تهران، میدان ولیعصر، جنب سفارت عراق، ساختمان مینو
مشهد، میدان شریعتی، نرسیده به احمد آباد ۱، طبقه بالای بانک دی

Karatu a Babolsar

Karatu a Babolsar

Loading

Garin Babolsar ɗaya ne daga cikin garuruwa masu kyau na lardin Mazandaran. A baya akan kira wannan garin da suna Mashhadsar, ana cewa tsohon sunan garin shi ne “Mashhad Sabz”. A wannan maƙala mun yi nufin bayyana muku yanayin karatu a garin Babolsar, yanayin iskar garin, yanayin rayuwa, wuraren yawon buɗe ido, al’adu da sauran abubuwan da suka shafi garin. Hadafinmu shi ne cewa ku iya yanke shawarar karatunku a Iran cikin sauƙi bayan kun karanta wannan maƙala.

Karatu a BabolsarBabolsar

Babolsar Gari ne a tsakiyar yankin duwatsun Alborz da gaɓar tekun caspian, akwai kogin Babolrud wanda ya ratsa ta cikin Babolsar inda ya raba garin biyu; gabas da yamma. Babolsar na maƙotaka da garin Fereydunkenar ta gabas, da garin Babol ta kudu. Har ila yau, daga cikin garuruwan da ke kusa da Babolsar akwai Sari da Mahmoud Abad. Garin na da tsufan shekaru 900 lokacin da garin ya fara a matsayin wani ɗan ƙauye a gefen kogin Babolrud. Ƙirgen shekarar 2016 ya nuna cewa akwai mutane 59966 a garin. A ƙiyasi,kowace shekara ana samun ruwan sama kimanin milimita 886. Garin a bushe yake a lokacin zafi, a lokacin damina kuma ana samun ruwan sama da dusar ƙanƙara. Haka kuma danshin iska na raguwa sosai a lokacin sanyi.
Mafi yawan mutanen garin suna magana ne da lahajar Mazandarani. Mutanen garin Babolsar ƴan ƙabilar Tabari ne. Daga cikin sana’o’insu akwai noma, kamun kifi, dillancin gidaje, da sauransu.
Daga cikin abubuwan tsaraba na Babolsar akwai kayan zaƙi na gargajiya, zaitun, kifi, ganyayyaki, da sauransu. Daga cikin sana’o’insu na hannu akwai sassaƙa, saƙar darduma, tukane, saƙar kaba, da sauransu.
Behnamir, Hadi Shahr, Armich Kola, Azan Abad, Esfandiyar Mahale, da Afratakhte na daga cikin ƙauyukan Babolsar.

Bayani a kan BabolsarKaratu a Babolsar

A lardin Mazandaran akwai jimillar jami’o’i da cibiyoyin koyarwa 77 ɗauke da ɗalibai 117771 da malamai 5878. Bincike ya nuna cewa an wallafa maƙalolin ilimi guda 101818 daga waɗannan cibiyoyin, ciki har da maƙalolin mujalla guda 14960 da maƙalolin taro guda 58152 a tarukan ilimi na cikin gida, da wasu maƙaloli a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Mazandaran ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in lardin Mazandaran waɗanda ke garin Babolsar. Za ku iya samun ƙarin bayani game da jami’ar a rubutunmu mai suna Karatu a Jami’ar Mazandaran.

Jami'o'in Babolsar

Nishaɗi da wuraren yawon buɗe ido

Garin Babolsar na da tarihi a ɓangaren shaƙatawa da yawon buɗe ido, nan ne babban wurin shaƙatawa da yawon buɗe ido na baƙi ƴan ƙasashen waje kafin juyin musulunci a Iran. Hakazalika a kowace shekara yana samun maziyarta daga sassa daban-daban na duniya. Garin na cikin garuruwan shaƙatawa da ake ji da su a lardin Mazandaran.
_ Gadar Mo’alaq
_ Shey Alim Waterfall
_ Ƙauyen Galesh Kola
_ Kogin Babolrud
_ Gidan zoo na Babolsar
_ Gaɓar tekun Mirud
_ Yankin shaƙatawa na Karfun
_ Madatsar Arab Khail
_ Imamzadeh Ibrahim
_ Makarantar Narges
_ Borj Sa’at
_ Meydane Mojassame
_ Aslake Saheli
_ Talab Azizak
_ Kouhi Khail
_ Ƙauyen Sar Hammam
_ Park
_ Tudun Bastani
_ Armich kala
_ SP Kala – Karim Kala
_ Sharmeh Kala
_ Da sauransu…

Yawon buɗe ido a Babolsar

Cibiyoyin magani da asibitoci

_ Asibitin Shahid Rajaei
_ Asibitin Hazrat Zainab
_ Asibitin Shafa
_ Da sauransu…

Hotal Hotal

_ Mizban Hotel
_ Shoka Hotel
_ Behesht Afra Hotel
_ Seh Kaj Hotel
_ Hotel
_ Shafaq Hotel
_ Delkadeh Hotel
_ Golfam Hotel
_ Borj Saat Hotel
_ Khez Shahr Jahangardi Hotel
_ Michka Hotel
_ Ladan Hotel
_ Da sauransu…

Laburaruka

_ Laburaren Amir Pazevari
_ Laburaren Shahr
_ Laburare da cibiyar al’adu ta Shohadae Gomnam
_ Laburaren Shahid Salehi
_ Babban Laburare da cibiyar ajiyar bayanai ta jami’ar Mazandaran
_ Laburaren Marhum Rahim Mohseni
_ Da sauransu…

Cibiyoyin Kasuwanci

_ Oxin Shopping Center
_ Europe Shopping Center
_ Persia Shopping Center
_ First Family Center
_ Bazaar Rouz
_ Royal Mall Complex
_ Iran Cotton
_ Tamasha Shopping Center
_ Babolsar Shopping Center
_ Saadi Passage
_ Daheghan Shopping Center
_ Da sauransu…

Gidajen cin abinci

_ Soseh Kebab Restaurant
_ Nah Restaurant
_ Lusso Restaurant
_ Molana Halim & Ash
_ Mizban Restaurant
_ Roza Bianko Restaurant
_ Toranj Restaurant
_ Cibo Restuarant
_ Matoo Plus Restaurant
_ Figaro Italian Restaurant
_ Baghche Restaurant
_ Mehr-o Mah Restaurant
_ Darya Kenar Traditional Restaurant
_ Agha Mahiche Restaurant
_ Da sauransu…

Related Posts
Leave a Reply