Hakim Sabzevari University Sunanta a baya Sabzevar University Jami’ar gwamnati ce a cikin garin Sabzevar. Jami’ar Hakim Sabzevari na ƙunshe a cikin fili mai girman hekta 210, mai tsayin kilomita 10 a arewacin garin na Sabzevar. Wannan ita ce jami’a mai girma ta biyu da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, wadda da biyo bayan jami’ar Ferdowsi ta Mashhad da ke lardin Khorasan Razavi, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun jami’o’i 22 na Iran. Karatu a jami’ar Hakim Sabzevari batu ne da ke jan hankalin mutane a kowace shekara.
Gabatarwa
Jami’ar Hakim Sabzevari wata jami’a ce ta gwamnati a garin Sabzevar, lardin Khorasan Razavi, kuma an assasa ta ne a shekarar 1987. A halin yanzu akwai ɗalibai 9192 da malamai 674 a wannan jami’a.
Nazari ya nuna cewa wannan jami’a zuwa yanzu, ta wallafa maƙalar kimiyya guda 5755 a wallafe-wallafe da tarukan cikin gida. Jami’ar Hakim Sabzevari ta mallaki lambar yabo kuma ta sami nasarar wallafa mujalla 5 na musamman, sannan kuma ta karɓi baƙuntar taruka 13. Baya ga haka, zuwa yanzu jami’ar ta wallafa maƙala 2019 a matakin ƙasa da ƙasa. Za ku iya samun ƙarin bayani dangane da jami’ar ta Hakim Sabzevari a ƙasa. A shekarar 2023, manazartan wannan jami’a sun wallafa mafi yawan maƙalolinsu ɗauke da kalmomin ‘daidaito a zamantakewa’ da kuma <HEC>.
Aiki mafi muhimmanci a jami’ar Hakim Sabzevari shi ne bunƙasa ayyukan bincike da nazari, wanda zuwa yanzu a wannan fage, an rubuta litattafai 42 tare da fassara wasu 18, an gabatar da maƙaloli na ilimi guda 481 a tarukan cikin gida da na ƙasa da ƙasa, an kuma wallafa maƙala 336 ta hanyar membobin tsangayar ilimi a mujalloli daban-daban na gida da na waje.
Martabar Jami’a
Jami’ar Hakim Sabzevari a shekararta ta huɗu (a jere) da shiga tsarin ranking na times, ta shiga sahun fitattun jami’o’i (1001 – 1200) na duniya kuma tana gaba da wasu manyan jami’o’in Iran. Tsarin ranking na TIMES ɗaya ne daga cikin shahararrun tsarukan martaba jami’o’i (ranking) na duniya wanda ya fara aiki a shekarar 2004 tare da haɗin gwiwar tsarin QS, inda aka kira shi da tsarin ranking na “Times-QS”, daga shekarar 2010 zuwa yanzu kuma ya ci gaba da aiki tare da Reuters.
Bisa dogaro da bayanan ƙarshe na shafin ‘university-guru’, wanda ke aikin binciko matsayin jami’o’in duniya a cikin tsarukan ranking daban-daban, a tsarin ranking na Times, jami’ar Hakim Sabzevari ta yi nasarar samun matsayi na 11 a tsakankanin jami’o’in da suka cika sharuɗan ma’aikatar ilimi. Har ila yau, wannan shafin ya sanar cewa, jami’ar Hakim Sabzevari ta samu matsayi na 18 a cikin jami’o’in fasaha waɗanda suka cika sharuɗa, da matsayi na 26 a cikin jami’o’in Iran.
Kuɗin makarantar Hakim Sabzevari University
Makarantu
Makarantar Literature and Human Sciences
Makarantar Literature and Human Sciences ta fara gudanar da ayyukan ta na koyarwa a matsayin makaranta ta farko a jami’ar Hakim Sabzevari, a shekarar 1987. A halin yanzu akwai sassa (department) 5 kamar haka; Persian Language and Literature, French Language and Literature, Educational Sciences, da kuma Political Sciences, waɗannan sassa su ke da alhakin tafiyarda karatu da ayyukan bincike na kimanin ɗalibai 1300 a matakin digiri, mastas, da kuma PhD.
