Wannan rubutun ya shafi karatu a jami’o’i masu kyau kuma masu sauƙin kuɗi a Iran ga ɗaliban waje. A cigaban rubutun mun yi ƙoƙarin kawo waɗannan jami’o’i, hakan zai sauƙaƙe muku zaɓinku game da Karatu a Iran.
Karatu a jami’o’i masu sauƙin kuɗi a Iran
Fita waje karatu ɗaya ne daga cikin abubuwan da ke yin tasiri a goben mutum. Saboda muhimmancin hakan ne ya sa yana da kyau kafin mutum ya yi bincike sosai game da ƙasar da yake son zuwa karatu. Zamaninnan ƙasashe na fuskantar kai-komo na mutane masu yawa tsakaninsu saboda mabambantan dalilai da suka haɗa da karatu, aiki, samun walwala, ko kuma gudun hijira saboda yaƙi ko matsalolin siyasa, da dai sauransu.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi karatu shi ne zaɓen makaranta wanda hakan na iya dogara da yanayin tsadar makarantar. Ana sanar da kuɗin makaranta ga ɗaliban waje kamar yadda makarantun suka saka. A cigaba, za mu kawo sunan jami’a tare da kuɗin makarantarta.
Al-Zahra University
An assasa Jami’ar Al-Zahra (AS) a shekarar 1952 a arewa maso yammacin garin Tehran bisa hadafin ilmantar da ɗalibai mata a matakin jami’a, inda bayan nasarar juyin juya hali na Iran jami’ar ta ci gaba da bunƙasa ta ɓangarori daban-daban. Manufar assasa jami’ar ita ce tarbiyantar da mata a ilmance da al’adance waɗanda bayan kula da iyali, za su iya taka rawa a ɓangare zamantakewar al’umma, siyasa, al’adu, da tattalin arzikin ƙasa. Yanzu haka a jami’ar akwai ɗalibai 0279 masu karatu a ƙarƙashin kulawar ma’aikatan tsangayar ilimi 129 a sassan koyarwa 33 ɗauke da kwasa-kwasai 33 a matakan digiri, masters, da PhD a cikin makarantu 33. Kusan kashi 2 bisa 3 na malaman wannan jami’a mata ne. Kashi 31% daga cikin membobin tsangayar ilimi sun kai matakin professor, kashi 11% na matakin associate professor, sai kashi 19 masu assistant professor. A kowace shekara ana wallafa dubban maƙaloli da gomman littafai daga ayyukan bincike na ɗalibai da malaman jami’ar a matakin cikin gida da matakin ƙasa da ƙasa. Jami’ar Al Zahra na daga cikin jami’o’i masu sauƙin kuɗi a Iran kuma tana da kayan aiki na koyarwa, bincike, al’adu, da wasanni a cikin farfajiyarta mai kyau, mai girman fiye da hekta 33 a cikin Tehran da reshenta na garin Urmia. Jami’ar ta tanadi duka irin kayan aikin da ake buƙata domin bunƙasa ilimin ɗalibanta.
University of Birjand
Jami’ar Birjand ita ce ginshiƙin ilimi da karatu a gabacin ƙasar Iran, kuma ita ce cibiyar koyarwa mafi daɗewa a lardin Khorasan Junubi, tana da tarihin sama da shekaru 46 a fannin karatu, al’adu da zamantakewa.inda ta horar da ƙwararrun ma’aikata 30,000. Jami’ar ta cika duka sharuɗan da ya kamata ace jami’a na da su kuma tana da tsayayyun membobin kwamitin amintattu da kwamitin bincike na musamman. Jami’ar Birjand na da kimanin ɗalibai 13,000 a masu karatun kwasa-kwasai 340 a matakan associate degree, B.Sc, M.Sc, da PhD. Ɗaliban da ke karatu a matakin postgraduate a wannan jami’ar za su kai kashi 30 bisa ɗari na duka ɗaliban jami’ar. Jami’ar na da ma’aikatan tsangayar ilimi guda 350 kuma tana ɗaya daga cikin jami’o’i masu sauƙin kuɗi a lardin Khorasan Junubi na ƙasar Iran. Jami’ar na da ma’aikata 350 a ɓangarori daban-daban na jami’ar irinsu ofisoshi, ayyukan da suka shafi karatun ɗalibai, walwalar ɗalibai, da sauran sassa. Jami’ar na da kwalejoji 11 a harabobi 3 na Shokat Abad, Amir Abad, da Shohada. Makarantun sun haɗa da; Kwalejin Science, Agriculture, Engineering, Literature and Human Science, Art, Sport Science, Educational Sciences and Psychology, Mathematical Sciences and Statistics, Natural Resources and Enviroment, Kwalejin Electrical and Computer, da kwalejin Technical.
