Karatu a Qom University of Technology
Jami’ar fasaha ta Qom wato Qom University of Technology jami’a ce ta gwamnati da ke birnin Qom, a lardin Qom. Ta fara aiki da kwas biyu a shekarar 2008: kwas ɗin Industrial Engineering da Computer Engineering, bisa hadafin horar da ɗalibai masu himma. A halin yanzu a wannan jami’a ana koyar da kwas 23 a matakin digiri da na mastas, a kwalejoji uku mabambanta. Ku kasance tare da mu domin samun cikakken bayani game da karatu a wannan jami’a.
Gabatarwa
Jami’ar Fasaha ta Qom a taƙaice tana cikin birnin Qom mai tsarki. Tana ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin ilimin addini a ƙasar Iran da duniya baki ɗaya, kuma tana yaye manyan malaman addinin musulunci a makarantunta. Baya ga haka, birnin Qom na taka muhimmiyar rawa a wajen sadarwa tsakanin masana’antun Iran, tare da assasa garuruwa 7 tare da yankuna 4 na masana’antu. Hakazalika Qom na da arzikin ma’adanai wanda hakan ya ƙarƙafi bunƙasar cibiyoyin masana’antu da kasuwanci.
Saboda haka ne aka assasa wannan jami’a ta fasaha a Qom domin ƙarfafar masana’antun lardin da kuma horar da ƙwararrun ma’aikata. A halin yanzu tana da makarantu guda uku kamar haka: Kwalejin Electrical and Computer Engineering, Mechanical Engineering, da kuma kwalejin Technical Engineering. Jami’ar na aiki da ƙwararrun, tawagar gudanarwa, da haziƙan ɗalibai domin bunƙasa tattalin arziki a ilmance da kuma samar da ƙima.
Martabar Qom University of Technology
Ya kamata a lura cewa, jami’ar fasaha ta Qom tana daga cikin manyan jami’o’i a duniya saboda ingancin hanyoyinta na koyarwa. A cikin Iran, jami’ar ta samu kimantawa bisa la’akari da wasu ma’aunai irin su bincike, ayyukan koyarwa, kima a idon duniya, kayan aiki, da kuma ayyukan zamantakewa, tattalin arziki, da na masana’antu.
A tsarin ranking na ƙungiyar Islamic World Science Citation Center (ISC), jami’ar ta zo a matsayi na 17 a cikin jami’o’in masana’antu guda 29 na Iran a ɓangaren koyarwa, matsayi na 7 a daraja, matsayi na 25 a ayyukan bincike, matsayi na 24 a kayan aiki, sai kuma matsayi na 14 a ayyukan zamantakewa da tattalin arziki da na masana’antu.
Kuɗin Makarantar Qom University of Technology
Makarantu da Kwasa-Kwasai
Makarantar Electrical and Computer Engineering
- Bachelor’s Degree in Electrical Engineering (Communications, Control, Power)
- Bachelor’s Degree in Computer Engineering (Software, Computer Systems Architecture)
- Master’s Degree in Electrical Engineering (Control, Power Systems, Power Electronics and Electric Machines,
- Communication Systems, Electronic Circuits, Wave Field Communication)
- Master’s Degree in Computer Engineering (Software)
Makarantar Technical Engineering
- Bachelor’s Degree in Engineering Physics
- Bachelor’s Degree in Industrial Engineering
- Bachelor’s Degree in Mechanical Engineering
- Bachelor’s Degree in Civil Engineering
- Bachelor’s Degree in Polymer Engineering
- Bachelor’s Degree in Energy Engineering
- Bachelor’s Degree in Materials Engineering
- Master’s Degree in Organic Chemistry
- Master’s Degree in Applied Mathematics
- Master’s Degree in Industrial Engineering – Systems Optimization
- Master’s Degree in Environmental Civil Engineering
- Master’s Degree in Geotechnical Civil Engineering
- Master’s Degree in Mechanical Engineering – Applied Design
- Master’s Degree in Mechanical Engineering – Manufacturing
- Master’s Degree in Mechanical Engineering – Energy Conversion
- Master’s Degree in Polymer Engineering – Processing
- Doctorate in Mechanical Engineering – Applied Design
- Doctorate in Industrial Engineering – Systems Optimization
Makarantar Mechanical Engineering
- Bachelor’s Degree in Mechanical Engineering
- Bachelor’s Degree in Energy Engineering
Abubuwan More rayuwa
Wannan jami’a ba ta da girma sosai, tana da fadin mita murabba’in mita 31,800. A farko, sararin koyarwar ta ya kasance murabba’in mita 4,000, amma saboda ginin da sabuwar hukumar jami’ar ta yi, wannan sarari ya ƙaru da kashi 30%. Duk da haka, don bunƙasa jami’ar a shekarun da ke tafe da kuma jawo ɗalibai masu yawa, akwai buƙatar ƙarin kayan aiki masu inganci. Masu ruwa da tsaki suna fatan cewa ta hanyar shiryawa da gina babbar harabar jami’ar a kan fili mai girman hekata 24 da ke a kilomita 9 daga hanyar Qom-Tehran.
Jami’ar Qom University of Technology na da zauren wasanni mai suna ‘Shahid Shari’ati’, mai girman murabba’in mita 450. Hakazalika, ta karɓi hayar wani zauren wasanni a kusa da ita domin amfanin ɗalibanta. A watan September na shekarar 2020 ne jami’ar ta buɗe filin wasanninta mai grass carpet wanda girmansa zai kai murabba’in mita 1,250.
Wuraren Kwanan Ɗalibai
Jami’ar na da hostel guda uku na ɗalibai. Hostel na farko an ware shi ne domin ɗalibai maza ‘yan aji biyu zuwa uku, kuma yana cikin jami’ar. Sabbin ɗauka kuma suna da hostel a titin 15 Khordad, sai kuma hostel na uku wanda shi na mata ne, yana cikin jami’ar Mofid ta birnin Qom.
Yanayin Wuri
Jami’ar na nan a cikin birnin Qom a titin Khodakaram, kwana ta 30. A kusa da jami’ar akwai masallaci, cibiyar agajin gaggawa ta Qom, zauren wasanni, kwalejin electrical and computer engineering, da cibiyar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ta Rezvan. Akwai kuma wuraren cin abinci kamar Mahban Restaurant da Reyhoon Restaurant, inda nan ɗalibai ke zuwa cin abinci. Hakazalika akwai wuraren shan shayi a kusa da jami’ar kamar Omid Traditional Restaurant, da Prunus Cafe inda nan ma ɗalibai kan je domin hutawa.