Makarantar Theology and Islamic Studies
An kafa Kwalejin ‘Theology and Islamic Studies’ a shekarar 2009, kuma a halin yanzu tana da kwasa-kwasai guda biyar a matakin digiri, 7 a mastas, ɗaya a PhD.
Makarantar Physical Education
Wannan kwalejin ta fara aikinta na koyarwa a shekarar 2006 a matsayin department ɗin Physical Education a ƙarƙashin kulawar kwalejin Literature and Human Sciences, tare da malamai biyu. A watan February na shekarar 2016 ne rukunin farko na ɗalibai masu karatun digiri a sashen physical education su 30 suka fara karatunsu a department.
Ta hanyar ɗaukar ƙwararrun ma’aikata biyu da jawo membobin tsangayar ilimi a jika, cikin sauri aka samar da kayan aiki da na karatu waɗanda ake buƙata a wannan kwas ɗin, abubuwa kamar zaurukan wasanni daban-daban, filin kokawa da wasan table tennis, swimming pool, filin wasa mai haki, da ɗakin gina jiki.
A shekarar 2004 ne bayan ƙara yawan malamai da kayan aiki, aka buɗe matakin mastas a wannan sashen. Haka kuma a shekarar 2006 an ƙaddamar da reshen Sports Physiology a matakin mastas, 2010 aka soma sports physiology a PhD, sai kuma a 2012 inda aka fara kwas ɗin Movement Behavior da na Sport Management a matakin mastas.
An kafa Kwalejin Physical Education a September 2007 tare da amincewar majalisar jami’ar. Baya ga horarda ƙwararru (digiri, mastas da PhD), a kowane term ana gabatar da sama da azuzuwa 80 na general physical education 1 & 2 ga ɗalibai 1600 masu karatun wasu kwasa-kwasan daban.
Makarantar Geography and Environmental Sciences
Wannan kwalejin an kafa shi ne a shekarar 2009 lokacin da aka ɓamɓare sassan karatu na geography daga kwalejin Literature and Human Science, sashen biology kuma daga kwalejin Basic Sciences, inda ya fara aiki da sassa guda uku kamar haka; Nature Geography, Human Geography, da Environment. A halin yanzu yana da malamai 23 waɗanda dukansu membobi ne a tsangayar ilimi, sama da ɗalibai 825 a matakin diploma, HND, digiri, mastas, da PhD.
Makarantar Mathematics and Computer Science
Kwalejin Mathematics na ɗaya daga cikin departments ɗin da suka fara aiki tun lokacin assasa jami’ar kuma a halin yanzu tana da kwas 4 a matakin digiri, kwas 15 a mastas, 2 kuma a PhD (Algebra da Analysis). A wannan kwalejin ake gabatar da kwasa-kwasan Computer Sciences a digiri da mastas.
Makarantar Basic Sciences
Wannan kwalejin ya fara ayyukansa na koyarwa da bincike ne a shekarar 1995. A halin yanzu yana da department 3 kamar haka; Biology, Chemistry da Physics, waɗanda ke da alhakin gudanar da ayyukan koyarwa da nazari ga kimanin ɗalibai 1592 a matakin digiri, mastas, da PhD.
Makarantar Technology and Engineering
Ita kuma wannan makaranta ta fara gudanar da ayyukanta ne a shekarar 1997 tare da makarantar Literature and Human Science, da ta Basic Sciences. A halin yanzu akwai department guda 10 na technology and engineering a makarantu 4 mabambanta. Daga ciki akwai department ɗin Civil Engineering, Mechanical Engineering, da Materials Engineering (polymer) a ƙarƙashin kwalejin na fasaha, kuma su ke da alhakin tafiyarda ayyukan koyarwa da na bincike ga kimanin ɗalibai 960 a matakan digiri, mastas, da PhD.
Makarantar Electrical and Computer Engineering
Tarihin kafa wannan kwalejin ya samo asali ne tun shekarar 1997, da kuma lokacin da aka fara ɗaukar ɗaliban fannin Electricity, a matakin diploma. Ta hanyar kammala membobin tsangayar ilimi da kuma samar da kayan aiki na ɗakunan gwaje-gwaje (laboratories), da buɗa kwasa-kwasan Electrical-Electronic Engineering, Mechatronics Engineering, da Computer Engineering, a shekarar 2009 wannan kwalejin ya fara cin gashin kansa. A halin yanzu kwalejin na ɗauke da kimanin ɗalibai 922 a kwasa-kwasai mabambanta na electrical engineering, medical engineering, da mechatronics.
