Lardin Chahar Mahal-o Bakhtiyari, mai tsayin kwatankwacin mita 2,153 wuri ne mai yawan tsaunuka. Shahrekord University of Medical Sciences wato jami’ar karatun likitanci ta garin Shahrekord, jami’ar gwamnati ce da ke garin Shahrekord na lardin Chahar Mahal-o Bakhtiyari; Jami’ar ta fara aiki ne a shekarar 1986. Ku kasance tare da mu domin samun bayani a kan yanayin karatu a wannan makaranta.
Gabatarwa
Shahrekord University of Medical Sciences ta fara aikinta ne a shekarar 1986 tare da karɓar ɗalibai 260 a kwas 3 da kuma matakan karatu 2, a ƙarƙashin makarantu 2. A halin yanzu kuma akwai kusan ɗalibai 1957 da ke karatu a wannan jami’a, a kwas 19 mabambanta, a matakan karatu 7 na; clinical specialized doctorate, PhD doctorate, professional doctorate, master’s degree, continuous bachelor’s degree, non-continuous bachelor’s degree, da associate degree. Jami’ar na da makarantu 6; Shahrekord Faculty of Medicine, School of Paramedicine, School of New Technologies, School of Health, Nursing and Midwifery, da Borujen School of Medical Sciences.
Daga cikin kayan aikin wannan jami’a akwai azuzuwan karatu waɗanda girmansu a jumlace zai kai murabba’in mita 30,000, kayan aiki na zamani, tallafin karatu da bincike, cibiyoyin bincike guda 4, asibitin koyarwa 2, laburare 2 na musamman ɗauke da sabbin litattafan kimiyya, da kuma ɗakin kwamfuta da intanet don amfanin malamai da ɗalibai.
A halin yanzu akwai kimanin ɗalibai 2385, da malamai 244 a wannan jami’ar. Bayanai sun gwada cewa zuwa yanzu an wallafa maƙalar ilimi guda 1764 a wannan cibiyar, a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar karatun likitanci ta Shahrekord ta mallaki lambar yabo sannan kuma ta wallafa mujalla 5 na musamman. Har ila yau jami’ar ta shirya taro 1 zuwa yanzu. A shekarar 2023, masu bincike na wannan jami’ar sun wallafa akasarin maƙalolinsu da kalmomin “STRESS” da “ART THERAPY” a matsayin muhimman kalmomin maƙala.
Martabar Jami’a
A sabon bayanin sakamakon da tsarin ranking na TIMES ya fitar a shekarar 2024, jami’ar karatun likitanci ta Shahrekord a karon farko ta yi nasarar shiga jerin jami’o’in duniya da suke matsayi na 800 – 1000.
Kuɗin karatu a Shahrekord University of Medical Sciences
Level | Duration | Fee(per year) |
---|---|---|
Bachelor | 4 years | 3,000$ |
Master | 2 years | 3,500$ |
M.D | 7 years | 4,000$ |
Subspecialty | 2 years | 4000-5000$ |
Fellowship | 1-1.5 years | 3,500$ |
Short-Course | up to 1 years | 3,500$ |
Makarantu
Shahrekord School of Medicine
Makarantar likitanci (School of Medicine) ta garin Shahrekord ta fara aiki ne daga shekarar 1987 a matsayin kwaleji ta farko ta wannan jami’a. A halin yanzu makarantar na karbar ɗaliban likitanci ne a duka zanguna biyu na karatu a kowace shekara. Wannan kwalejin yana da ma’aikatan koyarwa a sashen Basic Science da Clinical Science, sashen tafiyarwa da hada-hadar kuɗi, da sashen bincike. A wannan kwalejin akwai daura biyar na horarwa a kwas biyar kamar haka; Internal Medicine, surgery, (4) children, anesthesia, da women. Akwai kuma daurar General Surgeon a kwas ɗin medicine, daurar masters a kwas ɗin parasitology, bacteriology, human genetics, da kuma Immunology.
Dental College
An buɗe Kwalejin dental ta garin Shahrekord ne a shekarar 2014, inda ta fara aiki a farkon shekarar 2015 tare da karɓar ɗalibai 20 a fannin Professional Doctor of Dentistry.
School of Health
Wannan kwalejin tana da sassa (departments) uku na koyarwa kamar haka: Educational Department of Epidemiology and Biostatistics, Educational Department of Public Health, da kuma Educational Department of Environmental Health Engineering. Kwalejin ya yaye ɗalibai 1,699 zuwa ƙarshen zangon karatu na biyu na shekarar 2012/2013.
