Garin Shahrekord shi ne babban birni ko cibiya ta lardin Chaharmahalo Bakhtiyari. Daga cikin muhimman jami’o’in da ke wannan gari akwai Jami’ar Shahrekord. A wannan rubutun mun tattara muku bayanai a kan yanayin karatu a wannan gari na Shahrekord.
Shahrekord
Wannan garin yana tsakanin digiri 50 mintuna 49 da sakanni 22 zuwa digiri 50 mintuna 53 da sakanni 44 longitude, da kuma tsakanin digiri 18 mintuna 22 da sakanni 23 zuwa digiri 23 mintuna 21 da sakanni 50 latitude, nisan kilomita 85 daga kudu maso gabacin garin Isfahan. Har ila yau, garin na yankin arewacin duwatsun Zagros. Garin na da tsayin mita 2050 zuwa 2310 daga tsoron saman teku, shi ne cibiyar lardi mafi tsayi a Iran.
Hakazalika garin na da madaidaicin yanayi, babu tsananin zafi amma akwai sanyi sosai a lokacin hunturu. Matsakaicin awon yanayi na shekara a wannan garin shi ne digiri 11.5 na centigrade. A tsawon shekaru 30 da suka wuce mafi ƙarancin darajar yanayi da aka shigar na wannan gari shi ne digiri 32 mafi yawa kuma digiri 42 na centigrade. Wata mafi sanyi a wannan gari shi ne watan ‘Dey’, mafi zafi kuma watan ‘Mordad’. Kodayake a lokacin sanyi danshin iskar garin yana ɗan yin yawa, ba’a samun wadataccen ruwan sama a watannin shuka (noma) in bacin watan ‘Ordibehesht’ da ‘Farvardin’.
Masana’antu da tattalin arziki
Tattalin arzikin garin na cikin gida ya ginu ne a kan saƙar carpet, ƙera makulli, saƙar takalmi, saƙar shimfiɗa, da kuma dafa tukane wanda waɗannan sana’o’in sun ragu yanzu sakamakon sauyin zamani. A halin yanzu akwai manyan masana’antu da muhimman kamfanoni a kusa da wannan gari inda yawancin ma’aikatan wuraren mazauna garin ne ko mazauna garuruwan kewaye da shi. Daga cikin kamfanonin akwai:
- Zagros Steel
- Barfab Household Appliances
- Faradaneh Aquatic Feed Production Factory
- Aquatic Feed Production Factory
- Fidar Patira
- Shahrekord Cement
- Carbonic Gas
- Shahrakian Hijab Textile
- Shahrakian Milk and Dairy Industries
- Barfab Factory
Zirga-Zirga
Bus ta gari
Hukumar kula da jigilar mutane da sufuri ta Shahrdarie Shahrekord ta yi tanadin motocin bus kusan guda 154 masu zuwa ko’ina cikin garin don amfanin mutanen gari.
Taxi
Baya ga tsarin kiran taxi daga nesa guda 2 waɗanda ke haɗe da babban tsari na ƙasa (133) da (1800), akwai kimanin motar taxi 1,500 masu zaman kansu, motocin taxi na musamman (irin motocin taxi na filin jirgi da na tashar mota) masu jigilar fasinjoji a wannan gari.
Filin jirgin Shohada na garin Shahrekord
Filin jirgin ƙasa da ƙasa na garin Shahrekord ɗaya ne daga cikin filayen jirgi mafi tudu da ake da su a ƙasar Iran, yana nan a babbar hanyar Shahrekord-Farsan. An fara aiki da wannan filin jirgi a shekarar 1999. A kowane sati akwai jirage masu zuwa garin Tehran da Mashhad daga filin jirgin.
Tashar mota
Akwai tashoshi biyu na fasinja a wannan gari domin sauƙaƙe wa fasinjoji ɗawainiya, daga ciki akwai tashar fasinja ta Azadi wadda ita ce babba kuma ita ta fi taka rawa wurin jigilar fasinjoji zuwa garuruwa daban-daban na ƙasar Iran.
- Tashar Payane Azadi (zuwa garuruwa daban-daban da yammacin lardin Chaharmahal)
- Tashar Terminale Gharb (zuwa garuruwan yammacin lardin)
Layin dogo
Zuwa yanzu dai wannan gari na Shahrekord ba ya da hanyar jirgin ƙasa, amma ana kan aikin gina hanyar jirgin ƙasa wadda za ta sada garin da layin dogo na ƙasar Iran. An fara aikin gina hanyar jirgin ƙasan a shekarar 2022 kuma ana kan aikin yanzu haka. A cewar masu kula da aikin, idan yanayi ya bada za a kammala aikin kuma a buɗe hanyar jirgin ƙasan zuwa ƙarshen shekarar 2023.
Wuraren tarihi da yawon buɗe ido
Garin na da iska mai sanyi-sanyi a lokacin zafi, wannan ya sa garin Shahrekord na samun baƙi masu yawon buɗe ido sosai a lokacin zafi, masu zuwa wurare kamar park ɗin Kuhestane Mellat, park laleh, chahar bagh, da park talijan.
Daga cikin wuraren tarihi na garin Shahrekord kuma akwai hubbaren Imamzadegan Dokhatun, Hamam Khan, Ghal’e Chaleshtar, Otaq A’ineh Shahrekord, Gidan tarihi na Bastanshenasi, Masallacin Atabkan, Babban Masallaci, Masallcin Abu Muhammad, Bazarche Haj Ahmad, Tappe Sarab, da Gorgari Tappe.
Laburarukan gari
- Laburaren gari na Molavi
- Laburaren gari na Hafez
- Laburaren gari na Rudaki (na makafi)
- Laburaren gari na Imam Khomeini
- Laburaren gari na Amirkabir
- Laburaren Ayatollah Dahkordi
- Laburaren gari na Shohada
Wuraren addini
- Imamzadegan Halime da Hakime Khatoun (tsakiyar gari)
- Imamzadeh Sayyed Muhammad Sabzpoush (yammacin gari)
- Imamzadeh Shahzadeh Azizullah Shahrakiyan (kudancin gari)
- Mosallae Imam Khomeini
- Masallacin Atabkan (Imam Sadiq)
- Sagha Khane Arbab Mirza
- Masjid Jame
- Masallacin Abu Muhammad
Ingantattun cibiyoyin koyarwa da jami’o’i
- Jami’ar Shahrekord
- Shahrekord University of Medical Sciences
Karatu a garin Shahrekord
Kasantuwar cewa akwai amintattun jami’o’i da yanayi mai daɗi a garin na Shahrekord, ga kuma sauƙin farashin rayuwa a garin, akwai ɗalibai da yawa masu sha’awar yin karatu a garin.
A duka lardin Chaharmahalo Bakhtiyari akwai jimillar cibiyoyin ilimi da jami’o’i guda 17. Jami’o’in lardin sun keɓantu da wallafa mujallu 15 na musamman na ilimi sannan kuma zuwa yanzu sun wallafa mujallu guda 311. Lardin na Chaharmahal ya karɓi baƙuncin tarukan ilimi 33 na musamman, gami da tarukan lacca guda 5. Researchers (masu bincike) na jami’o’i da cibiyoyin ilimi na wannan lardi sun wallafa maƙalolin ilimi guda 25638 waɗanda a ciki akwai maƙalolin mujalla guda 5467, maƙalolin tarukan kimiyya na cikin gida 11424, da maƙaloli 5467 a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2018 an samu kimanin ɗalibai 21,633 masu karatu a jami’o’in wannan lardi, hakazalika an samu jimillar malamai da ma’aikata membobin tsangayar ilimi guda 864 a lokacin.