Jagorantar ɗaliban waje a wurin zaɓen jami’ar da ta dace da su a ƙasar Iran ɗaya ne daga cikin abubuwan da ma’aikatanmu suka ba wa muhimmanci a kamfanin Tolo Safiran Noor. Muna ƙoƙarin ganin cewa an zaɓi jami’a daidai da ma’aunan da ɗalibai ke dubawa. Akwai yiwuwar cewa ma’aunan su bambanta tsakanin ɗalibai, amma ma’aunai mafi muhimmanci na iya zama yanayin iskar garin da za ayi karatun, kuɗin makaranta a wannan jami’ar, ko matsayin jami’ar a tsarurrukan ranking na duniya. Muna tare da ku domin yi muku jagora wajen zaɓen jami’ar da ta dace da ku.
Ga jagoran ɗaliban waje wurin zaɓen jami’a a ƙasar Iran kamar haka
Sharuɗan zaɓen jami’a da gabatar da manyan jami’o’in ƙasar Iran:
- Yanayin iska da abubuwan kallo na garin karatu
- Kuɗin makaranta
- Manyan jami’o’in Iran
Yanayin iska da abubuwan kallo na garin karatu
Dayawan ɗalibai kan nemi shaƙatawa bayan karatunsu. Saboda haka yanayin wuri ɗaya ne daga cikin sharuɗan zaɓen makaranta. Ƙasar Iran na da yanayi iri huɗu; hakan na nufin ƙasar na da wuraren yawon buɗe ido masu yawa. A arewacin ƙasar akwai jami’o’i irin su Jami’ar Babol Noshirvani da Jami’ar Mazandaran. Yankin arewacin ƙasar na da madaidaicin yanayi da ɗanyun dazuzzuka.
Garin Tehran ne cibiyar ƙasar Iran. A cikinsa akwai manyan jami’o’i masu matsayi a tsarukan ranking na duniya kamar Jami’ar Tehran, Jami’ar Fasaha ta Shahid Beheshti, Jami’ar Kimiyya da Fasaha, Amirkabir, Tarbiat Modarres, da sauransu waɗanda sun taka babban matsayi na ilimi. Garin Tehran na da wuraren shaƙatawa da na gani. Akwai manyan kasuwanni da cibiyoyin kasuwanci.
A tsakiyar ƙasar Iran akwai wuraren gani na tarihi masu kyau. Akwai Jami’o’in Bu-Ali Sina, Shiraz, Isfahan, Semnan, da sauransu. Hakazalika akwai gaɓar tekun Oman da tekun Farisa a kudancin ƙasar, kuma akwai jami’ar Shahid Chamran da jami’ar likitanci ta Jundi Shapur a yankin.
Kuɗin makaranta
Ana sanya kuɗin makaranta bisa la’akari da matsayin jami’a na ilimi da ayyukanta. Jami’o’in ƙasar Iran na cikin jami’o’i masu arha idan an kwatanta matsayinsu na ilimi da irin ayyukansu. Ɗalibai na la’akari da kuɗin makaranta idan za su zaɓi jami’a. A wannan babin kuma, manyan jami’o’i sun fi yawan kuɗin makaranta.
