A wasu ƙasashe akwai dokoki mabambanta da akan gindayawa mutanen da ba ‘yan ƙasar ba. A ƙasar Iran ma akwai waɗannan dokokin waɗanda suka katange baƙi daga shiga wasu wuraren, zama a cikinsu, ko kuma waɗanda suka shafi karatu. A wannan rubutu za mu kawo muku bayani ne a kan garuruwa da kwasa-kwasan karatu waɗanda aka haramta ga ɗaliban waje a Iran.
Kamar yadda muka sani cewa an gindaya sharuɗa da iyakoki wajen zaɓar kwas da wurin karatu ga ɗaliban da ba Iraniyawa ba. An saka waɗannan iyakokin ne saboda wasu dalilai kamar na tsaro, tattalin arziki, al’adu, da sauransu. Misali, baƙin ɗalibai ba za su zauna a bakin iyakokin ƙasa ba ko kuma garuruwan da za su iya tare guraben aikin ‘yan ƙasa ba. Hakazalika, me yiwuwa controlling ɗinsu ya yi wahala idan suka zauna a wasu garuruwan. Tawagarmu ta shirya muku bayanai masu muhimmanci da suka shafi waɗannan haramtattun garuruwa da kwasa-kwasai.
Haramtattun kwasa-kwasai
Waɗannan su ne jerin kwasa-kwasan da ba’a ba ɗaliban waje ‘yan ƙasar Afghanistan, Iraq, da sauran ƙasashe damar karantasu a Iran ba.
Jerin haramtattun kwasa-kwasai ga ɗaliban waje:
Atomic Physics
Nuclear Physics
Molecular Physics (Plasma)
Fundamental Particle Physics
Plasma Engineering
Safety Engineering (technical inspection and protection of aircraft)
Maintenance Engineering (helicopters and airplanes)
Aerospace Engineering
Aeronautical Engineering (piloting, aircraft navigation, aircraft maintenance, helicopter piloting and flight maintenance)
Military Sciences
Aviation Electronics
Aircraft Maintenance
Airplane Communication
Air Traffic Control
Information technology (IT, Intelligence)
Satellite Technology Engineering
Computer Engineering (cyber security engineering)
Waɗannan kwasa-kwasan galibi haramcinsu ya shafi duka ƙasashe ne, ba tare da fifita wata ƙasa ba. To amma haramcin garuruwan karatu ba haka bane, na wata ƙasa kan iya bambanta da na sauran ƙasashe. Wannan ne dalilin da ya sanya kwasa-kwasan da ɗaliban waje za su iya karantawa suka bambanta a wasu wuraren, ɗaliban wasu ƙasashe ba za su iya karanta wasu kwasa-kwasan a wasu garuruwan Iran ba. Duba da cewa sanin wasu irin kwasa-kwasai da garuruwa ne aka haramta ma baƙin ɗalibai yana da matuƙar muhimmanci, a nan za mu kawo muku duka kwasa-kwasan da wannan haramcin ya shafa. A cigaban rubutun kuma za mu kawo muku garuruwan da ba’a yarda baƙin ɗalibai su yi karatu a cikinsu ba saboda ku iya zaɓen kwas ɗin da kuke so ku karanta da garin da kuke so ku zauna ba tare da wata matsala ba.
Haramtattun garuruwa
Azarbaijan ta Yamma: Idan aka cire garin Urmia, ɗaliban ƙasar Afghanistan da sauran ƙasashe ba su da izinin yin karatu a jami’o’in da suke cikin sauran garuruwan wannan lardin.
Azarbaijan ta gabas: A wannan lardin kuma, garin Tabriz ne kawai ɗaliban ƙasashen waje suke da izinin yin karatu a cikinsa.
Isfahan: A lardin Isfahan kuma, ɗaliban waje ba za su iya yin karatu a waɗannan garuruwan ba: Natanz, Faridan, Fereydunshahr, Semirom, Chadegan, Khansar, Dehaqan, Naeen, Golpayegan, Khur and Biabanak, Ardestan, da yankin Abuzeyd na garin Aran-o-Bidgol.
