[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Karatu a Sanandaj

Karatu a Sanandaj

Loading

Lardin Kurdistan (wanda ya ƙunshi kalmomi biyu na ‘kurd’ da ‘stan’ da ma’anar “ƙasar kurdawa”) na nan a yammacin ƙasar Iran a nahiyar Zagros, garin Sanandaj shi ne cibiyar lardin Kurdistan. Manufarmu ta kawo muku rubutu mai take “Karatu a Sanandaj” shi ne sharhanta muku yanayin iska, al’adu, karatu, yawon buɗe ido, da sauransu na wannan gari.

Karatu a SanandajSanandaj

Sanandaj shi ne gari na biyu mafi yawan al’ummar kurdawa sannan kuma yana cikin garuruwa mafi kore (ɗabi’a) a ƙasar Iran kuma yana da tarihi mai tsawo. A shekarar 2019 UNESCO ta shigar da sunan wannan gari a jerin sunayen garuruwa masu fasaha a fagen waƙoƙi na duniya.
Lardin Kurdistan mai girman murabba’in kilomita 29137, yana da iyaka mai tazarar kilomita 200 da ƙasar Iraq. A rabon ƙasa da aka yi na ƙarshe a shekarar 2011, lardin Kurdistan na da ƙananan garuruwa 10 da birane 29. ƙananan garuruwan sun haɗa da: Baneh, Bijar, Saqqez, Sanandaj, Qorveh, Marivan, Divandarreh, Kamyaran, Sarvabad, da Dehgolan.
Daga arewa lardin Kurdistan na da iyaka da lardin Azerbaijan Gharbi da Zanjan, ta gabas lardin Hamadan da Zanjan, ta kudu Kermanshah, ta yamma kuma ƙasar Iraq kamar yadda muka ambata a baya.

Bayani game da Sanandaj a dunƙule
Kasantuwar cewa garin yana da yanayi mai daɗi mutane sun jima suna zama cikinsa, hakazalika duk da cewa Sanandaj birni ne, yana da salon gini na gargajiya sakamakon ayyukan gine-gine na zamanin Safawi da Qajar. Aikin ƙirgen da aka yi a shekarar 2016 ya nuna cewa akwai mutum 1603011 a lardin Kurdistan. Kurdanci shi ne yaren mutanen wurin. Mafi yawan mutanen wannan lardi musulmi ne ƴan ahalus sunnah. Lrdin Kurdistan na cikin yankin duwatsu sannan yana da yanayi mai sanyi da jiƙaƙƙiyar iska. Ana samun ruwan sama mai yawa a lokacin hunturu a wannan yanki.

Karatu a Sanandaj

Akwai cibiyoyin ilimi gami gami da jami’o’i guda 18 a kurdistan sannan akwai ɗalibai 24617 masu karatu tare da malamai 959. Bincike ya nuna cewa an wallafa maƙalolin ilimi guda 20707 waɗanda suka ƙunshi maƙalolin mujalla guda 3667 da maƙalolin taro guda 9525 a tarukan cikin gida, da kuma maƙala 3667 a matakin ƙasa da ƙasa. Daga cikin sanannun cibiyoyin ilimi da ke lardin Kurdistan akwai:
_ Kurdistan University of Medical Sciences
_ University of Kurdistan
Kuna iya ziyartar waɗannan maƙalolin domin samun ƙarin bayani Karatu a Kurdistan University of Medical Sciences da Karatu a University of Kurdistan.

Jami'o'in Sanandaj

Abubuwan more rayuwa da wuraren yawon buɗe ido

A lardin Kurdistan akwai wuraren shaƙatawa masu yawan gaske, wuri ne da ya dace da yawon buɗe ido. Kogwanni, ɗagwararrun ƙauyuka, salon waƙe na kurdawa, tsayayyun gidaje, tsofaffin tsaunuka, da gidajen sarauta na tarihi duk suna cikin wuraren buɗe ido na wannan lardi. Bayan dazuzzukan da ke arewacin Iran, akwai wasu dazuzzuka masu muhimmanci a lardin Kurdistan. Dazuzzukan na nan a kewayen garin Baneh da Marivan.
_ Masallacin Khosro Abad
_ Kogon Karafto
_ Fadar Khosrow Abad
_ Kasuwar Sanandaj
_ Gidan Salar Saeed
_ Gidan Imam Marivan
_ Fadar Daj Zivieh
_ Cocin Sanandaj
_ Hammam Shishe
_ Gidan Asif Vaziri
_ Sang Nebeshte Uraman (rubutun tangi var)
_ Pol Garan
_ Masallacin do manareh Saqqez
_ Babban masallacin Sanandaj
_ Gadar Farhad Abad
_Gidan Mashir Divan
_ Gidan Wakil
_ Idon ruwan Baba Gorgor
_ Chehel Cheshme
_ Kasuwar Biijar
_ Changiz Qal’e
_ Gidan Amjadal Ashraf Sanandaj
_ Gadar Qajor (Gadar Qashlaq)
_ Gidan wanka na Haj Saleh
_ Wurin shaƙatawa na Abdar
_ Tafkin Zarebar
_Da sauransu…

Yawon buɗe ido a Sanandaj

Cibiyoyin Magani

_ Asibitin Kausar
_ Asibitin Besat
_ Sanandaj Social Security Hospital
_ Shahid Ghazi Clinic
_Shahid Beheshti Hospital Qorveh
_ Imam Hossein (AS) Hospital
_ Asibitin Sinai
_ Asibitin Fajr
_ Asibitin Tauhid
_ Asibitin Imam Khomeini (R)
_ Asibitin Bu-Ali
_ Asibitin Shohada
_ Asibitin Qods
_ Ara Clinic
_ Hamzeh Sayyedal Shohada Clinic
_Da sauransu…

Hotal Hotal

_ Shadi Hotel
_ Jahangardi Hotel Sanandaj
_ Kurd Hotel
_ Haleh Hotel
_ Dawinco Hotel
_ Zeribar Hotel
_ Mad Hotel
_ Aryan Hotel
_ Nowruz Hotel
_ Shar Hotel
_ Zana Hotel
_ Hedayat Hotel
_ Azadi Hotel
_Da sauransu…

Ɗakunan Karatu

_ Laburaren Azandan
_ Laburaren Avihang
_ Laburaren Baharan
_ Laburaren Hosein Abad
_ Laburaren Mastureh Ardalan
_ Babban Laburaren Sanandaj
_ Laburaren Imam Reza (AS)
_ Laburaren Shahid Motahari
_ Laburaren IT
_ Laburaren Molla Borhan
_ Babban Laburaren Imam Khomeini (R)
_ Laburaren Mamusat
_ Laburaren makafi da masu raunin gani na Daneshga
_ Laburaren Khatamal Anbiya
_ Laburaren Ferdowsi
_Da sauransu…

Related Posts
Leave a Reply