Yazd gari ne a tsakiyar ƙasar Iran kuma shi ne babban birnin lardin Yazd, sannan yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan ƙasar Iran, A cigaban rubutunmu za mu kawo muku bayanan da za su ishe ku sanin wannan gari na Yazd da kuma fa’idar da za ku samu idan kun yi karatu a Yazd.
Yazd
Garin Yazd ya shahara da ɗanyar ƙasa (laka) a duniya sannan shi ne garin tarihi na farko a ƙasar Iran hakazalika na 22 a jerin abubuwan al’ajabi na ƙasar Iran a list ɗin UNESCO. Garin na Yazd yana ɗaya daga cikin ginshiƙan likitanci da al’adu na ƙasar Iran. A wannan gari ne aka gina akwatin sirri na farko na duniya shekara 1700 da suka wuce.
Cigaban wannan gari na Yazd ya soma ne a ƙarni na takwas na hijiri zuwa yanzu, Atabkan na Yazd suna daga cikin abubuwan da suka sabbaba cigaban garin a ƙarnonin baya. A shigar da record ɗin saƙa na wannan gari a ranar 7 ga watan March na shekarar 2006 da lambar shigarwan 15000, a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan ƙasa na Iran. Garin ya sharara da sunaye kamar haka; darul ibadah, darul ilm, darul amal, garin kekuna, garin shirini, garin wuta, garin qunut, da sauran sunaye.
Zirga-Zirga
Filin Jirgi
FIlin jirgi na garin Yazd ya fara aiki a shekarar 2006 a wani wuri mai girman hekta 578 a kudancin hamadar tsakiyar ƙasar Iran, a yammacin garin da nisan kimanin kilomita 10 daga cikin gari. Tsayin hanyar jirgin ya kai mita 4100 faɗinsa kuma mita 60 (tare da mita 15 na shoulder). Filin jirgin yana a asalin mahaɗar sufurin arewa-kudu kuma ga hanyoyin jiragen ƙasa da ƙasa kamar haka; UL125, da UL124. Sai jiragen cikin gida (Iran) su kuma; R654, R663, da W5. Da yawan jiragen gida da na waje harda jiragen yaƙi suna bi ta sararin samaniyar wannan filin jirgin.
Baya ga jiragen da an riga an tsara kaikomonsu a wannan filin jirgi, jirage na iya amfani da shi idan yanayi na emergency ya taso.
Layin Dogo
Da yawan mutane suna da burin amfani da layin dogo (hanyar jirgin ƙasa) domin zirga-zirga ko yin sufurin kaya. Burin na mutanen lardin Yazd na amfani da jirgin ƙasa ya cika a watan June na shekarar 1971. Kodayake an fara aikin hanyar jirgin ƙasa na yankin kudu maso gabas a matsayin hanyar Qom – Zarand a shekarar 1938 kuma an kammala mafi yawan ayyukan gine-ginensa a lokacin, amma saboda al’amuran siyasa na ƙasar ba’a buɗe shi a lokacin ba sai shekarar 1971.
A daidai lokacin ɓullowar juyin juya hali na masana’antu da assasa masana’antar ƙarfe ta garin Isfahan, buƙatuwar amfani da ma’adanai da ƙarafa da duwatsu ta sanya shugabanni suka ƙara maida hankali ga aikin layin dogon har ya zama kammala shi ne hadafinsu na farko saboda muhimmancinsa a tattalin arzikin ƙasar. Injiniyoyi da ma’aikata na cikin ƙasar Iran ne suka aiwatar da dukkan ayyukan fasaha da taswirar a cikin ƙanƙanin lokaci.
Tashar Fasinja
An fara aikin gina tashar ne a wani muhalli mai girman hekta 57 a tsakanin hanyar Shahrake San’ati da titin Shahid Daheghan mallakin hukumar Shahrsazi, bayan cika duka sharuɗan mallaka a ranar 10 ga watan April na shekarar 1998, inda ta fara aiki a ranar 5 ga watan January na shekarar 2010 tare da rufe tsohuwar tashar. Girman gine-ginen tashar zaikai kusan murabba’in mita 14000 wanda ya ƙunshi filin tashar, ɗakuna, da sauransu.
Wuraren shaƙatawa da koren fili
Garin Yazd na da manyan park guda 12 (na gari) da kuma ƙanana guda 153 (na unguwanni). Daga cikin parks ɗin mafi shahara akwai:
- Kuhestan Park
- Shadi Park (akwai amusement park a ciki)
- Markar Park (babban park na garin)
- Ghadir Park
- Haft Tir Park
- Azadegan Park
Wurin shaƙatawa na Kuhestan (kuhestan park) ɗaya ne daga cikin koren wuraren shaƙatawa mafi kyawo wanda ake ƙoƙarin gina game sets, da gazebos a sashensa na biyu. Hakazalika an gina wani fountain mai suna ‘Musical Harmony’ a cikin park ɗin.
