تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Ilam

Karatu a Ilam

Loading

Mun tattara muku bayanai game da karatu a garin Ilam wanda nan ne cibiyar lardin Ilam, tun daga kan bayanai da suka shafi yanayin geograpghy na wurin har zuwa muhimman wurare da kayan aiki na garin. Garin Ilam na kewaye da tsaunuka da dazuzzuka, kuma yana da madaidaicin yanayi.

Karatu a IlamIlam

Garin na Ilam mai girman hekta 67.212804 kenan kaso 62.10 na gabaɗayan lardin Ilam, a ma’aunin geography garin Ilam na nan tsakanin faɗin digiri 33 da mintuna 21 da sakanni 30 zuwa digiri 33 da mintuna 51 da sakanni 48 arewa, da tsayin digiri 45 da mintuna 41 da sakanni 7 zuwa digiri 46 da mintuna 51 da sakanni 19 ta gabas, sannan yana maƙotaka da garuruwan Ivan, Sirvan, Chardavol, Darreshahr, Mehran, da kuma ƙasar Iraq. Ta arewa akwai duwatsun Shanchir, ta gabas duwatsun Shalam, ta yamma akwai dutsen Qalaghir da kuma dutsen Kuh Kabir a kudancin garin Ilam.

Har ila yau garin na Ilam na kewaye da duwatsu da dazuzzuka sannan yana da madaidaicin yanayi da ƙiyasin ruwan sama kimanin milimita 619 a shekara, da awon ɗumin yanayi na darajar centigrade 13.6 zuwa 31.2.

Bayanan sansanonin nazari sun nuna cewa watan January ne wata mafi sanyi inda shi kuma watan June yake mafi zafi. Yanayin iskar na canzawa ne daga watan June ya ci gaba da sanyaya har zuwa wuraren September.

Karatu a Ilam

Zirga-Zirga

Filin jirgi na Ilam na daga cikin filayen jirgi da jiragen cikin gida kawai ke sauka a cikinsu. A garin Ilam, da gabaɗayan lardin Ilam babu hanyar jirgin ƙasa saboda haka ba a zuwa garin Ilam ta jirgin ƙasa. Kodayake za a iya hawa jirgin ƙasa a je Khuzestan daga can a ƙarasa Ilam. Amma ana zuwa da mota ta hanyoyi mabambanta. Hanyar Kermanshah – Ilam ita ce hanya mafi sauƙi ta zuwa garin Ilam idan an taso daga garuruwan gabas da arewa maso gabas.

Wuraren yawon buɗe ido

Wuraren ziyara da cibiyoyin addini

Babu haramin Imamzadeh a cikin garin Ilam, amma akwai wasu wuraren da ake ziyara. Sun haɗa da:

 • Masallacin Wali: Wannan wani masallaci ne daga cikin masallatan tarihi da ke garin Ilam wanda ya samo asali tun zamanin daular Qajar.
 • Maziyartar Shohadae Gomnam: Marƙadin Shahidan Gomnam a maƙabartar Beheshte Reza da ke garin Ilam, kowace shekara yana samun maziyartan ayarin Rahiyan Noor.
 • Masallacin Sahibaz Zaman da Majinginar Sayyed Musawi: Masallacin Sahibaz Zaman ɗaya ne daga cikin wurare masu tsarki na garin Ilam waɗanda ke samum maziyarta a mabambantan lokuta, hakazalika majinginar Sayyed Musawi ɗaya ne daga cikin wuraren tarihi na garin Ilam wanda shi ma yana samun maziyarta a lokuta daban-daban na shekara.
 • Mosallae Ilam. Ɗaya ne daga cikin manyan wuraren ziyara na garin Ilam, an gina shi da salo irin na masallacin Al-Aqsa.

