Khajeh Nasir Toosi University of Technology ɗaya ce daga cikin jami’o’in gwamnati na Iran a garin Tehran kuma jami’ar fasaha ta farko a Iran. An assasata ne a shekarar 1980 bisa amincewar majalisar sauyin al’adu inda aka haɗe manyan cibiyoyin koyarwa 9 aka sanya musu suna “University of Technology and Engineering” kafin a sanya mata sunan fitaccen masanin kimiyya na Iran wato “Khajeh Nasiraldeen Toosi” a shekarar 1988. Ku kasance tare da mu domin samun bayani game da yanayin karatu a wannan jami’a.
Gabatarwa
Jami’ar fasaha ta Khajeh Nasir Toosi na da ginshiƙan kimiyya 85 a halin yanzu, tare da laboratory guda 194 na karatu da na bincike, cibiyoyin bincike guda 13, ƙungiyoyin bincike 3, makarantun bincike 6, kamfanonin koyarwa 11, da masana’antu 28 masu aiki don cigabantar da mabambantan fannonin jami’ar.
Jami’ar ta yi nasarar shiga cikin nasarori daban-daban na ayyukan bincike na ƙasar Iran ta hanyar ƙulla yarjejeniya da kamfanoni daban-daban na ƙasar a babin magance waɗansu keɓantattun matsaloli. Tarin ayyukan bincike na jami’ar na nuna irin ƙarfinta a fannoni daban-daban na ilimi da masana’antu ta yadda duka ma’aikatan wasu fannonin za ku samu ko dai ɗaliban wannan jami’ar ne ko kuma sun yi karatu a cikinta.
Bayanai daga mabambantan shafukan ranking na duniya sun nuna cewa Jami’ar Fasaha ta Khajeh Nasir Toosi ta samu ci gaba sosan gaske.
Wannan jami’a na da makarantu 11 inda ake yin kwasa-kwasai 18 a matakin digiri, 53 a matakin masters, da kwas 23 a matakin PhD. A cewar Mahmoud Ahmadiyan mataimakin shugaban ofishin al’amuran koyarwa na jami’ar, idan za a kwatanta yawan malaman wannan jami’a bisa la’akari da yawan ɗalibanta, ga kowasu ɗalibai 18 akwai malami 1.
Martabar Jami’a
Bayanai daga mabambantan shafukan ranking na duniya sun nuna irin cigaban da jami’ar ta samu. Bayanan tsarin ranking na ISI, sun nuna cewa wannan jami’a ita ke samar da kaso 1 cikin ɗari na ilimin da ake samu daga jami’o’in duniya. A shekarar 2017 tsarin ranking na TIMES ya bayyana Jami’ar Fasaha ta Khajeh Nasir Toosi a cikin fitattun jami’o’i 6 na ƙasar Iran. Hakazalika a ranking ɗin shekarar 2018 wanda aka yi bisa la’akari da keɓantattun fannonin Physics, Astronomy, Pure Chemistry, da General Engineering, jami’ar ta zo matsayi na 3 a jami’o’in ƙasar Iran, a fannin Civil Engineering, Mechanical and Aerospace Engineering, Electrical Engineering, Mathematics, da Statistics kuma ta zo a matsayi na 4, a fannin Computer Science kuma ta samu matsayi na 2 a tsakanin jami’o’in Iran, duk a tsarin ranking na TIMES ɗin.
A tsarin ranking na URAP kuma jami’ar fasaha ta Khajeh Nasir Toosi ta zo a matsayi na 460 a tsakanin jami’o’in duniya, a fannin Technical Sciences – Engineering, Computer and Technology.
A tsarin ranking na Leiden na shekarar 2017 (CWTS Leiden Ranking) kuma, jami’ar ta shiga sahun fitattun jami’o’i 10 na ƙasar Iran, matsayi na 161 a jami’o’in yankin Asia, da kuma matsayi na 368 a duniya.
A tsarin ranking na QS na shekarar 2020, jami’ar ta samu matsayi na 401 – 450 a fannin Electrical Engineering, da matsayi na 451 – 500 a fannin Mechanical Engineering.
Har yanzu a tsarin na QS a shekarar 2023, jami’ar Khajeh Nasir Toosi ta samu matsayi na 351 – 400 a tsakanin jami’o’in duniya.
A shekarar 2023 tsarin CWTS Leiden Ranking ya bayyana jami’ar a matsayi na 900 – 1000 a jami’o’in duniya.
Tsarin TIMES a shekarar 2023 ya bayyana jami’ar a matsayi na 200 – 251 a yankin Asia, da matsayi na 1000 – 1200 a duniya.
Makarantu da cibiyoyi
- Faculty of Mathematics
- School of Chemistry
- Faculty of Physics
- Faculty of Electrical Engineering
- Faculty of Industrial Engineering
- Faculty of Civil Engineering
- Faculty of Computer Engineering
- Faculty of Mechanical Engineering
- Faculty of Engineering and Materials Science
- Faculty of Aerospace Engineering
- Faculty of Geodesy and Geomatics Engineering
- Sashen koyarwa na darussan General Studies
- Khajeh Nasir Al-Din Toosi University of Technology Business School
Kwasa-Kwasai
- ELectrical Engineering
- Mechanical Engineering
- Civil Engineering
- Aerospace Engineering
- Industrial Engineering
- Mapping Engineering
- Computer Engineering
- Engineering and Material Science
- Mathematics
- Physics
- Chemistry
Wuraren bincike
- Space Systems Design Research Institute
- Peptide Research Institute
- Information and Communication Technology Research Institute
- Remote Sensing Research Institute
- Power and Propulsion Systems Research Institute
- Oil Industry Productivity Research Institute
Kuɗin makarantar jami’ar Khajeh Nasir Toosi
desired section | Length of study period | Tuition price (annual) |
---|
Abubuwan More Rayuwa a jami’ar Khajeh Nasir Toosi
- Ɗakin karatu
- Zauren cin abinci
- Laburare
- Azuzuwan karatu ɗauke da majigin kallo
- Wurin kwanan ɗalibai
- Filin ball
- Filin wasan volleyball
- Filin wasan basketball
- Filin tattaki
- Table tennis
- Badminton
- Swimming Pool
- Gym
Alfanun karatu a jami’ar Khajeh Nasir Toosi
- Mu’amala da ƙwararrun malamai
- Ta’ammuli da kayan karatu na zamani
- Karatu a cikin jami’a mai babbar daraja
- Ta’ammuli da laboratory masu inganci
Wuraren kwanan jami’ar Khajeh Nasir Toosi
Jami’ar na da rukunin hostel guda 10 waɗanda za mu ambaci sunayensu a ƙasa.
- Wurin kwanan ɗalibai na Karamat
- Wurin kwanan ɗalibai na Andisheh
- Wurin kwanan ɗalibai na Sedaghat
- Wurin kwanan ɗalibai na Hekmat
- Wurin kwanan ɗalibai na Danesh
- Wurin kwanan ɗalibai na Ihsan
- Wurin kwanan ɗalibai na Iman
- Wurin kwana na Jamhori (na ɗalibai masu iyali)
- Wurin kwanan ɗalibai na Amir
Adireshin jami’ar Khajeh Nasir Toosi
Adireshi: Tehran, Mirdamad Gharbi, Block na 470
Shafin jami’a:kntu.ac.ir