Makarantar Architecture and Urban Planning
Makarantar Architecture and Urban Planning ta fara ayyukanta na karatu da bincike a shekarar 2013. A halin yanzu makarantar na aiki da department biyu na Architectural Engineering da Restoration of Historical Buildings. Ya kamata a san cewa department ɗin architecture ya fara aiki ne tare da karɓar ɗalibai a shekarar 1997.
Ita ce makarantar farko ta Architecture da Urban Planning a gabacin Iran kuma yanzu haka tana gudanar da ayyukanta da malamai 11, kuma tana da ɗalibai sama da 390 a matakan digiri, mastas, da PhD.
Makarantar Petroleum and Petrochemical Engineering
An buɗa wannan makarantar ne a watan March na shekarar 2009 tare da halartar ministan man fetur a gini mai girman murabba’in mita 3000, wanda ya ƙunshi azuzuwa 12, ɗakunan gwaje-gwaje guda 8, da zauren taro mai ɗaukar mutum 206. A watan Oktobar 2009, makarantar ta fara aiki ta hanyar karɓar ɗalibai a fannin Petroleum Engineering (exploitation) da Chemical Engineering, a matakin digiri. Zuwa yanzu tana da ɗalibai 508 da malamai 10.
Laburaren Jami’a
An samar da ita ne tun bayan assasa jami’ar kuma sannu a hankali cikin ‘yan shekarun nan saboda ƙaruwar da aka samu a fannonin karatu a matakai daban-daban musamman kwasa-kwasan karatun ƙarin ilimi, an ƙara yawan kayan da ke cikinta, ta yadda a halin yanzu tana ɗauke da sama da kwafin litattafai 82,000 a cikin harsunan farsi da larabci, guda 16,000 a rubutun latin, da kuma wallafe-wallafe 320 na latin da farsi. Laburaren yana aiwatar da ayyuka na yabawa ga ɗalibai, malamai, da sauran ma’aikatan jami’ar.
Abubuwan more rayuwa na ɗalibai
Rufaffen swimming pool, wurin gina jiki, filin wasa mai grass carpet, zauren mabambantan wasanni, rukunan hostel guda 2 ɗauke da hostel 8 wanda za su iya ɗauke ɗalibai 3500, cibiyar bada magani da shawarwari, gidan al’adu na ɗalibai, babban zauren cin abinci mai ɗaukar mutum 2000, da zakin taro mai ɗaukar mutum 360.
Ayyukan al’adu na ƙungiyoyin ɗalibai, wanda zuwa yanzu sun gudanarda shirye-shirye 460 na al’adu da na ilimi ga ɗalibai, kuma suna da membobi 2050 daga ɗalibai a ƙungiyoyin na al’adu, kimiyya, da wasanni a cikin ƙungoyoyi 74.
A halin yanzu, an buga litattafan ɗalibai guda 27 a cikin jami’ar. Ya kamata a san cewa jami’ar Hakim Sabzevari ko yaushe tana samun matsayi na farko-farko musamman a ‘yan shekarunnan a fannin ƙungiyoyin kimiyya na ɗalibai saboda yanayi mai kyau da mas’ulanta suka samarwa ɗalibai.
Wannan jami’ar na da hostel 11 ga ɗaliban da ba ‘yan gari ba, 3 daga ciki na maza ne, 8 kuma na mata,
Yanayin Wuri
Jami’ar Hakim Sabzevari na nan a unguwar Shahrake Tauhid a Khorasan Razavi, garin Sabzevar. Wannan cibiyar na ɗaya daga cikin jami’o’i uku da manyan cibiyoyin ilimi na unguwar Shahrak Tauhid, Razavi Khorasan, garin Sabzevar.
Adireshi: Lardin Khorasan Razavi, garin Sabzevar, titin Shohadae Hastei
Shafin jami’a: https://www.hsu.ac.ir