Gidajen tarihi

Akwai gidajen tarihi guda 4 a garin Ilam:

 • Gidan tarihi na ɗabi’a
 • Gidan tarihi na Anthropology
 • Gidan tarihi na Keshavarzi
 • Gidan tarihi na Shohada

Yankunan tarihi

Ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan Gidan Wali
 • Gidan Wali. Wannan gidan yana a titin Pasdaran da ke tsakiyar garin Ilam. Gidan ya samo asali tun lokacin daular Qajar, hakazalika gidan tarihi na anthropology na cikin wannan gidan.
 • Fadar Falahati, titin Ayatollah Haidari Ilam (Shad Abad). An gina wannan fadar ne a lokacin Ma’asir kuma yanzu haka ofishin jahadin noma na Ilam na nan a cikin fadar. Ɗaya daga cikin siffofin wannan fadar shi ne ko kaɗan ba a yi amfani da kayan ƙawatawa ba a cikinta. Shi ma gidan tarihi na Keshavarzi yana nan a cikin wannan fadar.
 • Sangneveshte Ghoch Ali. Yana nan tsakanin Meidane Arghavan na garin Ilam, yana da tarihin tun zamanin daular Qajarieh.
 • Majinginar Abulfadl (AS): Wuri ne na addini a garin Ilam inda ke samun maziyarta masu yawa a kowace shekara. An keɓance ranar Litinin ɗin kowane sati a matsayin ranar ziyara ta mata a wannan wuri. Mutane sun yi imani da cewa ana karɓar addu’a sosai a wannan rana.

Wuraren gani na ɗabi’a

Garin Ilam na da wurare na ɗabi’a masu kyan gaske. Daga ciki akwai:

 • Yankin Shaƙatawa na Chegasabz. Wannan wani yanki ne daga cikin yankuna masu kyau na lardin Ilam wanda ba ya da nisa da cikin garin Ilam, kuma a ciki akwai abubuwa kamar Wonderland, Supermarket, Alacheq, Banɗaki, Restaurant, da sauransu.
 • Yankin Tang Arghavan. Wannan yankin na da yanayi na ɗabi’a mai kyau kuma mai ban mamaki. Wurin ya shahara ne da wasu itatuwan arghavan masu yawa.
 • Yankin shaƙatawa na Takht Khan. Wannan kyakkyawan wurin na nan a kilomita 20 wajen garin Ilam sannan yana da ɗabi’a mai kyau tare da wani kogi mai ƙafewa a lokacin rani, hakazalika akwai wani dutse mai rubutu na tarihi a wurin.

Karatu a Ilam

Cibiyoyin Magani

 • Asibitin Imam Khomeini
 • Asibiti da Ɗakin Gwaje-Gwaje na Kausar
 • Asibitin Shahid Mostafa Khomeini
 • Asibitin Vali Asr (AF)
 • Asibitin Ayatollah Taleghani
 • Asibitin Imam Reza
 • Asibitin Imam Husain
 • Asibitin Hazrat Rasulul Akram

Karatu a Ilam

Akwai jimillar cibiyoyin koyarwa da jami’o’i guda 19 waɗanda suka haɗa da jami’ar gwamnati 1, jami’ar likitanci 1, jami’ar Islamic Azad 1, jami’ar Payam Noor, Mu’assasa mai zaman kanta, da Ƙungiyar bincike a kan Agriculture. A lardin Ilam akwai malamai da ma’aikatan tsangayar ilimi guda 671 tare da ɗalibai 190000 masu karatu.

Jami’o’in lardin Ilam sun wallafa mujalla 2 zuwa yanzu. Masu bincike daga jami’o’i da cibiyoyin ilimi na lardin Ilam sun wallafa maƙala 11000 na ilimi zuwa yanzu, daga cikin maƙalolin akwai guda 597 na mujalla, 6118 na tarukan cikin gida, da kuma wasu a matakin ƙasa da ƙasa. Ilam University of Medical Sciences da University of Ilam su ne jami’o’i mafi muhimmanci a garin Ilam.

Karatu a Ilam

Cibiyoyin koyarwa

 • University of Ilam
 • Ilam University of Medical Sciences
 • Islamic Azad University Ilam
 • Payam Noor University of Ilam
 • Bakhtar Higher Institution Of Education
 • Ilam Comprehensive Scientific-Applied University
 • Ilam University of Science and Research

Laburarukan gari

 • Laburaren Payambar A’azam
 • Laburaren Parvin Etesami
 • Laburaren Imam Jaafar Assadiq

Masana’antu

 • Ilam Gas Refinery
 • Ilam Petrochemical
 • Iran Cement Factory

 

Related Posts
Leave a Reply