Garin Kermanshah shi ne cibiyar lardin Kermanshah kuma yana daga cikin manyan garuruwan ƙasar Iran. Kasantuwar ɗalibai masu yawa na sha’awar karatu a wannan gari, mun shirya tsaf domin kawo muku bayanan da za su taimaka muku wurin sanin wannan gari na Kermanshah.
Kermanshah
Garin Kermanshah ɗaya ne a cikin garuruwa ɗimbin tarihi da al’adu na ƙasar Iran, ya samo asali tun shekarar 3500 ƙamariyya. A lokacin daular Ashkaniyan yankin ya kasance muhalli a cikin gari kafin a maida shi fada ta biyu ta sarakunan Sasaniyan a ƙarnin miladiyya na 4, daga lokacin ya ci gaba da zama cibiyar Sasaniyawa ta biyu har lokacin harin larabawa ga ƙasar Iran. A tsakanin wannan lokacin an gina lambuna masu girma wanda sarakunan sasaniyawa ke zuwa shaƙatawa a ciki.
Ƙarni uku bayan harin musulmai an samu dauloli biyu da suka mulki garin, Kurd Hasanwayan da Bani Ayaran. A lokacin daular Seljukiyan da aka yi a ƙarni na 11 na miladiyya, an zaɓi garin a matsayin babban garin Kurdistan. A ƙarnonin tsakiya an kasance ana kallon Qarmasin a matsayin ɗaya daga cikin yankunan ajami guda huɗu na Iraq. A lokacin ana kiran yankin Jabal da ‘Iraƙin Ajamawa’ don kar a ɗauka ɗaya take da Iraƙin Larabawa.
A zamanin Safawiyan, dangin kurdawa na Zanganeh sun kafa wata daula wadda ta kai har farkon ƙarni na 19 tana ci. Garin Kermanshah ya kasance ƙarƙashin mulkin Qajarawa kafin ya koma cibiyar kasuwanci daga rabin ƙarni na 19. A yaƙin duniya na farko da na biyu garin ya faɗa hannun sojojin mamaya amma ya samu ƴanci bayan kammala yaƙin.
Zirga-Zirga
ZIrga-Zirga a cikin gari
Manyan hanyoyi
Saboda matsalar cinkoson ababen hawa da garin Kermanshah ya fuskanta musamman a shekarun farko na bayan yaƙin Iran da Iraq, hakan ne ya tilasta amfani da tsarin manyan hanyoyi. Akwai wani babban shataletale da aka gina a yammacin garin a saba’inoni (1970s) wanda yanzu ya shigo cikin gari da yake garin ya ci gaba da bunƙasa. Wannan shataletalen yanzu an mayar da shi park ɗin kan hanya (Bagh Rah) inda aka soma gina wani sabo. Hakazalika an buɗe wani shataletalen a gabacin garin a shekarar 2000. An buɗa wasu manyan hanyoyi biyu masu suna Shahid Dayipour da Shahid Sarabian a shekarar 2022. A halin yanzu mahaɗar manyan hanyoyin garin ta haɗa hanyoyi shida a ɓangaren gabas, yamma, kudu, da arewacin garin. Daga cikin akwai:
- Babbar hanyar Imam Khomeini (Shataletalen Gabas)
- Bagh Rah Imam Ali (Shataletalen Yamma)
- Babbay hanyar Khalije Fars a kudu
- Babbar hanyar Sayyad Shirazi a arewa
- Babbar hanyar Shahid Dayipour mai tsayin kilomita 3, daga Beheshte Zahra zuwa Shahrake Aryashahr
- Babbar hanyar Shahid Sarabian mai tsayin kilomita 3, daga Shahrake Kihanshahr zuwa babbar hanyar Imam Khomeini
Sakakkun hanyoyi
- Azadrahe Hamadan – Kermanshah
- Azadrahe Kermanshah – Hamil
- Azad Rahe Kermanshah – Khosrovi
Bus
An assasa kamfanin zirga-zirgar motocin bus na wannan gari ne a shekarar 1965 inda ya fara aiki da wani adadi na motocin bus da minibus daga hanyar Meidane Vaziri (Nawab Safavi) zuwa Meidane Jalili. Yanzu haka kuma akwai motoci 262 na bus masu aiki a yankuna 5 a wannan garin.
