[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Karatu a Jundishapur University of Medical Sciences

Loading

Karatu a Jundishapur University of Medical Sciences da ke garin Ahwaz a matsayinta na ɗaya daga cikin cibiyoyin karatu masu tarihi kuma matakin da ta taka a ɓangaren ilimi abun lura ne sosai ga mutane. A wannan rubutun, mun maida hankali akan batun karatu a Jundishapur University of Medical Sciences, kayan aikinta, da sauransu.

Gabatarwa

A garin Ahwaz akwai fitattun jami’o’in Iran (domin ƙarin bayani kuna iya bincikar rubutun Karatu a garin Ahwaz) Misalin ɗaya daga cikin waɗannan cibiyoyin, ita ce Jundishapur University of Medical Sciences and Health Services Ahwaz wadda aka assasa a shekarar 1954. Saboda bunƙasar matsayinta na ilimi tun bayan assasa ta zuwa yanzu, ana kallon Jami’ar Ahwaz a matsayin jami’a mafi muhimmanci a kaf jami’o’in yankin Khuzestan. A halin yanzu, akwai ɗalibai 6400 da malamai 646 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa, wannan jami’a ta wallafa maƙalar ilimi guda 3521 a taruka da wallafe-wallafen cikin gida,[1161 مقاله ژورنالی و 2360 مقاله کنفرانسی] da maƙaloli 9053 karɓaɓɓu a matakin ƙasa da ƙasa. Hakazalika ita ce mamallakiya kuma mawallafiyar mujalloli na musamman guda 6. Zuwa yanzu an gudanar da taruka 9 a cikin wannan jami’a.

Martabar Jami’a

Ahvaz Jundishapur Uiversity of Medical Sciences a karonta na farko wajen shiga tsarin ranking na Times shekarar 2022, ta yi nasarar samun matsayi na 601-800 kuma ta shiga sahun fitattun jami’o’i na duniya.

Makarantu

Bayan kafa makarantu daban-daban masu zaman kansu, adadin ɗaliban da ake karɓa a wannan jami’ar shima ya ƙaru. _Makarantar Medicine _Makarantar Public Health _Makarantar Pharmacy _Makarantar Rehabilitation _Makarantar Allied Medical Sciences _Makarantar Dentistry _Makarantar Nursing & Midwifery _Harabar Khodgardan _Bustan Nursing College

Asibitoci

_Asibitin Shafa, Ahwaz _Asibitin Baghaee2, Ahwaz _Asibitin Razi, Ahwaz _Asibitin Sinai, Karun _Asibitin Abozar, Ahwaz _Asibitin Salamat, Ahwaz _Asibitin Golestan, Ahwaz _Asibitin Imam Khomani, Ahwaz _Asibitin Ayatollah Taleghani

Cibiyoyin Bincike

_Nanotechnology _Cancer _Hearing _Toxicology _Gastrointestinal infections _Cardiovascular _Environmental _Research consultation _Laboratory Animals _Improving Reproductive Health _Comprehensive Research Laboratory _Infectious and Tropical Diseases _Center for the Growth of Pharmaceutical Technologies _Fertility and Infertility and Fetal Health _Clinical Research Development Unit of Golestan Educational Center _Physiology _Gastrointestinal Infections _Medicinal Plants _Research Consultation _Marine Pharmaceutical Sciences _Comprehensive Research Laboratory _Nutrition and Metabolic Diseases _Hyperlipidemia Research Center _Renal Insufficiency _Diabetes _Pain _Cellular and Molecular _Air Pollution _Eye Infections _Menopause and Andropause _Thalassemia and Hemoglobinopathy _Social Factors Affecting Health _Musculoskeletal Rehabilitation _Nursing Care in Chronic Diseases

Kwasa-Kwasan karatu

_General Practitioner _Pharmacy _Dentistry _Surgery Room _General Hygiene _Obstetrics and Gynecology _Urology _Orthopedics _Nursing _Radiology Technology _Audiologists _Laboratory Sciences _Nutritional Science _Speech Therapy _Midwifery _Anesthesia _Environmental Health Engineering _Occupational Therapy _Physiotherapy _Glands _Children _Neurosurgery _Anesthesia _Medicinal Chemistry _Oral and Maxillofacial Surgery _Health Information Technology Anesthesia _Physiotherapy _Audiology _Medical Genetics _Medical Entomology and Fight Against Vectors _Clinical Pharmacy _Management of Health Services _Poisoning and Forensic Medicine _Orthodontic Da sauransu… Domin ƙarin bayani, ku sauke list ɗin kwasa-kwasan Jundishapur University of Medical Sciences