Ardabil : A wannan lardin, garin Ardabil ne kawai ɗaliban ƙasar Afghanistan za su iya yin karatu a ciki, su kuma ɗaliban ƙasar Iraq suna da haramcin zama ko karatu a garuruwan Parsabad, Bileh, Savar, Germi, Meshginshahr, da garin Namin.
Ilam: A wannan lardin, akwai haramcin zaman ɗaliban ƙasar Afghanistan a duka garuruwan lardin in bacin garin Ilam, su kuma ɗaliban sauran ƙasashe suna da haramcin zama a garin Mehran, Dehloran, da sauran garuruwan da suke bakin iyaka.
Alborz: Babu haramcin karatu ga ɗaliban duka ƙasashe a wannan lardin.
Tehran: Dukan ɗalibai (na kowace ƙasa) za su iya karatu a duka jami’o’in wannan lardi. Amma akwai yanki ɗaya da ba’a yarda ɗaliban Afghanistan su zauna ciki ba, shi ne yankin khojir da ke cikin shiyya ta 13 a garin Tehran.
Bushehr: Akwai haramcin karatu ga ɗaliban dukan ƙasashen waje a garuruwan Deylam da Gonaveh na wannan lardi.
Khorasan ta kudu: Akwai haramcin zaman duka ɗaliban waje a jami’o’in garuruwan iyaka na wannan lardi, garuruwan su ne; Nehbandan, Sarbisheh, Darmian, Qaen, Zirkuh, Ferdows, Sarayan, da Tabas. Ɗaliban ƙasar Afghanistan za su iya karatu a garuruwan Khosf da Birjand. Akwai haramcin zaman ɗaliban ƙasar Iraq a duka garuruwan wannan lardi in bacin garin Birjand.
Chaharmahal-o-Bakhtiari: Akwai haramcin zaman ɗaliban ƙasar Afghanistan a duka garuruwan wannan lardi in bacin garin Shahrkord.
Khorasan ta arewa: Bayan garin Bojnord, ba’a yarda ɗaliban ƙasar Iraq da Afghanistan su zauna a sauran garuruwan wannan lardin ba.
Khorasan Razavi: A wannan lardi akwai haramcin zaman ɗaliban ƙasar Afghanistan a garuruwan da ke kan iyaka, irinsu Torbate Jam, Quchan, Taybad, Khaf, Sarakhs, Kalat Naderi, da Dargaz.
Zanjan: Akwai haramcin zaman ɗaliban ƙasar Afghanistan a jami’o’in wannan lardin in bacin garin Zanjan, su kuma ɗaliban ƙasar Iraq in bacin garin Zanjan da na Khodabandeh, ba su da izinin zama a sauran garuruwan lardin.
Khuzestan: Akwai haramcin zaman ɗaliban Afghanistan a garuruwan wannan lardin in bacin garin Ahvaza da Gotvand, su kuma ɗaliban sauran ƙasashe ba’a yarda da zamansu a garuruwan Abadan, Khorramshahr,da Dashte Azadegan ba. Abin Lura: Ɗaliban da suke da iƙama za su iya zama a garin Abadan da Khorramshahr.
Sistan Baluchestan: Akwai haramcin zaman ɗaliban Afghanistan da Iraq a duka jami’o’in da ke wannan lardin (in bacin garin Zahedan), su kuma ɗaliban sauran ƙasashe ba’a yarda da zamansu ko kai-komonsu ba a garuruwan Zabol, Hermand, Zahak, da wasu sassan garuruwan Khash Iranshahr, Saravan, da Chah Bahar.
Seman: Akwai haramcin zama ko kai-komon ɗaliban waje a jami’o’in yankin Garmsar, ko shigarsu Ghasre Bahram, Cibiyar gwaje-gwaje ta Meraj, da wani yanki na garin Damghan, bin hayar Chandogh zuwa cibiyar gwaje-gwaje ta Soraj. Hakazalika akwai haramcin zaman ɗaliban Afghanistan a garin Shahrod da Damghan.
