A hankali, ƙasar Iran na ci gaba da zama wurin zuwan ɗaliban ƙasashe daban-daban domin cigaba da karatunsu, musamman baya-bayannan, musamman kuma a matakin postgraduate, wato master’s da phd. A wannan rubutun, za mu tattauna damarmaki da ƙalubalen karatu a Iran ga ɗaliban ƙasashen waje masu karatu a waɗannan matakan.
Karatu a Iran ga ɗaliban ƙasashen waje a matakin Master’s da PhD
Fannonin Karatu
Manyan jami’o’in Iran na ɗauke da ɗimbin kwasa-kwasan karatu a matakin masters da na phd. Daga cikin waɗanda suka fi shahara akwai:
- Engineering Sciences: Electrical Engineering, Mechanical Engineering, Civil Engineering, Computer Engineering
- Humanities & Social Sciences: History, Sociology, Language, Literature
- Medical Sciences: Medicine, Dentistry, Pharmacy.
- Basic Sciences: Mathematics, Physics, Biology, Chemistry.
Akwai jami’o’i masu yin karatu da turanci, wanda hakan ya fi sauƙi ga ɗaliban da basu iya yaren farsi ba.
Amfanin Karatu a Iran
Kuɗin makaranta da tsadar rayuwa: Kuɗin karatu da sauran buƙatun yau da kullum sun fi sauƙi a ƙasar Iran bisa ga ƙasashen turai da wasu ƙasashen.
Damarmakin Research: Jami’o’in ƙasar Iran na da damarmakin bincike da ƙirƙire-ƙirƙire masu yawa musamman a fannonin engineering da likitakci.
Bambancin Al’adu: Zama a Iran na bada damar buɗe idanu da sabawa da mabambantan al’adu.
Ƙalubale
Yare: Yaren karatu a mafi yawan jami’o’i shi ne yaren farsi, hakan babban ƙalubale ne ga ɗaliban da basu iya yaren ba. Kodayake akwai ɗaiɗaikun jami’o’i masu karatu da turanci, iya yaren farsi na da matuƙar muhimmanci ga wanda ke son ya zauna Iran.
Tsarin Gudanarwa: Tsarin admission da registration na iya zama mai rikitarwa da cin lokaci, sannan ɗalibai za su iya cin karo da matsaloli na ayyukan gudanarwa.
Matsin Lambar Zamantakewa: Wasu ɗalibai na iya fuskantar matsin lamba na zamantakewa sakamakon banbancin al’adu, wanda hakan na buƙatar a saba a hankali.
Samun Resources: A wasu fannonin karatu, resources ɗin karatu da na bincike na wahalar samu, saboda haka dole ɗalibai su nema da kansu.
Tsaro da yanayin zamantakewa:
Halin zamantakewa da siyasa a Iran na iya haifar da damuwa ga wasu ɗalibai. Fahimta da sanin yanayin al’adu da zamantakewar ƙasar na iya sauƙaƙa tajarubar karatu a ƙasar.
Tsarin Admission a Kwasa-Kwasan Master’s da PhD
Ga amatakan admission ga ɗaliban ƙasashen waje masu son karanta masters ko phd kamar haka:
Zaɓar jami’a da fannin karatu: Bincike a kan jami’o’i da fannonin karatu.
Cika form: Bayar da dukkan takardun da ake buƙata irin su transcripts, shaidar iya yare (TOEFL, IELTS, da sauransu), da CV.
Interview:Wasu jami’o’i na yin interview domin tantance matakin ilimin ɗalibi.
Neman Biza: Da zaran ɗalibi ya samu karɓuwa, abu na gaba shi ne ya tura buƙatar neman biza.
Goben Karatu a Iran
Ƙasar Iran na aiki tuƙuru domin faɗaɗa yanayin karatunta a matakin ƙasa da ƙasa ta hanyar bunƙasa ingancin karatu, mu’amalar ƙasa da ƙasa, da faɗaɗa karatu a harshen turanci. Hakazalika magance wasu ƙalubalen da bunƙasa kayan aiki ta yadda zai ƙara jan hankalin ɗaliban ƙasashen waje.
Rufewa
Karatu a Iran ga ɗaliban ƙasashen waje a mataki masters da PhD dama ce ta neman ilimi da faɗaɗa masaniya. Dukda ba za a rasa ƙalubale ba, amma akwai damarmaki na tattalin arziki da na bincike waɗanda ɗalibai za su amfana da su.
Waɗannan links ɗin na ƙasa za su iya taimaka muku:
Karatu a Iran + Jami’o’i 7 da Shawarwari 7 ga masu son zuwa karatu