Cibiyoyin kimiyya, na karatu, da na al’adu
Kashi 99.9 cikin ɗari na lardin Yazd sun samu karatun sharar fage, kuma garin Yazd shi ne na farko a wannan zancen. A shekarar 2022, muatnen garin Yazd sun fi kowa cin jarabawar shiga ta “Konkur” kuma wannan shi ne karo na 29 a jere. A garin Yazd akwai cibiyoyin ilimi da yawa, ga kaɗan daga ciki:
- Yazd University
- Shahid Sadoughi University of Medical Sciences
- Meybod University
- University of Applied Sciences Yazd
- Yazd Farhangian University
- Yazd Province Technical and Vocational University
- Azad University Yazd
- Payam-e Noor University of Yazd
- University of Science and Arts of Yazd
- University of Science and Research
- Yazd Science and Technology Park
- Museum of Natural Sciences
- Makarantun Sakandare 2 na Barazande Moghaddam da Shahid Sadoughi
- Makarantun Malek Sabet da Darakhshande
- Makarantar Sakandare ta Imam Husain
- Mahnoor Cultural Complex
- Imam Ali Cultural Complex
- Javad Institute of Higher Education
- Mulla Sadra Institute of Higher Education
- Javadalaime Applied Science Center
- Makarantar Shahid Sadoughi
- Ashkazar Azad University
- Payam Noor University, Razvanshahr, Sadough
- Ardakan University
- Water Waves Swimming pool Rezvanshahr Sadough
Cibiyoyin lafiya
- Yazd Infertility Center
- Mortaz Hospital
- Shahid Sadoughi Burn Accident Hospital
- Superspecialized Gynecology, Obstetrics and Maternal Infertility Hospital
- Afshar Heart Specialized Hospital
- Shahid Rahmonun Hospital (Farkhi)
- Shahid Sadoughi Hospital
- Shohadaye Kargar Hospital
- Goudarz Hospital
- Sayyedal Shohada Hospital
- Mujibian Hospital
- Ramzanzadeh Radiotherapy and Chemotherapy Center
- Khatamal Anbiya Medical Center
- Baqaeipur Specialized and Subspecialty Clinic
- Herati Medical Center
- Shah Wali Hospital
Yawon buɗe ido
An sanya birnin Yazd a cikin jerin abubuwan tarihi na UNESCO a ranar 9 ga July, 2017, dalilin kyawawan gine-ginensa na tarihi waɗanda ba’a taɓa canza su ba.
Gine-Gine da wuraren tarihi
- Lambun Dolatabad Chaharmanar
- Rukunin Lambuna na Khan
Kasuwannin tarihi
- Kasuwar Khan
- Kasuwar Panjeh Ali
- Kasuwar Ghayseri
- Kasuwar Alaghbandi
- Kasuwar Kashigari
- Kasuwar Chitsazi
- Kasuwar masallacin Mulla Ismail
- Kasuwar Ifshar
- Kasuwar Haji Ghanbar
- Kasuwar Muhammad Ali Khan
- Kasuwar Ja’afar Khan
- Kasuwar Sadri (Yarima Fazel)
- Kasuwar Darvazeh Mehriz
- kasuwar tagulla
- Kasuwar Nokhod Barizi
- Lambun Mosher Almamalik
- Gidan wankan Khan Bafghi
Randabawul-Randabawul na tarihi
- Meidane Khan
- Meidane Besat
- Mediane Qal’e
- Meidane Amir Chaqmaq
- Meidan Vaqt-o Sa’at
- Lord Asiab
- Lord Bajordi
- Lord Tazian
- Lord Khwaja Khizr
- Lord Fahadan
- Lord Kevan
- Lord Godal Mosalla
- Lord Koche Mirgotb
- Lord Moshir
Fitattun masallatan tarihi
- Babban masallacin Yazd
- Masallacin Amir Chaqmaq
- Masallacin Sarrig
- Masallacin Mulla Ismail
- Masallacin Shah Tahmasb
- Masallacin Farat
- Masallacin Hazireh
- Masallacin Mir Khizr Shah Char Manar
- Masallacin Beyaq Khan
- Masallacin Ahrestan
- Masallacin Shah Yahya (Qal’e Kohne)
- Babban masallacin Posht Bagh
Gidajen tarihi
- Gidan tarihi na Markar
A wuraren tarihi na Yazd za a iya ƙara masallatai 30, wanda ke taka rawar “masallatan unguwa”.
Wuraren tarihi
Babu shakka daga cikin abubuwan da garin ya keɓabta da su akwai tsofaffin unguwanni na tarihi waɗanda aka gina da laka da yumɓu, kasuwanni, masallatai, da gidaje. Akwai jimillar unguwanni 77 na garin Yazd waɗanda suke kewaye ko cikin yankin tarihi na garin, sakamakon haka a shekarar 2005 an yi musu rijista la lambar 15000, da sunan “Historical context of Yazd” a cikin “Athar Melli” wanda mafi muhimmanci daga ciki ita ce unguwar “Chahar Manar”. Unguwannin Masjid Jame, Bazar Nou, Fahadan, da Abol Qasem suna cikin babban yankin yawon buɗe ido na lardin sannan suna nan tsakanin babban masallaci da kurkukun Iskandar.
Hotal Hotal da Masaukai
- Dad Hotel
- Emarat Malmir Hotel
- Safaieh Hotel
- Bagh Moshiral Momalik Hotel
- New Citadel Hotel
- Fahadan Hotel
- Mehr Hotel
- Lab khandaq Hotel
- Khahan Do had Hotel
- Firouzeh Hotel
- Adib Al Momalek Hotel
- Pars Traditional Hotel
- Yazd Tourist Inn
Karatu a Yazd
Duba da bayanan da suka gabata a sama, garin Yazd wanda ke ɗauke da cibiyoyin ilimi da dama irin su Shahid Sadoughi University of Medical Sciences (ɗaya daga cikin fitattun jami’o’in kimiyyar likitanci), ya zama babban ginshiƙi na neman ilimi a yankin tsakiyar Iran.
Baya ga duk waɗannan abubuwa, garin Yazd na da wuraren shaƙatawa masu yawa. Gari ne wanda ya dace da ɗaliban ƙasashen waje.