Jami’ar Semnan (Semnan University) ita ce jami’a mafi girma a lardin Semnan kuma ita ke da alhakin sa ido da tantance manyan cibiyoyin koyarwa na lardin. Shekaru 45 sun shuɗe tun lokacin da wannan babbar cibiyar koyarwa ta farko a garin Semnan ta fara aikinta. Tawagarmu ta sauƙaƙe muku samun bayanai masu muhimmanci game da yanayin karatu a wannan jami’a ta Semnan.
Gabatarwa
Jami’ar Semnan ita ce uwar jami’a ta lardin na Semnan tare da Jami’ar Damghan, Mai tarihin kusan rabin ƙarni a ayyukan koyarwa, bincike, da fasaha, wadda aka assasa a shekarar miladiyya ta 1975 a matsayin cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare ta farko a garin Semnan, kuma a halin yanzu take girman sama da hekta 800, haraba 5 na koyarwa, ƙungiyoyin bincike mabambanta tare da cibiyoyin bincike, park ɗin kimiyya da fasaha, harabar international affairs, cibiyar karatun online, da ma’aikatan tsangayar ilimi ko malamai kusan 400 da ɗalibai 14000 a matakan karatu daban-daban, kusan kwas ɗin karatu 300. Ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in ƙasar Iran ita da jami’ar karatun likitanci ta wannan gari.
Zuwa yanzu wannan jami’a ta yaye sama da ɗalibai dubu hamsin a fagen ilimi da horarwa, 10000 daga ciki a matakin postgraduate wanda akwai ɗaruruwan ɗaliban ƙasashen waje a cikinsu. Bayanai sun nuna cewa jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi guda 11559 zuwa yanzu a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida, da maƙala 7515 a matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Semnan ta mallaki lambar yabo kuma ta wallafa mujalla 12, sannan ta shirya taruka 21.
Martabar Jami’a
Jami’ar Semnan tana da ranking mai kyau a tsarukan ranking na cikin ƙasa da na duniya irinsu ISC, Shanghai, Times, Leiden, URAP, U.S News, da sauransu… Kuma akwai gomman malamai da masu bincike na wannan jami’a waɗanda suka shiga sahun fitattun masana kimiyya na duniya.
A ranking ɗin Times <Higher Education World University Rankings> na shekarar 2023, jami’ar ta zo a sahun manyan cibiyoyin koyarwa na yankin Asia kamar yadda ta saba a shekaru masu yawa a jere. Tsarin na TIMES ya tantance cibiyoyin koyarwa 928 daga ƙasashe 36 na yankin Asia, da cibiyoyi 65 daga Iran. Jami’ar Semnan ta zo a matsayi na 401 – 500 a tsakanin ƙasashen Asia, da matsayi na 1200 – 1500 a jami’o’in duniya.
Hrabobi
- Harabar Human Science
- Harabar Basic Science
- Harabar Technical
- Harabar New Sciences and Technologies
- Harabar Veterinary Medicine, Natural Resources da Agriculture
- Harabar Art
Makarantu
- Faculty of Electrical and Computer Engineering
- Faculty of Chemical, Oil and Gas Engineering
- Faculty of Industrial Engineering
- Faculty of Civil Engineering
- Faculty of Mechanical Engineering
- Faculty of Materials Engineering and Metallurgy
- Faculty of Mathematics, Statistics and Computer Science
- Faculty of Physics
- School of Chemistry
- Faculty of Basic Sciences (Department of Biology)
- Faculty of Humanities
- Faculty of Economics, Management and Administrative Sciences
- Faculty of Psychology and Educational Sciences (Mahdishahr)
- Faculty of Persian Literature and Foreign Languages
- Faculty of Tourism
- Faculty of Petroleum
- Faculty of Biotechnology
- Faculty of Nanotechnology
- Faculty of Aerospace Engineering
- Faculty of New Energy Engineering
- Faculty of Architecture and Urban Planning
- Faculty of Art
- Faculty of Veterinary Medicine and Animal Husbandry
- Faculty of Desertology
- School of Natural Resources
- Shahmirzad Veterinary School
Cibiyoyin da ke ƙarƙashinta
- Nahad Rahbari in Semnan University
- Semnan University Academicians’ Field, Semnan University Charity Foundation
- Teachers’ Basij of Semnan University
- The Audit Board of Universities in South Alborz Region (Semnan University and Damghan University)
- The Secretariat of the Higher Education Monitoring and Evaluation Board of Semnan Province
- Semnan University Science and Technology Park
- Laboratory of Human Interaction and Information of Semnan University
- Center for the Growth of Technological Units of Semnan University
- Industry Relations Office
- Center of Modern Sciences
- The Center of Flourishing Creativity
- Intellectual Property and Patent Consulting Office
- Entrepreneurship Center
- Technical Skill Development Center
- Network Security Center
Ƙungiyoyi da Cibiyoyin Bincike
- Advanced Materials Research Institute
- Research Institute of Advanced Building Technologies
- Information Technology Research Institute
- Advanced Computing Center
Laburare da ɗakin taron Jami’ar Semnan
An wallafa tsarin zanen ginin laburare da ɗakin taro na jami’ar wanda ake kan ginawa yanzu haka a cikin jami’ar, a fitattun shafunkan duniya a matsayin ɗaya daga cikin dabarun zanen architecture mafi kyau a duniya. Mujalla da shafin evolo na ƙasar America wanda yana kula ƙirƙirarrun tsarukan gini kaɗai waɗanda suke kan gaba kuma suke da daraja a wannan ƙarni na 21, shi ma ya shiga yin nazari mai zurfi a kan wannan tsarin (zanen) ginin.
