Lardin Lorestan na daga cikin lardukan yammacin ƙasar Iran. Lorestan yanki ne mai yawan tsaunuka wanda in bacin wasu ɗaiɗaikun filaye, duka yankin na kewaye da duwatsun Zagros. A kowace shekara ana samun ɗalibai da yawa masu sha’awar karatu a Lorestan. Mun yi ƙoƙarin tattara muku bayanan da suka danganci yanayin karatu a wannan Lardin na Lorestan.
Lorestan
Lorestan ne kaɗai lardin Iran wanda ya mamaye ɗayan sassa 4 na gidan tarihi na Melli na Iran saboda muhimmancinsa. Ga sassan huɗu kamar haka; kafin tarihi, tarihi da lorestan, zamanin musulunci, tambari da kuɗi. Lardin Lorestan shi ne lardi na uku mafi yawan ruwa a Iran inda ya ƙunshi kaso 12 cikin ɗari na duka ƙasar Iran. Kodayake lardin ba ya kan iyaka, amma ya haɗu da hasarori masu yawa a lokacin yaƙin Iran da Iraƙi.
Lardin na Lorestan ɗaya ne daga cikin larduka masu duwatsu a yammacin Iran. Duwatsun Zagros ne suka kewaye mafi yawancin yankin wannan lardin. Yanayin iskar lardin ya bambanta tsakanin yankunansa, ana iya ganin bambancin yanayi tsakanin yankin gabas da kudancin lardin. Ta arewa, lardin Lorestan na maƙwabtaka da lardin Hamadan da lardin Markazi, ta yamma kuma lardin Isfahan,ta kudu Khuzestan, ta yamma kuma lardin Kermanshah da Ilam. Hakazalika ta yankin gabas lardin Lorestan na da iyaka da lardin Chaharmahalo Bakhtiyari. Daga garin Tehran zuwa Lorestan nisan kilomita 36301 ne.
Zirga-Zirga
A shekarar 1925 ne jirgin sama ya fara sauka a wannan filin jirgin. Tun daga lokacin da aka yi juyin juya hali a shekarar 1979 jirage suka daina kai-komo a filin jirgin wasu lokutan ma akan rufe shi gabadaya. Hanyoyin jirgin sama da ke aiki a filin jirgin Khorram Abad su ne layin jirgi na Khorram Abad, filin jirgi na Mehr Abad, da layin jirgi na Khorram Abad, filin jirgin Shahid Hashemi Nejad Mashhad.
Kasantuwar cewa yankin na da yawan tsaunuka, layin jirgin ƙasan lardin yana daga cikin hanyoyin jirgin ƙasa mafi muhimmanci na ƙasar. Hanyar jirgin ƙasa ta lardin Lorestan na da tsayin kilomita 215 ɗauke da tashoshi 15. A kan hanyar akwai kwarkwaɗa (tunnel) guda 133, hakazalika hanyar ta rsatsa a gefen kogin Dez da kogin Sezar. An fara aikin gina hanyar jirgin ƙasa ta arewa zuwa kudu a shekarar 1927 inda aka kammala a 1938. Da farko layin jirgin ƙasa na lardin Lorestan ya kasance a ɓangaren kudu kafin a maida shi tsakanin tashar Durood da tashar Andimeshk a shekarar 1945.
Wuraren yawo
Abubuwan Tarihi
Lorestan na da babban matsayi a tarihi. Tarihinta ya kasu gida uku; kafin tarihi, tsohuwar Iran, da kuma lokacin musulunci. Mafi yawan abubuwan tarihi na Lorestan sun ƙunshi zane-zane, sassaƙaƙƙin koguna, kayan ƙasa, da abubuwan tagulla. Dalilin yawan tsaunukan wannan yankin, mutanen farko mazauna wurin sun fara zama ne a tsakiya da yammacin lardin. A lardin Lorestan akwai kogo sama da 250 waɗanda kusan rabinsu sun samu shiga cikin jerin abubuwan tarihi na ƙasar Iran.
Daga cikin muhimman kogunan lardin akwai kogunan Homian 1, Homian 2, Mirmalas, kogon Doushe Chegani na Khorram Abad, kogunan kafin tarihi na Khorram Abad irin su kogon Pasangar, kogon Qamari, kogon Kanji, kogon Gerarjneh, kogon Yafteh, kogon Bastani, kogon al’ajabi na Poldokhtar, kogon Tamandar, kogon Shahrood, da kogon Aligudarz.