Manyan jami’o’in Iran
Kodayake ranking ɗin jami’a ba shi ne ma’aunin haƙiƙa na gane matsayinta na ilimi ba. Wannan ne ya sanya aka samar da wasu tsarukan ranking na musamman irinsu:
Tsarin ranking na Shanghai: Shugaban ƙasar China na lokacin ya damu sosai a kan ayyukan jami’o’in ƙasa da ƙasa, wannan ne ya sanya aka samar da tsarin Shanghai a shekarar 1998. Daga lokacin aka riƙa sabunta natijojin binciken wannan tsarin a kowace shekara. Ma’aunan da ake amfani da su a wanna tsarin sun haɗa da; ingancin karatu, ingancin membobin tsangayar ilimi, natijojin ayyukan bincike, da kuma yanayin aikin jami’a a dunƙule. Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tsarin ranking na TIMES: Ɗaya ne daga cikin tsarukan ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin ilimi na duniya wanda ya fara aiki a shekarar 2004. Shi kuma wannan tsarin na aiki da ma’aunai kamar haka; karatu (harabar karatu), bincike (yawan, kuɗin shiga, da shuhura), sanadodi (tasirin ayyukan bincike), kuɗin shiga daga masana’antu (ƙirƙira), da kuma kimar jami’a a idon duniya (ma’aikatanta, ɗalibanta, da ayyukanta na research). Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tsarin ranking na QS: Shi ma wani tsarin ranking ne wanda ya fara aiki a matsayin haɗin gwiwa da tsarin TIMES daga shekarar 2004 zuwa 2009. Daga bisani ya ci gaba aiki a ƙashin kansa. Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tsarin ranking na ISC: Ya fara aiki ne a shekarar 2010. Wannan tsarin ya bada ƙarfi wurin ranking ɗin jami’o’i da cibiyoyin ilimi da ke ƙasashen musulunci ne. Shi kuma wannan tsarin ma’aunansa sun haɗa da; bincike (ingancin bincike, tasirin bincike, rijistar haruffa, yawa, yawan mujallun da aka wallafa, yawan littafan da membobin tsangayar ilimi suka wallafa, yawan tsare-tsare da yarjejeniyoyin bincike), karatu (membobin tsangayar ilimi da aka karrama, maƙaloli masu citations da yawa, alaƙar membobin tsangayar ilimi masu PhD da sauran membobi, graduates da suka samu karramawa, alaƙar membobin tsangayar ilimi masu matsayi da sauran membobi, alaƙar membobin tsangayar ilimi da ɗalibai, alaƙar tsakanin ɗaliban postgraduate da sauran ɗalibai, ɗalibai masu lambar yabo a wasannin olympics na duniya), kima a idon duniya (alaƙar tsakanin ɗaliban waje da sauran ɗaliban makarantar, alaƙar membobin tsangayar ilimi da suka yi karatun PhD a ƙasar waje da sauran membobi masu PhD, yawan tarukan ƙasa da ƙasa, musharaka a ayyukan ƙasa da ƙasa, yawan musharakar jami’a a wallafa maƙalolin ƙasa da ƙasa), kayan aiki _ walwala (jimillar yawan taken littafai idan an kwatanta da yawan ɗalibai, yawan cibiyoyi da ƙungiyoyin da sansanonin bincike), ayyuka wa al’umma, tattalin arziki da masana’antu (yawan ƙungiyoyi da kamfanoni, yawan cibiyoyin bunƙasawa, yawan cibiyoyi masu dogaro da ilimi). Domin samun bayanai a kan ranking ɗin jami’o’in ƙasar Iran a tsarin Shanghai ku sauke wannan fayil.
Tehran University: Watakila ku buƙaci sanin abubuwan da ake buƙata domin karatu a jami’ar Tehran. Tambayoyi kamar: Yawan kuɗin makaranta, kwasa-kwasan karatu, matakan karatu, kuɗin hostel ko masauki a Tehran, da sauransu. Domin samun bayanan da kuke buƙata a kan wannan jami’a, ku ziyarci rubutunmu mai take Karatu a University of Tehran.
Sharif University of Technology: Mutane na buƙatar wasu bayanai domin yin zaɓin da ya dace da su. Taken wannan rubutun shi ne Karatu a Sharif University of Technology, wanda a ciki mun yi ƙoƙarin gabatar da jami’ar da matakinta na ilimi da sauran bayanan da suka shafe ta. Domin samun cikakken bayani, ku garzaya ku karanta rubutunmu mai suna Karatu a Sharif University of Technology.
Tarbiat Modare University: Jami’ar Tarbiat Modares ita kaɗai ce jami’ar karatun postgraduate zalla a ƙasar Iran kuma a garin Tehran take. Ku ziyarci wannan rubutu domin samun bayanai game da karatu a wannan jami’a; Karatu a Tarbiat Modares University.