A bayabayannan, fitaccen shafinnan na “arthitectural” ya sanya zanen ginin babban laburare da ɗakin taro na jami’ar Semnan a cikin jerin zane-zanen manyan architects na duniya irin su Zaha Hadid, Norman Foster, Steven Holl, da ƙungiyar BIG a matsayin tsarukan al’adu da suka fi kowasu yawan ‘yankallo a duniya.
Wannan tsarin har ila yau, ya shiga jerin gine-gine mafi kyau na duniya a bukin “World Architecture Festival” na shekarar 2010 tare da ginin gidan tarihi, zanen fitacciyar architect Zaha Hadid wanda shi ne ya lashe gasar.
A wannan project, an yi ƙoƙarin ganin cewa an tattara duka litattafai da sauran abubuwan laburare da zauren taronsa a wani wuri wanda za a iya tunawa da hotonsa cikin sauƙi. Sassa biyu ne suka gitta a saman iska, ta yadda za a iya ganinsu kamar a haɗe amma a zahiri ba haɗe suke ba. A yayinda aka ƙawata ginin da wasu gilashi masu duhu, suna wasa da haske gwanin ban sha’awa. Idan hasken rana ya ɗan lafa musamman a lokacin zafi, yanayin wurin yana yin daɗi sosai.
Ɗakin taron na da kujeru 1000, kujera 100 zuwa 200 na ɗakin meeting, multipurpose hall, ɗakin jira, da sauransu.
Laburaren kuma na da sashen karatu wanda rabinsa ya keɓanci karatun jaridu, ma’ajiya, cafe, zauren tattara references, ofishin tafiyarwa, da sauransu.
Injiniyoyin New Wave Architecture su ne suka zana tsarin ginin laburare da ɗakin taron jami’ar Semnan a shekarar 2006, wanda ake kan ginawa yanzu haka a wani fili mai girman murabba’in mita 8000.
Kuɗin makarantar Jami’ar Semnan
Science and Technology Park
An assasa park ɗin Science and Technology na jami’ar Semnan bayan amincewar tawagar gwamnatin Iran a wata ziyara da suka kai lardin Semnan a shekarar 2007, an gina wannan park ɗin ne a gefen jami’ar ta Semnan, shi ne park ɗin kimiyya da fasaha na biyu a lardin na Semnan.
Science and Technology Park na Jami’ar Semnan ɗaya ne daga cikin parks ɗin kimiyya da fasaha na ƙasar Iran kuma yana garin Semnan. An assasa park ɗin a shekarar 2007. Park ɗin yana da cibiyoyi kamar haka:
- Center for the Growth of Semnan Technology Units
- Center for the Growth of Technology Units – Mehdishahr (satellite) Unit
- Industry Relations Office
- Entrepreneurship Center
- Center for Modern Sciences (Science Park for Children and Adolescents)
- The Center of Flourishing Creativity
- Intellectual Property Consulting Center
- Office of Research Projects
- Office of Intellectual Property and Technology Transfer
- Idea Development and Future Studies Center
Wallafe-Wallafe da mujallun Jami’ar Semnan
- Journal of Modeling in Engineering
- Andisheh Science Magazine (Applied Chemistry)
- Journal of Faculty of Human Sciences (extensional science)
- Journal of Fiqh and Islamic Law Studies
- Specialized Quarterly Journal of Rhetorical Linguistic Studies
- Journal of Clinical Psychology
- The Magazine of New Ideas in Management
- Econometric Modeling Quarterly
- Journal of Veterinary Laboratory Research
- Journal of Applied Arts
- Studies in Arabic Language and Etiquette
- International Journal of Nonlinear Analysis and its Applications
- Journal of Rehabilitation in Civil Engineering
- Journal of Heat and Mass Transfer Research
- Transportation Infrastructure Engineering
- Iranian Journal of Cognition and Education
- Mechanics of Advanced Composite Structures
- Advances in Nanocomposite Research
Abubuwan More Rayuwa
- Zauren wasanni mai ɗaukar mutum 3500
- Fili mai grass carpet na asali da wurin gudu
- Fili mai artificial grass carpet, da hostel biyu na Farhangiyan
- Zauren wasan harbi
- Zauren gina jiki (Gym)
- Zauren Kausar (na mata)
- Filin wasa na yashi
- Hanyar keke a hostel ɗin Farhangiyan
- Sansanin kiwon lafiya a duka hostel
- Rukunin buɗaɗɗen filayen wasanni a hostel (volleyball, basketball, da sauransu)
- Cibiyar bada shawara a kan wasanni da lafiya
- Cibiyar Spirometry
- Cibiyar kimiyyar wasanni
- Cibiyar kiwon lafiya
- Rufaffen zauren wasanni (na mata)
Yanayin Wuri
Jami’ar Semnan na nan a unguwar Soukan ta garin Semnan, titin Mehrab. A kusa da jmai’ar akwai wurare kamar Kwalejin Electrical and Computer Engineering, laburare da ɗakin taro na jami’ar Semnan, kwalejin Civil Engineering na jami’ar Semnan, da Azad University ta garin Semnan.
Adireshi: Semnan, Soukan, titin Mehrab
Shafin jami’a: semnan.ac.ir