Imam Reza International University dake garin Mashhad, tana ƙarƙashin kulawar Astan Qods, wacce dalilin ingancin karatu da kayan aikin koyarwa da bincike ta samu nasarar jan hankalin ɗalibai da dama. A cikin wannan rubutun zamu mayarda hankali kan yadda karatu a Imam Reza University yake. Ku biyo mu domin samun bayani akan kuɗin makaranta da kuma yanayin ɗaukar dalibai a wannan jami’ar.
Gabatarwa
Ayatullahi Tabasi (Shugaban yankin Khorasan Razavi) shi ne ya assasa wannan jami’ar mai girman mita dubu uku (3000). Dalilin raba jinsi da akayi a wannan jami’ar, ɗalibai mata suna karatu ne a sashen Rezvan a inda ɗalibai maza suke karatu a sashen Asrar.
Jami’ar Imam Reza ta fara aiki ne a shekarar 1999. A wannan jami’a akwai kimanin ɗalibai 5900, malamai 52, mambobin kwamitin kimiyya 61 da suke a bakin aiki. Bincike ya nuna cewa an wallafa kimanin maƙalolin ilimi 2278 [413 مقاله ژورنالی و 1865 مقاله کنفرانسی]a taruka da wallafe-wallafen cikin gida, an kuma wallafa ingantattun maƙaloli 301 na ƙasa da ƙasa. A cikin wannan rubutun zamu maida hankali akan yadda karatu a Jami’ar Imam Reza yake.
Makarantu
_Makarantar Human Sciences
_Makarantar Engineering
_Makarantar Management and Accounting
_Makarantar Islamic Art and Architecture
Kwasa-Kwasan Imam Reza University
Ga kwasa-kwasan da akeyi a Imam Reza University kamar haka:
_Electrical Engineering
_Sports Science
_Counseling
_Financial Management
_Business Management
_Industrial Management
_Insurance Management
_Psychology
_Accounting
_Law
_Urban Design
-Computer Engineering
_English translation
_Audit
_Medical Engineering
_Sports Science
_Mechatronics Engineering
_Business Management
_Da sauransu
Domin samun cikakken list na kwasa-kwasan da akeyi a Imam Reza University da kuma matakin karatu da akeso, ku sauke wannan fayil na ƙasa.
Kwasa-kwasan Imam Reza University
Abubuwan alfahari na Imam Reza University
_Samun mataki na farko a martabar jami’o’i masu zaman kansu a ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta Iran
_Samun daraja ta ɗaya a tsakanin jami’o’i da makarantu masu zaman kansu a faɗin ƙasar, a tsarin martaba makarantu na ma’aikatar ilimi, bincike da fasaha ta Iran
_Wallafa da tarjama litattafai 58
_Kammala aiki 37 na bincike
_Samun martaba ta biyu a jami’o’i mawallafa na ƙasa
_Lashe martaba ta ɗaya da Agha Muhammad Sari’i yayi a ɓangaren wasan kwaikwayo na bukin yanki da Jami’ar Pak ta shirya karo na biyu
_Lashe martaba ta biyu a gasar ƙwallon hannu ta volleyball da tawagar jami’ar Imam Reza tayi a tsakankanin jami’o’i 13 na yankin
_Lashe martaba ta ɗaya a tsakankanin jami’o’i masu zaman kansu bisa ga tsarin ranking na CIVILICA (madogarar ilimi)
_Da sauransu
Kwas ɗin Karatu | Matakin Karatu | tsawon lokacin karatu | Kuɗin makaranta (na shekara) |
---|---|---|---|
Kwasa-kwasan Literature da Humanity | Digirin Farko (BSc) | Shekara 4 | Dala 400 |
Masters (MSc) | Shekara 2 | Dala 720 | |
Sauran kwasa-kwasai | Digirin Farko (BSc) | Shekara 4 | Dala 472 |
Masters (MSc) | Shekara 2 | Dala 842 |
Abubuwan more rayuwa
_Kayan aikin karatu da gwaje-gwaje Damar shiga shafukan intanet na cikin gida ta hanyar optical fibre da kuma amfani da intanet kyauta ga ɗalibai, ɗakin kwamfuta na amfanin kowa da kowa, kayan sauti da kallo a ɗakunan taro, samar da majigi da kwamfutoci a azuzuwan karatu, kayan aiki da suka shafi sadarwa, tsaron cibiyar sadarwa da microprocessors a ɗakunan gwaje-gwaje (labs), laburare da ɗakin karatu, da sauransu.
_Wurin kwanan ɗalibai: Wurin kwanan ɗalibai mata mai ɗaukar kimanin ɗalibai 300, wurin kwanan ɗalibai maza (musamman saboda ɗaliban ƙasashen waje) mai ɗaukar kimanin ɗalibai 70 (akwai motar makaranta domin kai-komon ɗalibai)
_Laburaren Astan Qods
_Ɗakin wasanni
_Da sauransu
Muhalli:
Jami’ar Imam Reza tana nan a unguwar Sanabad da ke garin Mashhad, titin Daneshga, lardin Khorasan Razavi. A zahiri, jami’ar tana kusa da muhimman wurare kamar wurin shaƙatawa na Serah Adabiat, Bag Melli, asibitin Doctor Shykh, Gol Narjis Zair Sarai da kuma asibitin Bint al-Hoda. Tashar jirgin ƙasa (metro mafi kusa) da jami’ar ita ce Tashar Sa’adi, tashar bas mafi kusa ita ce tsahar bas dake randabawul na Sa’adi wanda wannan ya sauƙaƙa zirga-zirga ga ma’aikatan da basuda ababen hawa na ƙashin kansu.
Cikakken adireshin Imam Reza University
Adireshi: Layin Daneshga 21/ Asrar, Titin Daneshga, garin Mashhad. (Sashen ɗalibai maza)
Randabawul na Falestin, Mashhad. (Sashen ɗalibai mata)
Tambayoyinda ake yawan yi dangane da karatu a Imam Reza University
- Shin ɗaliban ƙasar Iraƙi zasu iya karatu a Imam Reza University?
A’a, an cire wannan jami’a daga cikin jerin jami’o’in da ma’aikatar ilimi ta Iraƙi ta amince dasu. - Ya yanayin biyan kuɗin makaranta yake?
A wannan makaranta ana biyan kuɗin makaranta da Toman ne (kuɗin Iran) kuma a kowace shekara kuɗin makaranta suna ƙaruwa da kaso kusan 25 bisa 100.
[neshan-map id=”36″]