Watakila tambaya ta bijiro muku cewa me da me ake buƙata domin karatu a University of Tehran. Tambayoyi kamar: Nawa ne kuɗin makaranta, kwasa-kwasan karatu, matakan karatu, kuɗin hostel da kuma yanayin tsadar rayuwa a Tehran. A wannan rubutun, muna son mu amsa duka waɗannan tambayoyin naku saboda ku sami damar yanke shawara mafi kyau game da ci gaban karatunku.
Gabatarwa
Ana kallon Jami’ar Tehran (University of Tehran) a matsayin jami’a mafi kyau kuma mafi shahara a Iran.
Prof. Mahmoud Hassabi shi ne ya assasa wannan jami’ar a shekarar 1934. A halin yanzu, University of Tehran tana da haraba 25 da makarantu da dama.
Wannan jami’ar na da kimanin hostel guda 15, kwasa-kwasan BSc guga 111, 177 na M.Sc, da kuma kwas 156 a matakin PhD. Har ila yau, University of Tehran na da kusan malamai 1500 da ɗalibai 50,000.
Jami’ar tana randabawul na Inqilab a cikin garin Tehran, kuma za’a iya amfani da motar BRT ko jirgin ƙasa na Metro domin zirga-zirga cikin sauƙi. Ta wani ɓangaren kuma, mafi yawan makarantun wannan jami’ar suna cikin unguwar Inqilab, wanda nan ma za’a iya amfani da taxi.
Maƙalolin da suka wallafa
Adadin Maƙalolin ilimi na cikin gida: Maƙala 77574
Adadin maƙalolin ƙasa da ƙasa: Maƙala 72129
Mawallafiyar mujalla 114
Martabar University of Tehran
University of Tehran ita ce ta ɗaya a jami’o’in Iran; Wannan jami’a ita ke da matsayi na farko a kaf jami’o’in Iran sannan kuma a shekarar 2020, ta samu matsayi na 301 zuwa na 400 a tsarin Shanghai. Hakazalika tana da matsayi na 801 zuwa na 1000 a tsarin Times.
Cibiyoyin Bincike
• Petroleum Engineering Institution
• Central Eurasian Studies Center
• Applied Management Research Center
• Nano Science and Technology Research Center
• International Desert Research Center
• Biochemistry and Biophysics Research Center
• Kohin Soil and Water Protection Research Center
• International Cooperation Center
• North American and European Studies Institution
• Women’s Studies and Research Center
• Advanced Characterization Research Center
• Public Policy Studies Center
• Energy Law Studies Center
Ƙungiyoyin Bincike
• Culture and Art Research Institution
• Psychology and Educational Sciences Institution
• Applied Research of Iranian Culture Institution
• Research in Energy Management and Planning Institution
• Economic Development and Research Institution
• Comparative Law Institution
• Dehkhoda Dictionary Institution and International Center for Persian Language Education
• Public Law Institution
• Criminology Research Institution
• National Language Research Institution
• History of Science Research Institution
• Vehicle, Fuel and Environment Research Institution
• Water and Soil Environmental Research Institution
• Water Institution
• Geography Institution
• Archaeology Institution
• Geophysics Institution
• Social Studies and Research Institution
• The scientific Center of Technical Faculties
• Upgrade of Heavy and Rresidual Oil
• Surface Engineering and Corrosion Protection in Industries
• Materials in Low Energy Technologies
• Making Nano Silicon Devices
• Pharmaceutical Process Engineering
• Applied Electromagnetic Systems
• Photogrammetry Engineering in Dealing with Natural Disasters
Jerin Makarantu
Jami’ar Tehran tana da makarantu 25 da haraba 9. Tabbas, ku sani cewa haraba ba tana nufin cibiyoyin masu zaman kansu bane. Haraba a wannan jami’ar tana nufin jimillar wani adadi na makarantu a cikin wuri ɗaya. Ga makarantu da harabobin Jami’ar Tehran kamar haka:
Harabar Makarantun Fasaha
Gabatar da University of Tehran bai taƙaitu a iya karatu da ayyukan kimiyya ba kawai. Masu neman shiga zasu iya karatun kwas ɗin da suke muradi a cikin makarantun Jami’ar Tehran. Ɗaya daga cikin harabobin Jami’ar Tehran ita ce harabar Makarantar Fasaha . Ɗalibai zasu iya zaɓar kwas ɗaya ya dace da su daga cikin kwasa-kwasai 215 da ake yi a wannan makarantar. Harabar Makarantar Fasaha ta jami’ar Tehran tana da sama da malamai 750 da ɗalibai 5000 da suke karatu a wannan makarnta. Akwai kimanin ɗalibai 45000 da suka kammala karatunsu a Makarantar Fasaha ta Jami’ar Tehran. Makarantar Fasaha tana da kwalejoji kamar haka:
• College of Electrical & Computer Engineering
• College of Mechanical Engineering
• College of Civil Engineering
• College of Metallurgy & Materials Engineering
• College of Caspian
• College of Engineering Sciences
• College of Industrial Engineering
• College of Chemistry
• College of Mining Engineering
• College of Surveying and Geomatics Engineering
