Qazvin gari ne mai kyau sosai, ɗaya ne daga cikin manyan garuruwan Iran masu jan hankali wanda ya zama wurin zuwan masu yawon buɗe ido na ciki da na wajen Iran a lokuta daban-daban. Jami’ar karatun likitanci ta Qazvin (Qazvin University of Medical Sciences) ita ce babbar jami’a a wannan gari na Qazvin.
Gabatarwa
A duk faɗin Iran, manyan jami’o’in karatun likitanci sun duƙufa wurin horar da ma’aikata masu himma da ilimi a fannonin likitanci da na jinya. Ɗaya daga cikin waɗannan jami’o’in likitanci na Iran ita ce Qazvin University of Medical Sciences wadda aka assasa a shekarar 2004. A farko, an aza tubalin ginin jami’ar ne tare da ƙoƙari da gudummawar al’umma da zaɓaɓɓun shugabannin jami’ar, inda ainihin ayyukanta (na koyarwa) suka fara a shekarar 2005 ta hanyar ɗaukar dalibai 75.
Wannan jami’a tana ƙarƙashin kulawar hukumar kiwon lafiya da karatun likitanci ta Iran kuma a kowace shekara tana ɗaukar ɗalibai a fannoni daban-daban na likitanci, pharmacy, nursing, da sauransu a matakan digiri, mastas, da PhD bayan yi musu jarabawa. Jami’ar a halin yanzu tana aiki da asibitocin koyarwa guda 9 Sannan tana da kimanin ɗalibai 2800 da malamai 295.
Bayanai sun nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi 1274 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar ta wallafa mujalla 1 ta musamman, kuma ta shirya taruka 4 zuwa yanzu. Har ila yau, jami’ar ta wallafa maƙala 3063 a matakin ƙasa da ƙasa.
Martabar Jami’a
Tsarin ranking na Times ɗaya ne daga cikin fitattu kuma amintattun tsarukan ranking na duniya. Jami’ar likitanci ta Qazvin ta yi nasarar samun matsayi na 401-500 a ranking ɗin shekarar 2023.
Makarantu
_ School of Medicine
_ School of Dentistry
_ School of Paramedicine
_ School of Health
_ School of Nursing and Midwifery
Wurare da Cibiyoyin Bincike
Department of Health Technology Development
_Medical Microbiology Research Center
_ Health Products Safety Research Center
_ Dental Caries Prevention Research Center
_ Diseases and Health Consequences Registration Unit
_ Comprehensive Research Laboratory of the University
_ Research Development Units
_ Cohort Center of University Employees
_ Laboratory Animal Maintenance and Reproduction Center
_ Unit of International Scientific Interactions with Researchers
_ Student Research Committee
_ Research Institute for the Prevention of Non-Communicable Diseases Wanda ya ƙunshi waɗannan cibiyoyin:
_ Research Center for Social Factors Affecting Health
_ Child Development Research Center
_ Metabolic Diseases Research Center
_ Cell and Molecular Research Center
Kuɗin Makarantar Qazvin University of Medical Sciences
Cibiyoyin horarwa na likitanci
_ Bu Ali Sina Educational and Treatment Centers
_ Quds Educational and Medical Center
_ Kowsar Educational and Therapeutic Center
_ Shahid Rajaei Educational and Treatment Center
_ Educational and Therapeutic Center on 22 Bahman
_ Education and Treatment Center of the Province
_ Amir al-Mominin Hospital
_ Shafa Hospital
_ Rahimian Hospital
_ Shohada Hospital
_ Specialized and Sub-specialized Clinic of the University
Sansanonin kiwon lafiya
_ Sansanin kiwon lafiya na ABIK
_ Sansanin kiwon lafiya na Auj
_ Sansanin kiwon lafiya na Alborz
_ Sansanin kiwon lafiya na Bolandian
_ Sansanin kiwon lafiya na Boyin Zahra
_ Sansanin kiwon lafiya na Takistan
Sassan koyarwa (Departments)
School of Medicine:
Basic Sciences Departments:
_ Department of Biochemistry and Genetics
_ Department of Anatomical Sciences
_ Department of Physiology and Medical Physics
_ Department of Microbiology and Immunology
_ Pathology Department
_ Department of Islamic Studies
Clinical Departments:
_ Department of Gynecology and Obstetrics
_ Heart Department
_ Department of Psychiatry
_ Anesthesia Department
_ Children’s Department
_ Internal Department
_ Department of Surgery
_ Department of Infections
_ Department of Social and Family Medicine