Ɗakunan Karatu

_Laburaren School of Health _Laburaren School of Nursing and Midwifery _Laburaren Medical School _Laburaren Paramedical school _Laburaren Paramedical School _Laburaren School of Pharmacy _Laburaren School of Dentistry _Laburaren Bostan Nursing School _Laburaren Autonomous School _Laburaren Asibitin Abuzar _Laburaren Asibitin Imam Khomeini _Laburaren Asibitin Razi _Laburaren Asibitin Shahid Beqaei 2 _Laburaren Asibitin Taleghani _Laburaren Asibitin Golestan _Laburaren Digital

Abubuwan Alfahari

_Lashe matsayi na biyi a gasan Olympiad na ɗalibai a filin asibiti _Lashe mastayi na farko a jarabawar kwamitin musamman na cututtuka masu yaɗuwa _Samun matsayi na biyu a fannin ilimin ilimin cututtukan jini na yara _Samun karɓuwar dukan ɗalibai a babbar jarabawar ƙasa da ƙasa _Zaɓen cigaban karatu – Kwas ɗin Pharmacy a matsayin kwas ɗin online

Abubuwan more rayuwa

Bayan kammala karatunsu, ɗaliban Ahvaz Jundishapur University of Medical Sciences zasu iya yin attachment da internship ɗinsu a asibitoci da cibiyoyin jinya tare da sa idon Jundishapur University of Medical Sciences. Ɗaya daga cikin muhimma ayyukan Jundishapur University of Medical Sciences ga ɗalibai da kuma bunƙasa matakin ilimsu, shi ne samar musu da masana kuma ƙwararrun malamai. Jundi Shapur University of Medical Sciences, kamar dai sauran jami’o’in, ta yi tanadin kammalallun wuraren kwanan ɗalibai ta fuskacin kayan aiki domin kulawa da lafiya da kuma walwalar su. Ɗalibai zasu iya amfani da waɗanna hostel dai-dai da matakin karatunsu, misali, ɗalibai masu karatun masters ko diploma zasu iya amfani da hostel na iya tsawon shekara 2 kawai, ɗaliban digiri kuma shekara 4, ɗaliban Medicine da Dental kuma iya shekara 6 kawai. List ɗin wuraren kwana: _Wurin kwana na Bostan (na ɗalibai maza) _Wurin kwanan Gholestan ( na ɗalibai mata) _Wurin kwana na Shohada lamba 1 (na ɗalibai maza) _Wurin kwana na Shohada lamba 3 (na ɗalibai maza)

Muhalli:

Jami’ar Jundishapur na nan kusa da Chamran University of Ahvaz and Farvardin, Dey, Randabawul na Shohada. Ta fuskar muhalli, tana kusa da wurare kamar Asibitin Golestan, Gidan tarihi na Ahvaz Science and Nature, Babban ginin Sazeman Markazi, Bankin Refahe Kargaran, Central Research Laboratory, Soma Fast Food Restaurant, Shahrake Barq, da kuma Tiara Restaurant.

Magana da Ahvaz Jundishapur University of Medical Sciences

Adireshi: Titin Golestan – Ahwaz -Iran

Tambayoyin da ake yawan yi

  1. Wasu irin takardu ake buƙata domin yin rajista a Jundishapur University of Medical Sciences? Passport, hoto, script na results, Certificate, CV, Motivation letter, Recommendation letter.
  2. Shin biyan kuɗin hostel wajibi ne?Eh, biyan kuɗin hostel wajibi ne.
  3. Shin zai yiwu ɗaliban Iraki su yi transfa daga Junsdishapur University of Medical Sciences?Eh, ɗaliban Iraƙi zasu iya yin transfa zuwa ƙasarsu bayan sun kammala zango biyu na karatu.
[neshan-map id=”14″]
Related Posts
Leave a Reply