Tashar Mota
Akwai tashar mota guda biyu a garin Kermanshah. Ana amfani da motocin bus, minibus, da ma ƙananan motoci a tasahar Shahid Kavyani wurin jigilar fasinjoji zuwa garuruwa daban-daban. Kamfanin “Iranpeyma” da na “Ta’awonie Mosaferbari 7” na sayar da titikin matafiya a titin Modarres, inda da kamfanin “TBT” ke sayar da nasu a Meidane Sadegh. Akwai wata tasha mai suna “Payane Rah Karbala” inda ake jigilar fasinjojin wasu garuruwa da ke gabacin garin Kermanshah da matafiyan ƙasar Iraq.
Filin jirgin ƙasa da ƙasa
Filin jirgin lardin Kermanshah mai suna “Ashrafi Isfahani International Airport”, shi ne filin jirgi mafi inganci kuma mafi muhimmanci a gabacin ƙasar Iran.
Jiragen ƙasashen waje: Dubai, Damascus, Jiddah, Solaimanieh, da Istanbul.
Jiragen cikin gida: Tehran, Mashhad, Kish, Bandar Abbas, Kerman, Shiraz, Asaluyeh, da Sari.
Karatu a Kermanshah
Garin na da kayan aiki da cibiyoyin koyarwa masu inganci, akwai jami’o’i irinsu Kermanshah University of Medical Sciences. A lardin Kermanshah akwai jami’o’i da cibiyoyin koyarwa 24. Jami’o’in lardin sun keɓantu da wallafa mujallun musamman na kimiyya guda 21 kuma zuwa yanzu sun wallafa maƙaloli guda 246. Lardin ya karɓi baƙuncin tarukan kimiyya guda 42.
Researchers na jami’o’in wannan lardin sun wallafa maƙala 42490 na ilimi wanda suka haɗa da maƙalar mujalla 19061 a tarukan cikin gida, da maƙala 7754 na ƙasa da ƙasa. A shekarar 2018 ne aka samu kimanin ɗalibai 34,676 da ke karatu a jami’o’in lardin Kermanshah a ƙarƙashin kulawar malamai da ma’aikatan tsangayar ilimi 1,770.
Wuraren yawon buɗe ido
Park ɗin jeji na “Taghe Bustan” da ke arewa maso gabacin garin Kermanshah wanda a cikinsa akwai tsaunuka, idanuwan ruwa, koren sarari, ƙoramu, zanen duwatsun lokacin Sasaniyawa, wurin farauta na Khosro Parviz, wurin ya kasance mai jan hankali ga sarakunan Sasaniyawa saboda yanayi mai daɗi da yake da shi sakamakon haka aka riƙa amfani da shi a matsayin wurin farauta na gidan sarauta. Yanzu haka wurin ɗaya ne daga cikin wuraren yawon buɗe ido na shaƙatawa da na tarihi masu jan hankali.
Hakazalika akwai kogon Parau wanda shi ne mafi zurfi a Iran kuma na biyu a abubuwan tarihi a Kermanshah, a kowace shekara akwai masu hawan kogo na ciki da wajen Iran masu yawa da ke zuwa wannan wuri. Daga cikin abubuwan da Kogon Parau ya keɓanta da su shi ne kasantuwar ƙofarsa a tsroro mai nisan mita dubu uku daga saman teku, wannan nisa shi ne mafi yawa a duniya, dalilin haka ake masa laƙabi da “Everest na kogunan duniya”.
Abubuwan Tarihi
- Tagh Bastan
- Sangneveshte Biston
Mu’amalar ƙasa da ƙasa
Ofisoshin Jakadanci
- Iraq
- Birtaniya
- Russia