School of Nursing and Midwifery
Wannan makarantar kuwa, tana da kwasa-kwasai kamar haka; BSc Nursing (continous and non-continous), BSc Midwifery, Associate Degree in Midwifery, da kuma BSc Surgery Room.
Borojan Faculty of Medical Sciences
Wannan kwalejin yana da kwasa-kwasai kamar haka; BSc Nursing (continous), Emergency Medicine (associate & BSc), da kuma BSc Surgery Room. Kwalejin ya fara aiki da sunan School of Nursing ne a garin Borojan, a shekarar 1992 kafin a mayar da shi Faculty of Medical Sciences a shekarar 2022.
School of Paramedicine
A wannan kwalejin, ana gabatar da karatuttukan digiri a kwasa-kwasai kamar haka; Laboratory Sciences, Radiology, da Anesthesiology.
Kwasa-Kwasai
- Educational Department of Epidemiology and Biostatistics
- Educational Department of Public Health
- Educational Department of Environmental Health Engineering
- Parasitology
- Biochemistry
- General Medicine
- Human Genetics
- Descriptive Sciences
- Physiology and Pharmacology
- Education
- Bacteriology
- Immunology
- Clinical Sciences
- Children
- Nerves
- Orthopedics
- Urology
- Anesthesiology
- Surgery
- Eye
- Internal
- Radiology
- Psychiatry
- Women
- Emergency Medicine and Infectious Poisoning
- Heart
- ENT
- Surgery Room
- Adult and Elderly Nursing
- Nursing principles and skills
- Children’s Nursing
- Community Health and Psychiatric Nursing
- Midwifery
- Pregnancy Health
- Nursing and Surgery Room
- Medical Emergency
- Department of Medical Physics and Radiology
- Department of Laboratory Science
- Department of Anesthesia
- Department of General Studies
- Children
- Orthodontics
- Prosthesis
- Diagnosis (oral diseases)
- Oral and Maxillofacial Surgery
- Periodontics (gum surgery)
- Radiology
- Endodontics
- Recovery
- Oral pathology
- Jaw and Face
- Medical Biotechnology
- Molecular Medicine
- Tissue Engineering
Cibiyoyin Bincike
- Community Oriented Midwifery Nursing Research Center
- Research Center for Modeling in Health
- Cancer Research Center
- Aliqati Research Institute of Social Factors Affecting Health
- Basic Health Education Center
- Basic Health Sciences Research Center
- Rear Research Institute of Clinical Biochemistry
- Cell and Molecular Research Center
- Medicinal Plants Research Center
- Comprehensive Research Laboratory
Asibitoci
- Asibitin Ayatollah Kashani, Shahrekord
- Sashen bunƙasa bincike a kan jinya na asibitin Kashani
- Asibitin Hajar (AS), Shahrekord
- Sashen bunƙasa bincike a kan jinya na asibitin Hajar
- Asibitin Vali Asr (ATF), Borojan
- Asibitin Sayyedu Shuhada (AS), Farsan
- Asibitin Sina Jonghan
- Asibitin Shohadae Lardgan
- Asibitin Imam Reza (AS), Ardal
- Asibitin Imam Jawad (AS), Naghan
- Asibitin Shahid Arjomand Malikhalifa
- Asibitin Imam Sajjad (AS), Kohrang
Ababen More Rayuwa
- Wannan jami’ar na ɗaya daga cikin makarantun gwamnati waɗanda ke ba ma baƙin ɗalibansu wurin kwana (hostel).
- Jami’ar na da da zaurukan wasanni a fannoni daban-daban, ɗalibai masu sha’awar amfani da waɗannan wuraren na wasanni za su iya bincika hanyoyin da ake bi don amfani da shi.
- Har ila yau, jami’ar na da laburare cike da kayan aiki wanda ɗalibai za su iya amfani da su a lokacin buƙata.
- Sashen kula da walwalar ɗalibai na wannan jami’a kan bada bashin ɗalibai ga ɗaliban da ke buƙata.
- Lazim ne ɗalibai su yi amfani da sabis ɗin atomasiyon don karɓar abincin makaranta.
Yanayin Wuri
Hedikwatar jami’ar karatun likitanci ta Shahrekord tana nan a unguwar Shari’ati ta garin Shahrekord, a titin Kashani, titin Shanzdahom. Ta fuskar yanayin muhalli kuma, jami’ar na kusa da wurare kamar Parsiyan Hotel, Gidan mai na 17 Shahrivar, Idon ruwa na Kohrang, Idon ruwa na Dimeh, da asibitin Ayatollah Kashani.
Adireshi:
Shahrekord, Shari’ati, Titin Kashani, Khiyaban Shanzdahom