Gadoji da Ganuwoyi
Har yanzu akwai sauran ganuwoyi da gadoji tun na zamanin Hakhamenshian da Sasanian. Daga ciki akwai gadojin Gavmishan, Poldokhtar, Kashkan, Shapuri, Kalhour, Sipelleh, Mamoulan, fadar Nasir, masaukin ayari na Chameshk, da fadar Falak Illafalak. Akwai maƙabartu da tsaunuka masu ɗimbin tarihi a yankuna da dama na lardin Lorestan waɗanda har yanzu binciken masana tarihi bai biyo ta kansu ba tukuna. Fadar Shapur Khuwast fada ce ta tarihi a tsakiyar garin Khorram Abad. Ana kiran fadar da sunan “Qal’e Davazdah Burji”. Fadar Shapur Khuwast na saman wani tudu da ke kallon garin Khorram Abad a kusa da kogin Khorram Abad, nan ne wurin yawon buɗe ido kuma wurin tarihi mafi jan hankali na garin Khorram Abad.
Gidan Bajul da Gidan Mandish da ke garin Aligudarz ma wasu ne daga cikin wuraren tarihi na wannan yanki. Daga cikin abubuwan tarihi masu jan hankali na garin Dorud kuma akwai tsohuwar gadar Chalanchulan. An aza tubalin gina gadar ne a zamanin Sasaniyawa inda aka bunƙasata a zamanin Safawiyawa. Wannan gadar an ginata ne a saman kogin Sezar kuma tsayinta ya kai mita 6 x 120, sannan tana da kusurwa 6 wanda tsayin kowace kusurwa zai kai mita 1.
Gadar Chalanchulan na da tududuwan karya taguwar ruwa ta gefen arewa maso yamma. Akwai katangogi masu tsayin santimita 90 da aka gina a gefe-gefen gadar domin kaucewa haɗarin faɗawar masu tsallakawa. Gadar na da rijista a cikin jerin abubuwan tarihi na ƙasar Iran. Tana da nisan kilomita 20 daga cikin garin Dorud.
Wuraren buɗe ido na ɗabi’a
Kasantuwar cewa lardin Lorestan na kewaye da duwatsun Zagros da yawan ruwan da ke yankin, akwai yanayi mai daɗi da ya yi daidai da masu yawon shaƙatawa da kuma wurare na ɗabi’a masu jan hankali. Lardin Lorestan na da yanayi kala 4 mabambanta kuma yana da sanannun yankuna guda 3. A lardin akwai duwatsu masu tsayi, mafaɗar ruwa, tafkuna, dazuzzuka masu faɗi, da sauransu waɗanda ke jan hankalin masu yawon buɗe ido. Daga cikin muhimman wuraren buɗe ido da wuraren ɗabi’a akwai:
- Yankin yawon buɗe ido na Goldasht, Borujerd
- Tafkin Gahar, Dorud
- Oshtorankuh
- Furannin Dalani, Aligudarz
- Park ɗin jeji na Shurab
- Yankin Goldasht
- Tafkin Keeyow
- Dausayin Poldokhtar
Karatun gaba da sakandare
- Kwalejin Technical and Engineering
Islamic Azad University Khorram Abad - Lorestan University of Medical Sciences
- Lorestan University
- Islamic Azad University Science and Research Campus Khorram Abad
- Islamic Azad University Khorram Abad
- Islamic Azad University Kuhdasht
- Islamic Azad University Aligudarz
- Islamic Azad University Poldokhtar
- Ayatollah Boroujerdi University
- Islamic Azad University Borujerd
- Islamic Azad University Science and Research Campus Borujerd
- Islamic Azad University Dorud
- Houzeh Ilmiyeh Kamalieh
- Islamic Azad University Rumeshkan
Karatu a Lorestan
Lardin Lorestan na da yanayi na ɗabi’a mai daɗi kuma mai kyau, hakazalika akwai jami’o’i biyu masu muhimmanci a lardin; Lorestan University da Lorestan University of Medical Sciences.
Akwai jimillar jami’o’i da cibiyoyin koyarwa guda 19 a lardin Lorestan. Jami’o’in sun keɓanta da wallafa mujallun musamman na ilimi guda 16, sun jimillar mujallu 136. Jami’o’in lardin Lorestan sun karɓi baƙuncin taruka 34 na kimiyya. Researchers (masu bincike) na jami’o’in wannan lardi sun wallafa maƙalolin kimiyya guda 29966, guda 6288 daga ciki maƙalolin mujalla ne sai kuma guda 17413 a tarukan cikin gida, sauran kuma a matakin ƙasa da ƙasa. A shekarar 2018 an samu jimillar ɗalibai 51,177 masu karatu a jami’o’in lardin lorestan tare da malamai 1,407.