• College of Fouman Engineering
• College of Environment
Harabar Aburaihan
Harabar Aburaihan da ke cikin Jami’ar Tehran ita ma tana ɗauke da makarantu da dama. Harabar Aburaihan tana ɗauke da kwalejoji kamar haka:
• Agro-Technology Department
• Food Science Technology Department
• Food Science Technology Department
• Animal and Poultry Sciences Department
• Irrigation and Drainage department
• Agronomy and Plant Breeding Sciences Department
• Entomology and Plant Pathology Department
Harabobin yanki
Jami’ar Tehran na ɗaya daga cikin jami’o’i masu yawan ɗaliban ƙasar waje. Waɗannan ɗalibai a cikin harabobin yanki na jami’ar suke karatu. Harabobin yanki na Jami’ar Tehran sun haɗa da:
• Harabar Alborz
• Aras International Campus
• Kish International Campus
Makarantar Veterinary Medicine
Ɗaya daga cikin makarantun Jami’ar Tehran ita ce Makarantar Veterinary Medicine . Makarantar Veterinary Medicine ta ƙunshi sassa daban-daban da kuma ɗalibai da yawa masu karatu a wannan makarantar. Sassan Makarantar Veterinary Medicine sun haɗa da:
• Department of Animal and Poultry Health and Nutrition
• Department of Basic Sciences
• Department of Internal Medicine
• Department of Food hygiene and Quality Control
• Department of Microbiology and Immunology
• Department of Surgery & Radiology
Makarantun Kimiyya
Wata harabar Jami’ar Tehran kuma ita ce Harabar Kimiyya wacce take ɗauke da kwalejoji kamar haka:
• College of Mathematics
• College of Statistics and Computer Science
• College of Geology
• College of Biology
• College of Chemistry
• College of Physics
• Department of Biotechnology
• Colleges of Fine Arts
Kwalejin Fine Arts na jami’ar ya shafi dukan kwasa-kwasan karatu da suke da alaƙa da art. Kwalejin Fine Arts tana karɓar ɗalibai a sassan karatu mabambanta kamar; Architecture, Music, Graphics, Theater, da sauransu. Kwalejojin Fine Arts sun haɗa da:
• College of Urban Planning
• College of Architecture
• College of Performing Arts and Music
• College of Visual Arts
• College of Industrial Design
• Faculty of Humanities
Harabar Humanities ta ƙunshi makarantu kamar haka:
• Faculty of Foreign Languages and Literatures
• Faculty of Literature and Humanities
• Faculty of Theology and Islamic Studies
• Faculty of Law and Political Science
• Faculty of World Studies
• Faculty of Islamic Thoughts
Harabar Agriculture & Natural Resources
Harabar Noma da Albarkatun Ƙasa ta jami’ar Tehran tana cikin garin Karaj. Kwalejojinta sun haɗa da:
Kwalejin Farabi
Ɗaya daga cikin harabobin Jami’ar Tehran da zamu ambata a gabatar muku da wannan jami’a, ita ce Harabar Farabi . Wannan harabar tana cikin garin Qom kuma ta ƙunshi makarantu kamar haka:
• College of Theology
• College of Law
• Faculty of Engineering
• College of Management and Accounting
Sashen Social & Behavioral Sciences
Sashen Social & Behavioral Sciences na ɗauke da makarantu kamar haka:
• Faculty of Economics
• Faculty of Physical Education and Sport Sciences
• Faculty of Geography
• Faculty of Psychology and Education
• Faculty of Social & Behavioral Sciences
• Faculty of Entrepreneurship
• Faculty of Management
Kuɗin makaranta da sauran buƙatu
Idan kuna tunanin yin karatu a University of Tehran, dole kuyi tanadi akan kuɗin kashewa su ma, kasantuwar cewa garin Tehran ya ɗara sauran garuruwan Iran tsadar rayuwa saboda shi ne babban birnin tarayya. A bayani mai zuwa, mun kawo muku bayani akan yanayin tsadar rayuwa a garin Tehran.
Ƙiyasin farashin rayuwa a kowane wata: Dala 1013
Ƙiyasin albashin kowane mutum ɗaya: Dala 380
Ƙiyasin kuɗin haya (hayar gida mai ɗakin kwana 1 ko 3 a tsakiyar gari da sauran sassan garin): Dala 592
Ƙiyasin kuɗin haya akan kowane murabba’in mita ɗaya a tsakiyar gari: Dala 2247.09
رشته تحصیلی | مقطع مورد نظر | طول مدت دوره تحصیل | قیمت شهریه(سالیانه) |
---|---|---|---|
کلیه رشته ها | کارشناسی | 4 سال | 2300$ |
کارشناسی ارشد | 2 سال | 3400$ | |
دکتری | 3 الی 4 سال | 4300$ |
Jerin kwasa-kwasan da ake yi
A cigaban wannan rubutun, mun kawo mulu list na dukkan kwasa-kwasan da ake yi a Jami’ar Tehran domin ku samu damar zaɓar irin kwas ɗin da kuke muradi.
Adireshin Jami’ar
Adireshi: Babbar Cibiyar University of Tehran Titin Inqilab, titin 16 Azar, Randabawul na Inqilab, Tehran.
Tambayoyin da aka fi yi game da rubutun gabatarda University of Tehran.
- Shin ana karɓar ɗaliban ƙasar Iraƙi a matakin PhD a wanna jami’ar?
Eh ana karɓa, amma a wasu kwasa-kwasan tsarin karatu kawai ake karɓa (ba research ba).
[neshan-map id=”18″]