Jami’ar Imam Khomeini (Imam Khomeini University) mai faɗin hekta 230, tana cikin garin Qazvin. Domin kaiwa ga hadafofinta, wannan jami’ar tana karɓar ɗalibai a matakan karatu daban-daban. A wannan rubutun zamuyi muku bayani ne game da karatu a Imam Khomeini University. Ku kasance tare da mu.
Gabatarwa
Wannan cibiyar ta fara gudanar da ayyukanta na koyarwa da sunan International Islamic University a shekarar 1983 daga bisani a shekarar 1991 bisa umurnin Hukumar Ilimi ta lokacin, aka haɗe ta da Dehkhoda Institute of Higher Education, sannan aka canza mata suna zuwa Imam Khomeini University.
A halin yanzu akwai ɗalibai 7930, malamai 516, da mambobin kwamitin ilimi 320 a wannan jami’a. Bincike ya nuna cewa, wannan jami’ar ta wallafa maƙalar ilimi 8572 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida,[3099 مقاله ژورنالی و 5473 مقاله کنفرانسی] da ƙarɓaɓɓun maƙalolin ƙasa da ƙasa guda 3190. Har ila yau, wannan jami’a ta mallaki mujalloli 20 na musamman. Zuwa yanzu an gudanar da manyan taruka 21 a cikin wannan jami’a.
Ga abunda Ayatullahi Sayyid Ali Khamena’i, jagoran juyin musulunci ya faɗa game da wannan jami’a: Wannan jami’ar ita ce ƙimar nizaminmu.
Karon farko a shekarar 2020, wannan jami’ar ta samu kutsawa cikin tsarin ranking na Times inda ta samu matsayi na 601-800 a jami’o’in duniya.
Makarantu
_Makarantar Engineering
_Faculty of Literature and Humanities
_Faculty of Architecture and Urban Planning
_Makarantar Social Sciences
_Makarantar Agriculture and Natural Resources
_Makarantar Koyon Yaren Farsi
_School of Basic Sciences
_Makarantar Islamic Sciences and Research
_Future and Research Institute
Kwasa-Kwasai
_History
_Law
_Accounting
_Political Sciences
_Statistics
_Physics
_Architecture
_Civil Engineering
_Mechanical Engineering
_Chemistry
_Computer Engineering
_Urban Planning
_Persian Language and Literature
_Arabic Language and Literature
_English Language and Literature
_Electric Engineering
_Qur’an and Hadith Sciences
_Industrial Management
_Psychology
_Plasma
_Geology
_Agricultural Biotechnology
_History and civilization of Islamic Nations
_Philosophy
_Sport Sciences
_Sociology
_Islamic Jurisprudence
_Material Engineering and Metallurgy
_Mathematics and Applications
_English Language Translation
_Da sauransu…
Domin samun cikakken list ɗin kwasa-kwasan da ake yi a Imam Khomeini University, ku sauke wannan fayil na ƙasa.
Kwasa-Kwasan Imam Khomeini University
Kuɗin Makarantar Imam Khomeini University
Ababen More Rayuwa
Wurin Kwana: Zuwa yanzu wannan jami’a nada hostel guda 10:
_5 daga cikin waɗannan hostel na ɗalibai maza ne
_4 na ɗalibai mata
_Hostel ɗaya kuma na ɗalibai masu iyali.
Hakazalika ana kan gina wani hostel mai ɗaukar mutum 350.
Laburare: Babban laburaren wannan jami’a mai girman murabba’in mita 4062 yana nan a yammacin masallacin jami’ar kuma yana fuskantar ɗakin taro. Wannan laburaren yana ɗauke da kimanin litattafai 105,000 a yarukan farsi, larabci, da latin.
Abubuwan Alfaharin Jami’a
_ Aiki da sauran jami’o’in duniya
_Tarayya a aiki da jami’ar Valencia ta ƙasar Spain
_Tarayya da jami’o’in Tarayyar ƙasar Rasha
_Aiki tare da jami’ar ƙasa da ƙasa ta China
_Da sauransu…
Yanayin Wuri
Imam Khomeini International University, tana cikin unguwar Elahia dake titin Daneshga, layin Gadeer, kuma tana kusa da muhimman wurare kamar; Babban gidan rediyo da talabijin na garin Qazvin, Asibitin Velayat, da kuma kamfanin bayar da tallafin motoci na ƙasa.
Adireshin Jami’a
Adireshin Jami’a: Imam Khomeini University Titin Gadeer, Titin Daneshga, Elaiha, garin Qazvin.
Shafin Makaranta: www.ikiu.ac.ir