Garin Semnan ɗaya ne daga cikin garuruwan ƙasar Iran kuma shi ne babban birnin lardin Semnan. Ku kasance tare da mu domin samun bayanan da suka danganci yanayin karatu a wannan gari na Semnan.
Semnan
Semnan wani gari ne a ƙasar Iran sannan kuma cibiyar lardin Semnan. Garin na Semnan na nan a kudancin dutsen Alborz, kilomita 216 daga Tehran a kan hanyar Tehran – Khorasan. Garin Semnan ya haɗa iyaka da garin Damghan ta gabas, ta arewa yana da iyaka da garin Mahdi Shahr, ta yamma kuma yana maƙotaka da garin Sorkhe. Garin Semnan na a tsayin digiri 53 da daƙiƙa 23 da faɗin digiri 35 da daƙiƙa 34 a ma’aunin Geography, sannan kuma a tsayin mita 1130 daga saman teku.
Garin Semnan ya kasance cibiyar ayyukan sararin samaniya na ƙasar Iran tun daga wuraren 2011. Ƙungiyar masana’antun sararin samaniya na da sansani a kilomita 45 daga kudu maso gabacin garin Semnan, tana kuma da wani sansani a kilomita 80 daga kudu maso gabacin garin har ila yau inda ake gudanar da ayyukan harba tauraron ɗan’adam zuwa sararin samaniya, da rokoki masu cin dogon zango. Daga shekarar 2008 ne aka canja sunan hanyar soja wadda ta sada garin Semnan da sansanonin sojan sama, zuwa “Titin Safir Omid”. Hakazalika an canja sunan sansanin sararin samaniya na lardin Semnan a ranar 4 ga watan June na shekarar 2012, zuwa “Imam Khomeini Space Base”.
Lardin Semnan ya ƙunshi garuruwa guda 8; Semnan, Shahrud, Damghan, Garmsar, Mahdishahr, Aradan, Mayamey, da garin Sorkhe. Bayanan ƙirge na shekarar 2016 sun nuna cewa akwai mutum 185129 a garin Semnan. Ƙabilar mutanen Semnan ita ce “Aryayi”.
Zirga-Zirga
Nisan Semnan zuwa Tehran kilomita 216 ne, sannan yana da hanyar jirgin ƙasa wadda ta sadu da babban layin jirgin ƙasa na Tehran – Mashhad, hakazalika akwai filin jirgin sama a garin. Garin Semnan shi ne gari mafi yawan jama’a a lardin. Yana da yanayi mai zafi tare da busasshiyar iska. A shekarar 2013 garin Semnan na daga cikin garuruwan da aka so a maida babban birnin tarayya na ƙasar Iran.
Wuraren shaƙatawa
Tsofaffin wuraren tarihi
Baya ga kyau irin na ɗabi’a da wannan gari yake da shi akwai abubuwan tarihi masu yawa dalilin kasancewarsa a cikin muhimman waƙi’o’in tarihi, garin na da abubuwan tarihi tun na dauloli mabambanta kuma daɗaɗɗu irin su:
- Babban Masallaci
Babban masallacin Zavaqan - Hasumiyar Seljuk ta babban masallaci Shi ne ginin hasumiyar masallaci mafi daɗewa a ƙasar Iran, akwai wani katako a tsakiyar hasumiyar wanda idan aka mosta shi duka hasumiyar na motsawa.
- Masallacin Imam (masallacin shah ko sultan)
- Gidan wanka na Hazrat
- Gidan tarihi na gidan wankan Pahne
- Gidan wanka na Nasar
- Gidan wanka na Gholi
- Gidan wanka na Nokhost
- Ƙofar Arg
- Ginin Daral Hukumeh (Meidane Abuzar)
- Kasuwar Semnan
- Kasuwar Mordeha
- Kasuwar Shaikh Ala’ul Daulah
- Borj Chehel Dokhtaran
- Qal’e Saru
- Qal’e Pachnar
- Qal’e Kushmaghan
- Qal’e Zavghan
- Qal’e Kohn Daj
- Daj Charmineh
- Masaukin baƙi na Sangi Ahwan (tun ƙarni na 5 bayan hijira)
- Masaukin baƙi na Shah Solaimani Ahwan
- Masaukin baƙi na Shah Abbasi (Safawieh)
- Makwancin Shaikh Ala’ud Daulah Semnani
- Makwancin Hakim Ilahi Semnani
- Makwancin Pir Najm Al-Din
- Maƙabartar Dariush Mahmud
- Rizabuwar ruwa ta Nasar
- Rizabuwar ruwa ta Karkhane
- Rizabuwar ruwa ta Kohnedaj
- Rizabuwar ruwa ta Tawakkuli
- Tappe Nasar
- Makarantar Haj Fath Ali Big
- Makarantar Sadegh Khan
- Yakhdan Ateshgah
- Bayan su akwai wasu rizabuwoyi da hanyoyin ruwa masu salon gini na musamman irin na zamanin baya da tsoffin rubuce-rubucen garin Semnan.