Amirkabir University of Technology: Ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in ƙasar Iran. A wannan rubutu mun yi nufin muku bayanai game da sharuɗa da yanayin karatu a wannan jami’a domin sauƙaƙe muku wurin yin zaɓinku. Ku karanta wannan maƙala ta Karatu a Tarbiat Modares University domin samun cikakken bayani.
Shiraz University: Mutane na zuwa ƙasar Iran domin su yi karatu. Jami’ar Shiraz jami’ar gwamnati ce kuma jami’a ce mai tarihi kuma ta farko-farko a matakin ƙasa da ƙasa, a garin Shiraz. Jami’ar na karɓar adadi mai yawa na ɗaliban ƙasar waje daga ƙasashe daban-daban na duniya ciki har da ɗaliban ƙasar Iraq. Saboda haka karanta wannan rubutun na da muhimmanci ga ɗaliban da ke sha’awar yin karatu a jami’ar Shiraz. Ku karanta wannan rubutun domin samun cikakken bayani game da karatu a jami’ar Shiraz. Karatu a Shiraz University.
Iran University of Science and Technology: A wannan maƙala za mu yi muku bayani game Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Iran, za mu yi ƙoƙarin yin bayani a kan yanayin karatu a wannan jami’a da sharuɗanta na karɓar ɗalibai. Ku ziyarci wannan rubutun domin samun cikakken bayani game da jami’ar. Karatu a Iran University of Science and Technology.
University of Tabriz: Garin Tabriz (gari na uku mafi girma a Iran) na nan a arewa maso yammacin ƙasar Iran kuma shi ne cibiyar lardin Azarbaijan Sharqi. A garin ne jami’ar Tabriz take wadda ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in ƙasar Iran. Ku garzaya ku karanta rubutunmu mai suna Karatu a University of Tabriz domin samun cikakken bayani.
Ferdowsi University of Mashhad: Zaɓen jami’a na daga cikin ayyuka masu wahala da ɗalibai ke cin karo da su. Zaɓen jami’a ya kasance al’amari mafi muhimmanci ga ɗalibai. Sanin kowa ne makaranta kan iya canza rayuwar mutum. A wannan rubutu, za mu kawo muku bayani a kan janibobi daban-daban na karatu a Ferdowsi University kamar makarantunta, kwasa-kwasanta, kayan aikinta, da sauransu domin sauƙaƙe muku yin zaɓi mai kyau don ci gaba da karatunku. Ku karanta rubutunmu mai take Karatu a Ferdowsi University of Mashhad domin samun cikakken bayani.
_ Babol Noshirvani University of Technology: Idan kuna da sha’awar yin karatu a ƙasar Iran amma kuma suna shakka saboda tsadar kuɗin makaratnta, wannan jami’a zaɓi ne da ya kamata su yi la’akari da shi. Jami’ar ta Babol Noshirvani wadda aka mayar jami’ar fasaha ɗaya ce daga cikin jami’o’in fasaha na Iran masu daraja ta ɗaya a ƙasar. Har ila yau jami’ar na daga cikin jami’o’i da ke kiyaye sharuɗan karatu ɗari bisa ɗari. Za mu kawo muku ƙarin bayani game da jami’ar a cigaban rubutunmu. Domin samun cikakken bayani game da karatu a wannan jami’ar ku ziyarci rubutunmu mai take Karatu a Babol Noshirvani University of Technology.
_ University of Kashan: Jami’ar Kashan ita ce jami’a ta farko kuma jami’a mafi girma a Kashan na lardin Isfahan. Domin samun ƙarin bayani game da karatu a wannan jami’a kuna iya ziyartar rubutunmu mai taken Karatu a Jami’ar Kashan.
_ Shahid Beheshti University: Wata daga cikin sanannun jami’o’in ƙasar Iran kuma mai babban matsayi a ilmance ita ce jami’ar Shahid Beheshti. Za ku samu cikakken bayani game da yanayin karatu da sharuɗan karɓar ɗalibai a jami’ar a rubutunmu na Karatu a Shahid Beheshti University.
