[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Karatu a Qazvin

Karatu a Qazvin

Loading

Qazvin wani gari ne a shiyyoyin tsakiyar Iran kuma garin ya taɓa zama birnin tarayya na ƙasar Iran a baya. Karatu a garin Qazvin na da fa’idoji masu yawa kama daga yanayin iskar garin har zuwa abubuwan more rayuwa wanda za su sauƙaƙe wa ɗalibai karatu.

Karatu a Qazvin

Qazvin

Garin Qazvin ne cibiyar lardin Qazvin, mai tsayin mita 1,278 daga saman teku. Tarihi da asasin garin ya samo asali ne daga zamanin daular Sasaniyawa inda aka kafa shi bisa umarnin Shapour, wani sarki daga cikin sarakunan Sasaniyawa. Wannan gari ya kasance hanya ga attajirai masu safarar kaya daga gabas zuwa yamma.

Garin na Qazvin ya kasance cibiyar ƙasar Iran na tsawon shekaru 57 a lokacin mulkin Safawi, wannan ya sa garin ya samu wurare da gidajen tarihi masu tarin yawa. Hakazalika garin Qazvin ne cibiyar rubutun calligraphy a ƙasar Iran, kuma daga cikin ƙwararrun masu rubutun calligraphy a harshen farsi akwai Mir Imad Qazvini. Garin Qzvin shi ne na ɗaya wurin yawan abubuwan tarihi a Iran kuma na uku a duniya. Daga cikin abubuwan tarihi na Qazvin akwai; Qal’e Samiran, Karvansarae Sa’ad Al Saltaneh, Babban Masallacin Qazvin, Meimun Qal’e, Hammam Qajar, Tankin ruwa na Sardar, Peyghambarieh, Kakh Chehelsetun, Imamzadeh Husain, da titin Sapeh (titin da aka fara yi a ƙasar Iran).

Kasantuwar cewa garin na da kusan hekta 2,500 na lambu a kewaye da shi da kuma lambun Barajin mai girman hekta 1,400, an zaɓe shi a matsayin gari mafi tsaftar yanayi a shekarar 2013.

Karatu a Qazvin

Zirga-Zirga

Garin Qazvin na da keɓantaccen filin jirgi na ƙananan jirage da jirage na musamman kamar jiragen koyo da jiragen yawon buɗe ido. Hukumar kula da gari ta Qazvin (Shahrdari) ta saye filin jirgin a manufarta ta bunƙasa hanyoyin zirga-zirga na garin, sannan a ƙoƙarinta na inganta harkokin yawon buɗe ido (tourism)a garin Qazvin ta bunƙasa filin jirgin inda ta mayar da shi filin jirgin matafiya. A halin yanzu ƙananan jiragen matafiya (irin su: Fokker 100) na iya sauka a filin jirgin.

Shahardari na garin Qazvin na da tashoshin mota biyu a gabaci da yammacin garin. Tashar Terminale Azadegan mai girman murabba’in mita 27966 na ta gabas inda tsahar Terminale Gharb mai girman murabba’in mita 8328 ke yammacin garin Qazvin.

Bus

Ma’aikatar motocin bus da ke ƙarƙashin Shahardari na Qazvin ta na da tsarin tafiyarwa guda uku, tana da wurin tsayawar motoci da wurin gyara a Chaharrahe Vali Asr da kuma wurin tsayawar motoci na Shahid Rajaei. Akwai kimanin mutane 165000 masu amfani da motocin autobus da kimanin mutane 130000 masu amfani da motocin minibus na ma’aikatar Shahardari domin zirga-zirga a cikin garin Qazvin. Hakazalika akwai hanyoyin autobus 20 da motocin ke amfani da su, 15 daga cikin hanyoyin suna cikin gari sauran biyar kuma suna farkon gari inda wasunsu ke zuwa har cikin garuruwan Mohammadieh, Alvand, Eghbalieh, Mahmoud Abad, da garin Choobindar.

Taxi

An bude ma’aikatar tafiyarwa da kula da motocin taxi na garin Qazvin a shekarar 1997. Aikinta shi ne tsarawa da tafiyar da motocin taxi na wannan gari. Yanzu haka akwai motocin taxi sama da 6000 da ke aiki a garin Qazvin.

Wuraren shaƙatawa

Wuraren tarihi

Rukunin lambunan Safawi

Akwai wani gidan gwamnati na Safawi mai girman kimanin hekta 6 a tsakiyar garin Qazvin. Gidan gwamnatin na Safawi da ake kira da lambun al’adu ya fara ne daga ginin Ali Qapour na arewa ga titin Sepeh sannan ya haɗe da gidan Chehelsetun. Daga cikinsa ana iya ganin abubuwan tarihi da suka saura daga zamanin mabambantan dauloli (safawi, afsharieh, zendieh, da qajarieh), abubuwan tarihi irin su Sardar Ali Qapour, Bagh Ali Qapour, Emarat Saharbani, Shotrkhan, Grand Hotel, Grand Hotel Cinema, Peyghambarieh, Kakh Chehelsetun da Gidan Tarihin Qazvin.

