Lardin Lorestan na ɗaya daga cikin lardukan yammacin Iran. Lardin na da girman murabba’in kilomita 29308 ɗauke da fiye da mutane 1,760,000. A Iran shi ne lardi na 13 a yawan jama’a; Khorramabad ne cibiyarsa. Lorestan wuri ne mai yawan tsaunuka, kusan dukansa yana kewaye ne da duwatsun Zagros. Jami’ar Lorestan (Lorestan University) kuma wata jami’ar gwamnati ce a garin Khorramabad, lardin Lorestan kuma an assasa ta ne a shekarar 1977. A ci gaban wannan rubutu za mu gabatar muku da bayani a kan yanayin karatu a Jami’ar Lorestan.
Gabatarwa
Jami’ar Lorestan ɗaya ce daga cikin jami’o’in ma’aikatar ilimi bincike, da fasaha ta Iran a garin Khorramabad. Jami’ar ta kasance cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare a ƙarƙashin Jami’ar Jundishapur ta Ahvaz a shekarar 1964 inda ta fara aikinta da karɓar ɗalibai a kwasa-kwasan Physics, Chemistry, Mathematics, da Biology a matakin digiri. Bayan juyin juya hali na Iran, an ɓalle ta daga jami’ar Jundishapur ta Ahvaz, inda ta ci gaba da ayyukanta a matsayin cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare mai zaman kanta.
A shekarar 1988 aka gabatar da babban shirin samar da Jami’ar Lorestan ga Majalisar Kula da Al’adu da Karatun gaba da Sakandare kuma ta amince da shirin, inda ayyukan gudanarwa na gina jami’ar suka fara a shekarar 1990, suka kuma kammalu a 1993 sannan ta koma “Jami’ar Lorestan”.
Yanzu haka akwai kimanin ɗalibai 9000 da malamai 503 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa Jami’ar Lorestan ta yi nasarar wallafa maƙala 9178 na ilimi a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Har ila yau, jami’ar ta wallafa mujalla 11 na musamman kuma ta shirya taruka 8 zuwa yanzu. Baya ga haka, ta wallafa maƙala 2760 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2023, manazartan jami’ar Lorestan sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu ne da muhimman kalmomin “Iran” da “Afat”.
Martabar Jami’a
A sabon sakamakon da tsarin ranking na TIMES ya fitar, Jami’ar Lorestan ta samu matsayi na 1000-1200 a tsakanin jami’o’in duniya, matsayi na 20 a cikin jami’o’i 37 na Iran. Jami’o’i 173 daga ƙasashen musulunci 19 ne suka samu shiga wannan ranking ɗin. Ita ce a matsayi na 7 a fannin Basic Sciences cikin jami’o’in Iran da suka samu shiga tsarin. Har ila yau, wannan jami’a ta zo na 11 a cikin jami’o’in Iran 37 a ɓangaren kwasa-kwasan Engineering da IT.
Kuɗin Makarantar Jami’ar Lorestan
Makarantu
Literature and Humanities
Wannan makaranta na da sassa 12 (departments) na koyarwa tare da malamai fiye da 80 na dindindin. Haka kuma, bayanan da muka samu daga shafin wannan jami’ar ya nuna cewa akwai kimanin ɗalibai 1995 da ke karatu a ƙarƙashin wannan makaranta.
Agriculture
An assasa ta a shekarar 1994 a kudancin garin Khorramabad. Makarantar na da sassa 10 na koyarwa, hakazalika bayanan da suka fito daga shafin makarantar ya bayyana cewa akwai kimanin ɗalibai 1800 masu karatu a ƙarƙashinta.
Basic Sciences
Wannan makarantar na da membobin tsangayar ilimi 78, da kwas 11 na digiri, 24 na mastas, da kuma kwas 16 na PhD.
Tech and Engineering
An assasa makarantar Engineering a shekarar 2003 kuma tana da department (sassa) 6 na koyarwa.
Veterinary Medicine
Ita kuma wannan makarantar an assasa ta da gine-gine masu girman murabba’in mita 6000, a shekarar 1993. A halin yanzu akwai kwas sama da 12 mabambanta da ake karantawa a cikinta.
Kwalejin Management da Economics
Wannan makaranta ta fara aiki ne a shekarar 2005 kuma a halin yanzu tana da malamai 16.
Cibiyoyin koyarwa
- Noorabad Higher Education Center
- Pol Dokhtar Higher Education Center
- Ashtar Higher Education Center
- Koh Dasht Higher Education Center
Kwasa-Kwasai
Kwasa-Kwasan department ɗin Humanities
- Natural Geography – Water and Meteorology
- Geographical Sciences
- Economical Science
- Management
- Educational Psychology
- General Psychology
Kwasa-Kwasan Basic Sciences
- Geology
- Petrology
- Organic, Inorganic, and Decomposition Chemistry
- Plant Physiology
- Biology – Plant Sciences
- Pure Mathematics
- Applied Mathematics
- Physics
- Kwasa-Kwasan Engineering
- Electrical Engineering
Kwasa-Kwasan department ɗin Agriculture and Natural Resources
- Soil Science
- Animal Nutrition
- Animal Science
- Marine structures
- Water Science and Engineering
- Plant Breeding
- Physiology of Agricultural Plants
- Agricultural Biotechnology
- Ecology of Aricultural Plants
- Forestry and Forest Science
- Courses of the Language Group
- Persian Language and Literature
- Arabic Literature
Ababen More Rayuwa
- Multipurpose hall
- Zauren wasannin kokawa da kare kai
- Zauren wasan table tennis
- Zauren gina jiki
- Ɗakin wasan chess
- Filin wasa na haki
- Filin gudu
- Rukunin buɗaɗɗun filaye kusa da hostel ɗin mata
- Zauren wasannin tsalle-tsalle
Hostel
Ɗaya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ya kamata a lura da su wurin zaben jami’a musamman ga ɗalibai mata waɗanda ba ‘yan gari ba, shi ne wurin kwana (hostel). Saboda haka yana da kyau mu ambaci cewa wannan jami’a tana da rukunin wuraren kwanan ɗalibai na mata da na maza a cikin harabar jami’ar, sannan kuma akwai wasu wuraren kwana masu zaman kansu da suke da alaƙa da jami’ar a cikin garin na Khorramabad.
Laburaren Jami’a
Masu sha’awar amfani da laburare, su san cewa jami’ar Lorestan na da sashe ɗaya na laburare mai ɗauke da kimanin litattafai 63000. Sashen ya fara aikinsa ne daga shekarar 1977 a fannonin Basic Sciences, Human Sciences, Engineering, Agriculture, yana da litattafai da sauran rubututtuka masu inganci a harshen farsi da latin. Akwai kimanin litattafan larabci da farisanci guda 4900, da kuma na latin sama da 140000 a laburaren.
Yanayin Wuri
Jami’ar Lorestan na cikin garin Khorramabad a titin Imam Khomeini, babbar hanyar Khorramabad mai suna Sepid dasht. Ta fuskar yanayin muhalli kuma, jami’ar na kusa da cibiyoyi kamar Makarantar Firamare ta Shahid Naseri, da masaukin baƙi masu yawon buɗe ido na Alachegh.
Adireshi: Khorramabad, titin Imam Khomeini, hanyar Khorramabad, Dasht
Shafin jami’a: https://www.lu.ac.ir