- Gidajen tarihi
- Gidan tarihi na gidan wankan Pahne
- Park ɗin gidan tarihi na Difa Moghaddas
- Gidan tarihi na Honar haye Ma’aser
Gidajen tarihi
- Gidan tarihi na Garmabeh Pahne
- Fada da lambun Amir
- Wurin parking na gidan tarihi na Difa Moghaddas
- Gidan tarihi na Honar haye Ma’aser
- Gidan tarihi na Hayat Wahsh
- Gidan tarihi na Sekkeh
Wuraren addini
- Qadamgah Abbas bn Ali
- Baqi’eh Payambaran
- Imamzadeh Yahya bn Musal Kazim (ɗan’uwan Imam Rida)
- Imamzadeh Ali bn Jaafar
- Mosalla Bozorg Semnan (Wurin sallar juma’a)
Asibitoci
- Shifa
- Kausar Medical Research Training Center
- Amirul Muminin Educational and Therapeutic Center
- Asibitin Sina (private)
- Asibitin Khatamal Anbiya
Wuraren kwana
Daga cikin hotal-hotal masu kyau na lardin Semnan akwai; Sangsar Hotel, Darband Hotel, Gootkemall Hotel, da Jahangardi Hotel. Akwai kuma hotal ɗin gargajiya na Khane-gol wanda zai dace da mutanen da sun fi sha’awar wuraren gargajiya.
Karatu a Semnan
Kamar yadda muka ambata cewa garin Semnan na ɗaya daga cikin muhimman garuruwan ƙasar Iran masu ɗimbin tarihi, garin na da yanayi mai kyau ga ma’abota neman ilimi. Daga cikin manyan jami’o’in lardin Semnan akwai Semnan University,Semnan University of Medical Sciences,Damghan University, da Shahrood University of Technology. Akwai cibiyoyin ilimi da jami’o’i 23 a lardin Semnan. Jami’o’in wannan lardi na Semnan sun keɓantu da wallafa mujallu 43 na musamman kuma sun wallafa jimillar mujallu 735 zuwa yanzu.
Har ila yau, lardin Semnan ya karɓi baƙuncin taruka 107 na ilimi da tarukan laccocin ilimi guda 12. Masu bincike daga jami’o’in lardin Semnan sun yi nasarar wallafa maƙala 62862 na ilimi waɗanda suka haɗa da maƙalar mujalla guda 11820, maƙalar taro guda 32332, da kuma wasu maƙaloli a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2018 an samu jimillar ɗalibai 65589 masu karatu a jami’o’in lardin Semnan tare da malamai 3617.
Dalilin karatu a Semnan
Saboda maƙotakar lardin Semnan da lardin Markazi da arewacin ƙasar, yanayin iskarsa ya sha bamban da na sauran wurare. Hakazalika akwai sauƙin tsadar rayuwa a lardin Semnan idan an kwatanta da sauran larduka.
Jami’o’in lardin Semnan irinsu Semnan University wadda a tsarin ranking na TIMES a shekarar 2023 ta samu shiga jerin fitattun jami’o’i 50 daga cikin jami’o’in ma’aikatar ilimi da jami’o’in hukumar lafiya ta Iran. Hakazalika akwai Damghan University wadda ita kuma a tsarin ranking na ‘Nature Index’ ta zo a matsayin jami’a ta goma a jami’o’in ƙasar Iran.
Wannan na daga cikin dalilan da suka maida lardin Semnan wuri da ya dace da karatu.