Gidajen sarauta

Kasancewar garin Qazvin birnin tarayya a zamanin mulkin Safawiyawa da yawan sarakuna da yarimomi da aka yi cikinsa na mabambantan dauloli, akwai ragowar gine-ginen sarauta da fadoji da yawa a cikinsa. Gidan sarauta mafi shahara shi ne Fadar Chehelsetun wadda ita ce kawai fadar daular Safawi da ta yi saura. Asalin wannan fadar masauki ce inda ake sauke baƙin gidan sarauta. Sai gidan Shahardari wadda wasu Rashawa suka gina a shekarar 1927 kuma shi ne ginin farko na Shahardari a Iran. Sai gidan Bagh Sepehdar, gidan tarihi na Keshavarzi, gidan Sardar Mofkham wanda ake kira gidan al’ada na Amirkabir, gidan Shaharbani, da kuma Mimoun Qal’e wanda ɗaya ne daga cikin gidajen sarauta na Aali Biveh.

Gidajen tarihi

  • Gidan Behrouzi
  • Gidan Arif Qazvini
  • Gidan Yazdiha
  • Gidan Jalil Arazi
  • Gidan Daei
  • Gidan Darbandi
  • Gidan Ra’oufi
  • Gidan Zanjanchi
  • Gidan Saroukhani
  • Gidan Qa’emi
  • Gidan Moeini
  • Gidan Mohasses
  • Gidan Sa’ad Assultan
  • Gidan tarihi na Zaeim
  • Gida da Husainiyyar Aminiha
  • Gidan Sayyid Hosein Beheshti
  • Gidan Sayyid Mahmoud Beheshti

Ƙofofin gari

A zamanin baya garin Qazvin ya kasance yana da ƙofofi guda 8 kamar haka; ƙofar Rasht, ƙofar Bagh Shah, ƙofar Darab Koshak, ƙofar Tabriz, ƙofar tsohuwar Tehran, ƙofar Shaikh Abad, ƙofar Imam Hosein, da ƙofar Khandaqbar. A yanzu kuma ƙofofi biyu kawai suka rage; ƙofar Tehran da ƙofar Koshak.

Gidajen Wanka

Akwai wuraren wanka da yawa a garin Qazvin, wurare kamar; gidan wanka na Razavi, gidan wanka na Qajar, gidan wanka na Dodar, gidan wanka na Sayyedian, gidan wanka na Mirza Karim, gidan wanka na Haji Mahmoud Rahim Safa, gidan wanka na Balur, gidan wanka na Rah Rey, gidan wanka na Darughe, gidan wanka na Akhund Qazvin, gidan wanka na Pir Hassar, wanda suna daga cikin wuraren gani na garin Qazvin.

Karatu a Qazvin

Hubbare

  • Hubbaren Hammadullah Mostaufi
  • Hubbaren Shahid Salis
  • Burj Bar Ajin
  • Maƙabartar Sultan Vis
  • Maƙabartar Abbas Babayi

Cocuna

  • Cocin Kantur
  • Cocin Rafi

Wuraren kallo na ɗabi’a

  • Qal’e Mardomi
  • Ivan Sangi Niyaq
  • Yankin Bar Ajin
  • Varchor Waterfall
  • Ruwan ɗumi na Yaleh Gonbad
  • Qal’e Shoja Al-din
  • Qal’e Sultan Vis
  • Lambunan gargajiya na garin Qazvin
  • Kuhne Baghestan

Hotal Hotal da Masaukai

Mafi yawan hotal da masaukan baƙi na garin Qazvin suna titin Imam Khomeini ne ko kuma kusa da shi.

  • Marmar Hotel (farkon gari, ta gabas)
  • Behrouzi Hotel
  • Alborz Hotel (kusa da tsaliyar gari)
  • Iran Hotel (tsakiyar gari)
  • Taleghani Hotel (Khaksar)
  • Varzesh Hotel
  • Mir Emad Hotel
  • Iraniyan Hotel (wajen gari)
  • Safir Hotel (kusa da kasuwa)
  • Rajya Hotel
  • Minoo Hotel (Vali Asr junction)
  • Masaukin baƙi na Bagheri
  • Masaukin baƙi na Markazi
  • Masaukin baƙi na Bu-Ali
  • Masaukin baƙi na Golshen
  • Masaukin baƙi na Nasim Shomal

Karatu a Qazvin

Karatu a Qazvin

Kamar yadda muka ambata a bya, akwai wuraren gani da na tarihi birjik a wannan gari. Garin Qazvin yana da yanayi mai kyau Kasantuwarsa a hanyar sufuri ta gabas, yamma, kudu, da arewacin ƙasar Iran, da kusancinsa da garin Tehran da Karaj, da mallakar masana’antu da dama da kayan aiki na koyarwa da ya yi, da jami’o’in gwamnati irinsu Jami’ar Imam Khomeini, Jami’ar Kimiyyar Likitanci ta Qazvin, da Jami’ar Azad – Bar Ajin.

 

 

Related Posts
Leave a Reply