Ahlul Bayt International University
An assasa jami’ar “Ahlul Bayt (AS) International University” a shekarar 2004 bisa hadafin taimakawa wajen bunƙasa ilimi da samar da abubuwan buƙatun ilimi da na bincike domin amfanin ɗalibai da masu bincike musulmai da kuma taimakawa wajen sanin al’adu da wayewar musulunci, a matakan karatu na postgraduate a wani ƙaramin muhalli kafin ta koma cikakkiyar jami’a a shekarar 2011. Jami’ar na nan a wani kyakkyawan muhalli a garin Tehran wato babban birin tarayya na ƙasar Iran, kuma tana da ƙwararrun ma’aikatan tsangayar ilimi a mabambantan kwasa-kwasai, sannan tana daga cikin jami’o’i masu sauƙin kuɗi a Iran ɗauke da ɗalibai masu yawa daga mabambantan ƙasashe kuma har yanzu tana da shauƙin karɓar ɗalibai daga ko’ina a faɗin duniya. Hakazalika wannan jami’a na alfahari da cewa tana cikin ƙungiyar jami’o’in ƙasa da ƙasa a ƙarƙashin ma’aikatar UNESCO sannan baya ga karatu, a kowace shekara tana karɓar baƙuncin malamai da masu bincike domin samar da damar bincike a sassa daban-daban na duniya.
Persian Gulf University
Jami’ar Khalije Fars jami’ar gwamnati ce da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi da binciken ta Iran, ita ce cibiyar koyarwa mafi girma a lardin Bushehr kuma tana cikin garin Bushehr ne. Jami’ar ta fara aiki ne da sunan “Jami’ar Bushehr” da kwasa-kwasai biyu kacal na Civil Engineering da Mechanical Engineering a shekarar 1992. Jami’ar Khalije Fars na da cibiyoyin bincike guda 9 da kwaleji guda 8 kamar haka; kwalejin literature and human science, kwalejin business, nanoscience and technology, agriculture, engineering, smart systems engineering and data science, art and architecture, kwalejin petroleum engineering, gas and petrochemical, marine science and technology, da kwalejin mass engineering. Hakazalika jami’ar na da ofisoshin al’amuran koyarwa 5, al’adu da al’amuran ɗalibai, bincike da fasaha, tsari da bunƙasawa, da albarkatun ɗan’adam. Yanzu haka ana yin kwasa-kwasai 99 a jami’ar wanda daga cikinsu, 31 na digiri ne, 56 na masters, 13 kuma na PhD.
Sajjad University of Technology
Jami’ar Fasaha ta Sajjad ta fara ayyukanta na koyarwa ne a shekarar 1995 a garin Mashhad a matsayin cibiyar koyarwa ta gaba da sakandare bayan ta karɓi lasisi daga majalisar bunƙasa karatun gaba da sakandare da ke ma’aikatar ilimi da bincike. Binciken ma’aikatar ilimi ya nuna cewa a koyaushe wannan jami’ar ta kasance a sahun gaba a cikin jami’o’in da ba na gwamnati ba na ƙasar. Bayanan ƙididdiga na ma’aikatar SANJESH sun nuna cewa a shekaru 5 da suka gabata, an samu kimanin ɗalibai 3500 da suka ci jarabawar ƙasa ta zuwa matakin masters daga wannan jami’a, hakazalika akwai ɗaliban da aka yaye daga jami’ar fasaha ta Sajjad da yawa a sassa daban-daban na masana’antun ƙasar, wannan ma babbar nasara ce ga jami’ar.