_ Medical ethics Department
Dental College:
Departments of General Studies:
_ Diagnosis of Oral and Dental Diseases
_ Oral and Dental Radiology
_ Pathology and Oral Pathology
_ General Endodontics
_ General Periodontics
_ Orthodontic
_ Dental Prostheses
_ Repair and Beauty
_ Pediatric Dentistry
_ Oral, Jaw and Facial Surgery
Specialized Training Departments:
_ Specialized Endodontics
_ Specialized Periodontics
_ Specialized Orthodontics
_ Specialized Prosthesis
Sauran Sassa:
_ Phantom Section
_ Autoclave Unit
School of Paramedicine:
New Medical Technologies Departments:
_ Master of Medical Biotechnology
_Master’s Degree in Medical Nanotechnology
Surgery Room:
_ Continuous Bachelor of Surgery Room
Anesthesiology:
_ Continuous Bachelor of Anesthesiology
Laboratory Sciences:
_ Continuous Bachelor of Laboratory Sciences
Medical Emergency:
_ Bachelor’s Degree in Emergency Medicine
_ Bachelor’s Degree in Emergency Medicine
School of Health:
_ Public Health and Health Education (Specialized Research Doctorate, Master’s Degree, Dachelor’s Degree)
_ Management of Healthcare Services (master’s degree, bachelor’s degree)
_ Environmental Health Engineering (Master’s Degree, Bachelor’s Degree)
_ Occupational Health Engineering (Master’s Degree, Bachelor’s Degree)
_ Food Hygiene and Safety (Bachelor)
_ Health Sciences in Nutrition (Master’s Degree)
_ Epidemiology and Biostatistics (duka matakai)
School of Nursing and Midwifery
Department of Special Care and Emergency Nursing :
_ Master of Special Care
_ Master’s Degree in Nursing and Emergency
_ Bachelor of Nursing
Psychiatric and Geriatric Nursing Department:
_ Master’s Degree in Geriatric Nursing
_Master’s Degree in Psychiatric Nursing
Midwifery Department:
_ Master’s Degree in Counseling in Midwifery
_ Bachelor of Midwifery
Ababen More Rayuwa
Asusun kula da walwalar ɗalibai: Domin walwalar ɗalibai da suke son karɓar bashin ɗalibai, an ware wani kaso daga cikin asusun welfare na hukumar kula da lafiya don amfanuwar ɗalibai a matsayin bashi da ake basu.
Abinci: Ɗalibi shi ne wanda aka karɓa domin ya yi karatu bisa ƙa’idojin koyarwa na jami’a, kuma tsarin karatun jami’ar ya amince da shi. Shi ne wanda zai iya amfani da tsarin abinci na makaranta na iya tsawon shekarun karatu da aka ayyana masa. Ɗalibin da ya cika sharuɗan da jami’ar ta saka na zama a hostel ɗin makarantar zai iya amfani da duk wani sabis da ya shafi abinci wanda jami’a ta tanada. Akwai katin da jami’a ta tanadar ma ɗalibai wanda za su iya amfani da shi a matsayin katin shaida, katin abinci, hostel, da sauran hidimomi na jami’ar.
Ofishin kula da harkokin abinci, ofishin kula da al’adu, da ofishin kula da al’amuran ɗalibai, waɗannan ofisoshin su ke da alhakin tafiyarwa da bin diddigin al’amuran da suka shafi abincin ɗalibai bisa la’akari da ƙa’idojin da aka ayyana. Domin samar da abincin ɗalibai (na safe, na rana, da na dare), jami’ar na amfani da tsarin kai-tsaye da su ke kira da “Tsarin Automasiyon” wanda ke bada damar ɗalibai su biya kuɗin abinci su kuma yi rizab ɗin abinci online. Dalibai za su iya karɓar suna da lambar sirri na shiga shafin sayen abinci daga sashen kula da harkokin abinci da al’adu na jami’ar. Haka kuma za’a iya saka kuɗi a asusunsu na sayen abinci ta hanyar amfani da katin ɗalibai. A shafin sayen abinci na jami’ar, akwai list ɗin kalolin abinci da ke akwai, saduwa da banki, wurin sayen abinci, wurin shigar da ra’ayi a kan ingancin shafin.
Harkokin Wasanni: Gabatar da darasin motsa jiki – neman izinin tsara rana da lokutan gabatar da azuzuwan motsa jiki – daidaita tsarin gudanarwa domin samun malaman da za su koyar da darasin – tura makin ɗalibai ga sashen kula da harkokin ɗalibai da kuma rahoton aikin malamai domin biyan albashinsu. Ana buɗe sashen motsa jiki (physical education) daga ƙarfe 7:30 na safe zuwa 15:30 domin sauraren koken ɗalibai.