_ Tehran University of Medical Science: Karatu a wannan jami’a (wadda ke garin Tehran) a matsayin ɗaya daga cikin jami’o’in gwamnati, wadda matsayinta a ilmance idan an kwatanta da sauran jami’o’i yana kwaɗaitar da mutane masu yawa zuwa bincike a kanta. Jami’ar na ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya, jinya da karatun likitanci. Ku karanta wannan rubutun domin samun cikakken bayani game da jami’ar Karatu a Tehran University of Medical Science.
_ Shahid Beheshti University of Medical Science: Bayani a kan wannan jami’a na da muhimmanci saboda yadda ɗalibai ke kwaɗayin karatu a cikinta saboda tasirin da zai yi a wurin gina rayuwarsu, bayani a kan tarihinta, kwasa-kwasanta, makarantunta da sauransu. Ku karanta rubutun Karatu a Shahid Beheshti University of Medical Science domin samun waɗannan bayanai.
_ Iran University of Medical Science: Ɗaya ce daga cikin jami’o’in likitanci na ƙasar Iran masu babban matsayi a ilmance. Domin samun bayani game da sharuɗan karɓar ɗalibai a wannan jami’a a matsayinta na ɗaya daga cikin zaƙwaƙuran jami’o’in ƙasar Iran, bayanai da suka shafi yanayin karatu a cikinta da sauran bayanai, ku karanta maƙalarmu ta Karatu a Iran University of Medical Science.
_ Mazandaran University of Medical Science: Mazandaran lardi ne a arewacin ƙasar Iran wanda a cikinsa akwai wata jami’ar likitanci da ke garin Sari. Ku garzaya wannan maƙala ta Karatu a Mazandaran University of Medical Sciences domin samun bayanai a kan jami’ar.
_ Kurdistan University of Medical Science: Ita wannan jami’a cibiya ce ta koyarwa da ayyukan kiwon lafiya a garin Sanandaj lardin Kurdistan. Ku karanta rubutun Karatu a Kurdistan University of Medical Sciences domin samun bayanai a kan jami’ar.
_ Urmia University of Medical Sciences: Garin Urmia ne cibiyar lardin Azarbaijan Gharbi, a yankin arewa maso yammacin ƙasar Iran. Wannan jami’a ɗaya ce daga cikin jami’o’i da cibiyoyin ilimi da ke cikin garin. Ku karanta rubutun Karatu a Urmia University of Medical Sciences domin samun bayanai a kan jami’ar.
_ Kashan University of Medical Sciences: Tana ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya a garin Kashan. An gina makarantar likitanci ta Kashan University of Medical Sciences and Healthcare Services a fili mai girman murabba’in mita 22610. Bayanai game da jami’ar likitanci ta Kashan na da muhimmanci ga mutane. Ku karanta rubutunmu na Karatu a Kashan University of Medical Sciences domin samun waɗannan bayanan.
_ Mashhad University of Medical Sciences: Garin Mashhad ne cibiyar lalrdin Khorasan Razavi a arewa maso gabacin ƙasar Iran. Saboda haramin Imam Rida (a) da ke wannan gari, garin Mashhad ya kasance abun girmamawa ga musulmi tun zamanin bayan kuma a kowace shekara garin na karɓar baƙuncin ɗimbin baƙi da maziyarta. Hakazalika garin na da babban matsayi a ilmance da al’adance. Akwai ingantattun jami’o’i masu yawa a wannan gari, Mashhad University of Medical Science ɗaya ce daga cikinsu. Ku karanta rubutun Karatu a University of Medical Sciences domin samun ƙarin bayani.
Jami’o’in da muka ambata kaɗan ne daga cikin jami’o’in ƙasar Iran. Akwai sauran jami’o’i da yawa waɗanda suna da matsayi mai kyau a ilmance, sai dai ba za mu sami damar kawo dukansu a nan ba.
Wani abun da ya kamata ku lura da shi shi ne kuɗin zirga-zirga. Idan kuna son ku riƙa kai-komo zuwa ƙasarku, kila ku fifita zama a manyan garuguwa ko garuruwan da suka fi kusa da ƙasashenku.