Jami’ar Sajjad na gabatar da ayyukan koyarwa a duka sassan karatu na digiri, mastas, da PhD sannan binike ya nuna cewa bayan jami’ar Ferdowsi, wannan jami’a ta fi kowace jami’a a garin Mashhad yawan ɗalibai da ke shauƙin yin karatu a cikinta.Kwamitin assasa jami’ar ya ƙunshi malaman jami’a da wasu jiga-jigai daga masana’antun ƙasar Iran. Jami’ar Sajjad ita ce jami’ar farko a ƙasar Iran wadda aka samar daga cibiyar bincike ta masana’anta.
International University Of Chabahar
Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Chabahar ta fara aiki shekarar 2002 inda ta karɓi ɗalibai a kwasa-kwasai 8 tare da haɗin gwiwar jami’ar London, inda akan yi jarabawoyin ƙarshen shekara a jami’ar Chabahar amma jami’ar London ce ke bada shaidar kammala karatu, daga bisani jami’ar ta Chabahar ta damƙa ma ɗalibanta. A shekarar 2009 wannan jami’a ta fara karɓar ɗalibai ta hanyar jarabawar shiga jami’a ta ƙasa bayan ta bunƙasa yawan kwasa-kwasanta a matakan digiri. Yanzu haka a wannan jami’a ana yin kwasa-kwasai sama da guda ashirin a matakin digiri da mastas.
University of Neyshabur
Jami’ar Neyshabur na amfani da sabbin fasahar gudanarwa, fasahar koyarwa da bincike, ƙarfafawa, da jajircewar ma’aikatanta na tsangayar ilimi da sauran ma’aikata domin tarbiyyantar da ƙwararrun ma’aikata da ƴankasuwa, tare da bunƙasa ilimi da al’adun ƙasar. A halin yanzu jami’ar Neyshabur na da kwaleji guda huɗu; Art, Human Science, Basic Science, da kwalejin Technical and Engineering. Jimillar girman wannan jami’a ya haura murabba’in mita 15730.
Qom University of Technology
Jami’ar fasaha ta Qom ta fara aiki a shekarar 2008 da kwasa-kwasai 2 na Industrial Engineering da Computer Engineering da nufin horar da ɗalibai masu himma da addini. Yanzu jami’ar na da makarantu 3; Technical and Engineering, Electrical and Computer Engineering, da Basic Science kuma tana da kwasa-kwasai 23 a matakin digiri da mastas, tana da membobin tsangayar ilimi 57 da ɗalibai 2000 daga sassa daban-daban na Iran musamman daga lardin Tehran da Qom. Ana fatan cewa ɗaliban da suka yi karatu a wannan jami’a su shiga sahun ƙwararrun injiniyoyi da masana kimiyya na ƙasar. Hakazalika jami’ar na daga cikin jami’o’in fasaha da suka dace da ɗaliban waje, sannan tana cikin jami’o’i masu sauƙin kuɗi a Iran.
University of Bojnord
Jami’ar Bojnord jami’a ce ta gwamnati wadda aka assasa a garin Bojnord a shekarar 2005. Yanzu haka akwai ɗalibai sama da 12000 masu karatu a jami’ar. Ana kallon jami’ar a matsayin ita ce jami’ar asali ta Khorasan Junubi. Rahoton hulɗa da jama’a na jami’ar Bojnord ya bayyana cewa cibiyar bada shawara ga ɗalibai ta wannan jami’ar ta samu kyautar matsayi na farko karo na 4 a jere, a bukin tattara shugabanni da ma’aikatan cibiyoyin bada shawara na ƙasa.
Rahoton ya nuna cewa an gudanar da binciken ne a fannin ayyukan lafiyar ƙwaƙwalwa da zamantakewar ɗalibai a kwanakin corona a shekarar 2020, inda aka gabatar da lambar yabo ta musamman daga hukumar lafiya da ma’aikatar ilimi zuwa ga wannan cibiyar. Dukda cewa jami’ar ita ce ta ɗaya a lardin Khorasan Junubi, tana ɗaya daga cikin jami’o’i masu sauƙin kuɗi ga ɗaliban ƙasashen waje.
Jami’o’in da muka ambata suna daga cikin jami’o’in iran masu kyau waɗanda basu da tsada kuma suna karɓar ɗalibai daga mabambantan ƙasashe a kowace shekara. A kodayaushe kamfaninmu na ƙoƙarin ganin cewa ya tattara muku muhimman bayanai game da jami’o’in ƙasar Iran.