashar Ilgoli zuwa tashar Ostad Shahryar tare da jirgin ƙasa na metro guda biyu masu tarago 10, a ranar 27 ga watan August, shekarar 2015. Tabriz ne gari na 4 da ya mallaki metro a ƙasar Iran.

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

Garin Tabriz na da yalwar koren sarari da ciyayi sakamakon yanayin iska da yake da shi mai kyau a tsawon shekara. A garin Tabriz akwai park guda 132. Daga ciki akwai Shah Goli Park wanda shi ne park mafi shahara a garin Tabriz kuma babban tambari ne da ke alamta garin. Garin Tabriz na cikin garuruwan da suka daɗe a harkar film. A garin Tabriz aka ƙiƙiri Shekarar Sinama ta farko mai taken “Soli Cinema” a shekarar 1900 a Iran.

Jami'o'in Tabriz

Karatu a Tabriz

A lokacin mulkin Khod Mokhtar na Azarbaijan a shekarar 1945, an samar da Jami’ar Tabriz bisa umarnin Sayyed Ja’afar Pishevari. Daga bisani a shekarar 1947 aka assasa Jami’ar Tabriz a hukumance bisa amincewar majalisar zartarwa ta ƙasa. Ga salon sanya wa jami’ar suna kamar haka: A shekarar 1947 (shekarar da aka assasa jami’ar) an saka mata suna “Jami’ar Tabriz”. Bayan ƴan shekaru aka canja sunan jami’ar zuwa “Jami’ar Azar Abadegan”. Bayan juyin musulunci a ƙasar Iran a shekarar 1979 aka sake maida mata tsohon sunanta wato “Jami’ar Tabriz”. Bayan wani lokaci kuma aka rabata da “Jami’ar kimiyyar Likitanci ta Tabriz“. Yanzu haka garin Tabriz shi ne gari na biyu na jami’o’i a Iran. Domin samun ƙarin bayani a kan jami’o’in da muka ambata za ku iya karanta maƙalolinmu na Karatu a Tabriz University of Medical Sciences da Karatu a University of Tabriz.Abubuwan kallo a garin Tabriz

Dalilin karatu a Tabriz

  • Babu shakka garin Tabriz ɗaya ne daga cikin garuruwa masu yanayin da ya dace da karatu dalili kuwa shi ne akwai rangwamen kuɗin makaranta a garin idan an kwatanta shi da sauran manyan garuruwa irinsu Tehran da sauransu. To amma kuɗin muhalli na iya zame kumu matsala. Saboda haka abunda ya fi shi ne ku yi amfani da hostel ko masaukan baƙi da suke cikin gari.
  • Jami’ar Tabriz na daga cikin jami’o’i mafi kyau kuma mafi inganci na ƙasar Iran kuma takardar shaidar kammala karatu da take ba ɗalibai karɓaɓɓiya ce a sauran ƙasashen duniya. Jami’ar ta tanadarwa ɗalibanta ingantattun kayan aiki da na koyarwa irin su laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, wuraren shaƙatawa da na wasanni, wuraren cin abinci, da sauransu.

Bayani a kan birnin Maragheh

Garin Maragheh shi ne babban gari na biyu a lardin Azarbaijan Sharqi. Garin Maragheh ya shahara da laƙabin “Cibiyar Ilimin Taurari” da kuma “Bagh Shahr Iran” kuma yana cikin garuruwan tarihi na ƙasar. Manufarmu a wannan rubutu ita ce kawo muku sharhi a kan yanayin iska, al’adu, yawon buɗe ido, karatu, da sauransu na wannan gari.
An samo sunan garin daga kalmar “Mar Agha” wanda hakan na nufin “Wurin Dattawa”. Saboda maƙotaka da kogin Sufiy Chai da dutsen Sahand, yana da madaidaicin yanayi a lokacin zafi amma yana da sanyi sosai a lokacin sanyi. Ana fara dussar ƙanƙara wato snow daga watannin ƙashen shekara har zuwa farkon wata shekara, ana yin ruwan sama a lokacin bazara wanda mutanen garin na kiran irin wannan ruwan saman da suna “Nissan”. Mutanen garin na magana ne da yaren turkanci sannan mafi yawansu musulmi ne masu bin mazhabin shi’a.

Karatu a MaraghehKaratu a Maragheh

Fitattun jami’o’in garin Maragheh su ne Jami’ar Maragheh da Jami’ar Shahid Madani. Kuna iya karanta maƙalolinmu na Karatu a Jami’ar Maragheh da Karatu a Jami’ar Shahid Madani domin samun ƙarin bayani.

Jami'o'in MaraghehNishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

A garin Maragheh akwai wuraren shaƙatawa da yawon buɗe ido dama wanda hakan ya sa garin ya zama ɗaya daga ciki wuraren yawon buɗe ido wanda a kowace shekara ana samun baƙi da yawa masu zuwa. Samuwar observatory a garin shi ne ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawowa garin shuhura.
_ Gonbad Kaboud
_ Gidan Ashraf Almuluk Naba’i Vand
_ Maragheh Observatory
_ Makwancin Awhadi Maraghai
_ Majami’ar Mehr
_ Gonbad Sorkh
_ Gowijeh Qal’eh
_ Gonbad Ghafarieh
_ Cocin Havanes
_ Hasumiyar Madur
_ Gadar Sarcheshme ta ƙauyen Mordagh
_ Tappe Qal’eh Jamal Abad
_ Gidan tarihin rubututtukan dutse na Maragheh
_ Gidan tarihi na Ilkhani
_ Gor Dagh Waterfall
_ Kogon Kaboutar
_ Maɓuɓɓugar ruwa ta Geshayesh
_ Da sauransu…

Abubuwan burgewa a MaraghehHotal Hotal

_ Maragheh Grand Hotel
_ Hotel Alliance

Laburaruka

_ Awhadi Margahei
_ Khaje Nasiraldin Toosi
_ Saminal A’immeh
_ Chahardah Ma’asoum
_ Babban laburaren Maragheh
_ Da sauransu…

Bayanai a kan MaraghehWuraren kasuwanci

_ Kabood Boutique Stylish
_ Babbar kasuwar busassun ƴaƴan itace ta Maragheh
_ Pasaj Jam Jam
_ Mehr Shopping Center
_ Atiq Shopping Center
_ Melki Shopping Center
_ Ati Center
_ City Star Shopping Center
_ Pasaj Atieh Shopping Complex
_ Pasaj Amirkabir
_ Da sauransu…

Bayani akan birnin Sahand

Ɗaya ne daga cikin garuruwa sabbin ƙirƙira a lardin Azarbaijan Sharqi. Ya zama gari mai zaman kansa ne a shekarar 2008. An kafa garin ne da manufar rage yawan mutane Tabriz sannan mutane sun yi na’am da hakan. A ƙirgen da aka yi a shekarar 2016, an samu mutum 82494 da ke zama a garin Sahand. Mutanen garin na magana da harshen turkanci ne kamar dai sauran garuruwan yankin Azarbaijan.

Karatu a Sahand

Daga cikin fitattun cibiyoyin koyarwa na wannan gari akwai Jami’ar Sahand. Za ku iya komawa ga maƙalarmu ta Karatu a Jami’ar Sahand domin samun ƙarin bayani.

 

Related Posts
Leave a Reply