Shahrood University of Technology ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati waɗanda ke cikin garin Shahrood ta lardin Semnan. Garin Shahrood yana kan hanyar Tehran zuwa Mashhad. Nisan garin Shahrood daga Tehran kilomita 412 ne, daga Mashhad kuma kilomita 511. Da yawan ɗalibai na da burin karatu a wannan jami’a ta Shahrood, ku kasance tare da mu don samun bayanan da suka dace game da jami’ar.
Gabatarwa
Ita dai wannan jami’a ta fasaha ta Shahrood (Shahrood University of Technology) ɗaya ce daga cikin makarantun gwamnati a ƙasar Iran wadda ta fara aiki a shekarar 1973 a matsayin babbar kwalejin ma’adanai. Ta taka rawa sosai a lokacin da tana ƙarƙashin ma’aikatar ma’adanai da masana’antu a shekarar 1975 kenan, jim kaɗan bayan nan, a shekarar 1982 aka mayar da ragamar tafiyar da kwalejin zuwa hannun majalisar al’adu da karatun gaba da sakandare.
Bayan fara yin kwasa-kwasan Mining Engineering a shekarar 1987 da kuma difilomar Electrical Engineering da Civil Engineering, kwalejin ta koma “Shahrood Higher Education Complex”, daga bisani aka maida ita “Shahrood University” a shekarar 1993, daga ƙarshe kuma aka maida ita “Shahrood University of Technology” a shekarar 2002.
A kowace shekara jami’ar na amfani da jarabawar shiga ko record ɗin karatu wajen ɗaukar sabbin ɗalibai. Jami’ar fasaha ta Isfahan ita ce jami’ar farko a kaf lardin Semnan da ta karɓi ɗalibai sama da 11,700 kuma tana da ma’aikatan tsangayar ilimi 340. A wannan jami’ar ana yin kwas 40 a matakin PhD, kwas 76 a matsers, da kwas 30 a matakin digiri, sannan tana da kwaleji 14. Ba shakka tana daga cikin jami’o’in fasaha mafi inganci na ƙasar Iran.
Martabar Jami’a
A sabon sakamakon da tsarin ranking na TIMES ya fitar, jami’ar fasaha ta Shahrood ta samu matsayi na 34 a jami’o’in ƙasar Iran, da matsayi na 301 – 350 a jami’o’in yankin Asia. Hakanan kuma jami’ar ta samu shiga jerin fitattun jami’o’i 400 masu tasowa na duniya.
Har ila yau, tsarin TIMES ɗin ya tantance wasu jami’o’i na duniya bisa la’akari da ayyukansu na ilimi a shekarar 2022 inda wannan jami’a ta fasaha ta Shahrood tare da wasu jami’o’i 9 daga ƙasar Iran suka samu shiga rukuni na 601 – 800 a fannin Engineering Sciences, sannan jami’ar ta zo matsayi na 5 a tsakanin jami’o’in Iran.
Kuɗin Makarantar Shahrood University of Technology
Grade | Annual tuition |
---|---|
Bacholar | 450$ |
Masters | 900$ |
PhD | 1,375$ |
Makarantu
- Faculty of Electrical Engineering
- Faculty of Computer Engineering and Information Technology
- Faculty of Mechanical and Mechatronic Engineering
- Faculty of Industrial Engineering and Management
- Faculty of Mining, Geophysics and Petroleum Engineering
- Faculty of Chemical and Materials Engineering
- Faculty of Architectural Engineering and Urban Planning
- Faculty of Agricultural Engineering
- School of Chemistry
- Faculty of Physics
- Faculty of Mathematics
- Faculty of Earth Sciences
- School of Physical Education and Sports Sciences
Kwasa-Kwasai
- Electronic Engineering
- Information Technology
- Aerospace Structures
- Civil Engineering
- Mining Exploration Engineering
- Industrial Metallurgy
- Architectural Engineering
- Food Science and Industry
- Nanophysics
- Pure Mathematics
- Geology
- Physical Activity and Wellness
- Petrology
- Engineering Physics – Plasma
- Physical Chemistry
- Da sauransu
Ɗakunan gwaje-gwaje da wuraren bita
- Thermodynamics Laboratory
- Fluid Mechanics Laboratory
- Dynamics and Vibrations Laboratory
- Strength of Materials Laboratory
- Automechanic Workshop
- Machine Tool Workshop
- Welding and sheet Metal Workshop
- Detection and Tracking Laboratory
- Laboratory for Determining the Mechanical Properties of Materials
- Wind Tunnel Laboratory
- Laboratory of Metallography and Microstructure of Materials
- Laboratory of heat Treatment of Metals
- Freezing and Casting Laboratory
- Laboratory of Mechanical Properties of Materials
- Advanced Ceramic Laboratory
- Operation Laboratory of Chemical Engineering Unit
- Chemical Engineering Heat Transfer Laboratory
- Process Control Laboratory in Chemical Engineering
Wuraren bincike
- Research Institute of Automation and Artificial Intelligence
- Water Resources Engineering Research Institute
- Buoyancy Propulsion Research Center
- Biotechnology Research Group
- Student Research Institute
Wuraren kwanan ɗalibai
Jami’ar fasaha ta Shahrood tana da hostel ɗin ɗalibai guda 6 na kanta, da wasu guda 4 masu zaman kansu. Rukunin hostel na ɗalibai maza wanda ke cikin babbar harabar jami’ar yana da block guda 5, akwai wasu block 3 a harabar kwalejin Engineering and Technology masu suna kamar haka; Basirat, Velayat, da Hedayat. Sai kuma block ɗaya na ɗaliban postgraduate, akwai kuma hostel ɗin masu research shi kuma yana da block 4 a Shahrak Daneshga.
Har ila yau, jami’ar ta kama hayar hostel mai suna Ahmadiyan mai block biyu domin ɗalibanta maza, da wani mai suna Mir Abutalib shi ma mai block biyu na ɗalibai mata.
Yanzu haka jami’ar na aikin gina hostel na ɗalibai masu iyali.
Abubuwan More Rayuwa
Kamar dai sauran jami’o’i, ita ma wannan jami’ar ta yi ma ɗalibanta tanadin abubuwan walwala da jin daɗin rayuwa na azo a gani. Saboda yanayin kwasa-kwasan da ake yi a cikinta na engineering, tana da laboratories da sauran abubuwan da ake buƙata domin inganta karatu. Duka abubuwan da ake buƙata na kayan aiki ko walwala na jami’ar za ku samu masu inganci ne. Abubuwa kamar:
- Sashen Engineering and New Technologies
- Shagon sayayya
- Self (sabis ɗin abinci)
- Laburare
- Computer Center
- Rufaffen filin wasa
- Filin wasa
- Koren fili
- Wuraren kwana
Yanayin Wuri
Jami’ar fasaha ta Shahrood na nan a unguwar Barq ta garin Shahrood, a titin Daneshga. A kusa da jami’ar akwai wurare kamar; masaukin jami’an tsaro, shagon kayan marmari na Bu-Ali, gidan biredi na Sangak, tashar mota ta Shahrood, da asibitin Khatamul Anbiya.
Adireshi: Shahrood, Meidane Hafte Tir, Shahrood University of Technology
Shafin jami’a: https://shahroodut.ac.ir