Gabatar da ƙarin wasu shirye-shiryen wasanni a ɓangarori daban-daban na dukan fannonin wasanni bisa ƙa’idojin gasa na hukumar lafiya waɗanda ake shirya gasa da su a kowace shekara (a ƙayyadaddun ranaku da lokuta) domin amfanuwar ɗalibai maza da mata, bayan an tsara gasar ana nemo alƙalai masu kyau sannan a sanar da ɗalibai ta shafin jami’a da sauran kafofin da ake da su. Ana zaɓe ɗaliban da suka yi bajinta a tura su wuraren gasa daban-daban a ƙarƙashin mai horarwa.
Sansanin Dalibai: Sansanin ɗalibai tafiye-tafiye ne na ƙungiyar ɗalibai waɗanda a kan shirya bisa izinin sashen al’adu na jami’a, kuma ya kasu kashi biyu:
Kashi na farko: Sansanonin al’adu: Sun haɗa da tafiye-tafiyen ziyara, wasanni, fasaha, shaƙatawa, halartar bukukuwan al’adu da fasaha.
Kashi na biyu: Sansanonin ilimi: Sun haɗa da halartar tarukan nuna gwaninta, ziyarorin gani da ido na musamman, tarurruka, zaune-zaune da ziyarorin kimiyya, tafiye-tafiyen karatu da bincike, ƙungiyoyi, cibiyoyi, ƙungiyoyi masu lasisi, da sauransu. Haka kuma sassan gudanarwa na jami’a za su iya karɓar izinin shirya yawon buɗe ido domin ƙarin ilimi a kan aikinsu.
Domin samar da yanayi na walwala da sakin jiki tare da damar karatu da ƙarin ilimi, jami’ar tana shirya sansanoni na al’adu, addini, da shaƙatawa a kowace shekara. Ta hanyar shiga waɗannan shirye-shiryen, ɗalibai suna bunƙasa ƙwarewarsu a fannin zamantakewa.
Wurin Kwana: Ana tura buƙatar neman masauki ne ta intanet (online), ana kuma biyan kuɗin masaukin ne bisa ƙa’idojin hukumar kula da masaukan baƙin ɗalibai da sunayen waɗanda ta tantance. Ɗalibai na zuwa sashen kula da al’amuran masauki da kansu don cike fom da gabatar da hotonsu domin a buɗa musu fayil, a kuma basu wasiƙar amincewa da zamansu a masaukin da aka ayyana musu.
Shawara ga ɗalibai:
_ Gabatar da daurori a kan ci gaban rayuwa
_ Gabatar da zaune-zaunen bada shawara da jagoranci
_ Gabatar da ayyukan Neurofeedback
_ Ayyukan Nazarin halayya (Psychology)
_Samar da ayyukan yi
_ Gudanar da tarukan bada shawara, kwamitin psychology
_ Shirya daurorin sanin makamar rayuwa
Yanayin Wuri
Qazvin University of Medical Sciences na cikin unguwar Shaykh Abad, a titin Bahonar na garin Qazvin. Jami’ar na kusa da wurare kamar; Kotu, tashar CNG ta Bahonar, General Court, Wakilin Saipa Kermani, da kuma Babbar Jami’ar Payamnoor ta Qazvin.
Saduwa da Jami’a
Adireshi: Qazvin – titin Shahid Bahonar – Qazvin University of Medical Sciences.
Shafin jami’a: https://qums.ac.ir/
Tambayoyin da ake yi game da Qazvin University of Medical Sciences
Ko jami’ar na bai wa ɗalibai masu iyali wurin kwana?
Duba da ƙarancin wuri, ba duka ɗalibai masu iyali ne za su iya samun masauki ba.
A wasu ɓangarori ne sashen bada shawara ga ɗalibai ke gabatar da shawara a online?
Ana bada shawarwari ga ɗalibai a fannoni kamar haka:
_ Karatu
_ Shawarwari a kan abubuwan da suka shafi tunani
_ Shawara a kan auratayya
_ Shawarwarin da suka shafi iyali, da na ma’aurata
_ Tunani, halayya, karatu, da sauransu
Yaya ɗalibi zai yi idan ya manta lambobin sirrinsa na shiga shafin sayen abinci?
Ya je wurin masu kula da harkokin abincin ɗaliɓai ya yi musu bayani.