Qazvin: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a duka jami’o’in wannan lardin in bacin garin Qazvin.
Fars: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a garuruwan Firouz Abad, Farashband, Darab, Arsenjan, Fasa, Mohr, Rostam, Khonj, da kuma Neyriz.
Kurdistan: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a jami’o’in wannan lardin (in bacin na garin Sanandaj), ɗaliban sauran ƙasashe kuma ba’a yarda su zauna a wani sashe na garin Saqqez ba da garuruwan Baneh, Marivan, da sauran garuruwan da ke kan iyaka.
Qom: Babu haramcin karatun ɗaliban waje a duka jami’o’in wannan lardi.
Kermanshah: In bacin garin Kermanshah, ba’a yarda ɗaliban ƙasar Afghanistan su yi karatu a sauran garuruwan wannan lardi ba. Su kuma ɗaliban sauran ƙasashe za su iya karatu a ko ina in bacin garuruwan da ke kan iyaka.
Kerman: Akwai haramcin karatun ɗaliban ƙasar Afghanistan a jami’o’in garuruwan Anbarabad, Baft, Manujan, Qalehganj, Bam, Fahraj, Rodbar, Faryab, Narmashir, Kahnuj, Jiroft, Anar, da kuma garin Rigan. Su kuma ɗaliban Iraq ba’a yarda su zauna a garuruwan wannan lardin ba in bacin garin Kerman.
Golestan: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a duka jami’o’in wannan lardin (bacin garin Gorgan da Gonbad).
Kohgiluyeh-o Boyer-Ahmad: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a duka jami’o’in wannan lardin bacin garin Yasuj.
Gilan: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a duka jami’o’in wannan lardi idan aka cire garin Rasht.
Lorestan: Ba’a yarda ɗaliban Afghanistan su yi karatu a duka jami’o’in wannan lardi ba, bacin na garin Khorram Abad.
Mazandaran: Ba’a yarda ɗaliban Afghanistan su yi karatu a jami’o’in wannan lardin ba, in bacin garin Sari.
Markazi: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a garuruwan Ashtiyan, Tafresh, Farahan, Farmahin, Khomein, Shazand, Mahallat, Zarandieh, Komijan, da Khandab.
Hamedan: Akwai haramcin karatun ɗaliban Afghanistan a garuruwan wannan lardi, in bacin garin Hamedan.
Hormozgan: Akwai haramcin karatun ɗaliban waje a duka garuruwan wannan lardi bayan garin Abumusa da garin Jask.
Babban dalilin wannan haramcin da ƙungiyar sanjesh ta sanar shi ne samarwa ɗaliban waje karatu mafi inganci, misali kowa zai iya karatu a Iran University of Science and Technology, Sharif University of Technology, Ferdowsi University of Mashhad, Mashhad University of Medical Science, da sauarnsu.
Shafin ma’aikatar kula da harkokin waje, domin bayanan da suka shafi ayyukan jakadanci mfa.gov.ir/portal/viewservices
Tambayoyi a kan haramtattun kwasa-kwasai da garuruwa a ƙasar Iran
- Wasu irin kwasa-kwasai ne aka haramta wa ɗaliban ƙasashen waje karantawa a Iran?
Ba’a karɓar ɗaliban waje a kwasa-kwasan da ke iya haifar da wajabcin ɗaukar aiki ga gwamnatin ƙasar Iran. Mun ambaci haramtattun kwasa-kwasai da yankuna ga ɗaliban waje a cikin rubutunmu. - Wasu yankuna ne aka haramta ma ɗaliban waje su zauna a ciki?
Akwai jadawali da cikakken bayani a kan waɗannan yankuna a cikin rubutunmu. - Menene makomar waɗanda ba ‘yan ƙasar Iran ba amma suna da katin shaidar zama na musamman?
Babu haramcin karatu ko kai-komo a waɗannan yankuna da muka ambata ga waɗanda ba Iraniyawa ba ne su amma kuma suna da wannan littafin na musamman wanda ‘yansandan immigration suka basu