Ɗaya daga cikin ayyuka mafi wuya da ɗalibai ke cin karo da su shi ne zaɓen jami’ar da za su yi karatu. Zaɓen jami’a ya kasance al’amari mafi muhimmanci ga ɗalibai. Sanin kowa ne jami’a kan iya canza rayuwar mutum. A wannan rubutu, za mu kawo muku bayani a kan janibobi daban-daban na karatu a Ferdowsi University kamar makarantunta, kwasa-kwasanta, kayan aikinta, da sauransu domin sauƙaƙe muku yin zaɓi mai kyau don ci gaba da karatunku. Ku kasance tare da mu.
Gabatarwa
Domin gabatar da Ferdowsi University, lazim ne mu yi ishara a kan cewa Jami’ar Ferdowsi wata jami’ar gwamnati ce a ƙasar Iran wadda a ke yi ma kirari da uwar jami’o’in garin Mashhad. A wannan jami’a, ɗalibai za su iya karatu a tsarin rana, dare, ko tsarin online. An assasa jami’ar ne a shekarar 1949 kuma a halin yanzu akwai kimanin ɗaliban Iran 23700, da ɗaliban ƙasashen waje 2513, malamai 813 a ciki. Yawan adadin ɗaliban da suka kammala karatu a wannan jami’a ta Ferdowsi ya kusa mutum 110000. Jami’ar Ferdowsi na da kwasa-kwasai 435 a matakai daban-daban na karatu, a cikin department 63.
Maƙalolin da Ferdowsi University ta wallafa
Adadin maƙalolin ilimi: maƙala 32671
Adadin maƙalolin ƙasa da ƙasa: maƙala 21049
Ta mallaki lambar yabo kuma ta wallafa mujalla 48 na musamman
Martabar Ferdowsi University of Mashhad
A sabon binciken ranking na jami’o’i, Jami’ar Ferdowsi ta samu matsayi na 901 – 1000 a tsarin ranking na Shanghai wanda martaba ce mai kyau idan an kwatanta da sauran jami’o’in Iran.
Har ila yau, Jami’ar Ferdowsi ta Mashhad ta samu matsayi na 1001 – 1200 tsakanin jami’o’in duniya, in ji tsarin ranking na Times.
Ta wani janibi, wannan jami’a ita ce a matsayi na 3 a jadawalin ranking na jami’o’in Iran inda ta biyo bayan Jami’o’in Tehran, Farhangian, da Shahid Beheshti.
Gine-Gine da wurare
• Babban gini (cibiya)
• Cibiyar bayanai da babban laburare
• Gidan tarihi na Ferdowsi University ta Mashhad
• Cibiyar sanadodi da abubuwan alfaharin jami’a
• Engarium (hasumiya ta sama na Jami’ar Ferdowsi ta Mashad)
• Masallacin Sayyida Zahra (AS)
• Masallacin Imam Reza
• Wallafe-Wallafen jami’a
• Cibiyar bunƙasa fasahohin zamani
• Cibiyar sadarwa ta ɗakin gwaje-gwaje
• Cibiyar jin daɗi (lamba 1 da 2)
• Masaukin baƙi na Jami’ar Ferdowsi
• Sashen (ofisoshin) al’adu, zamantakewa, da harkokin ɗalibai
• Kula da walwala da lafiya
• Rukunin wuraren kwana na Pardis (mata)
• Rukunin wuraren kwana na Fajr (maza)
• Wuraren cin abinci (Fajr, Pardis, Mehr, Zeitoon, da Yas)
• Kafteriya (a hostel da makarantu)
• Cibiyar kiwon lafiya da magani
• Sashen gudanarwa na motsa jiki
• Pardis water complex
• Rukunin wasanni na 22 Bahman
• Zauren wasanni na Jahan Pahlavan Takhti
• Zauren wasanni na Imam Reza
• Zauren wasanni na Imam Ali
• Zauren wasanni na Kowsar
• Rukunin wasan tennis na waje
• Wuraren wasanni na waje (haraba da kwalejoji)
• Wuraren wasanni na hostel
• Sashen gudanar da ayyukan al’adu da ayyukan sa-kai
• Cibiyar shawara da ƙarfafawa
• Cibiyar fasahar ƙere-ƙere
• Zauren Rudaki
• Cibiyar fasahar bayanai da sadarwa
• Consumer Cooperative Company (chain store)
• Babban zauren taruka
Makarantun bincike na Jami’ar Ferdowsi
• Havakhorshid Research Institute
• Plant Sciences Research Institute
• Water and Environment Research Institute
• Biotechnology Research Institute
• Oil and Gas Research Institute
• Research Institute of Aviation Sciences and Technologies
• Pilgrimage and Tourism Research Institute
• Research Institute of Islamic Studies in Human Sciences
Cibiyoyin bincike na Jami’ar Ferdowsi
• Applied Zoology Research Center
• Research Center for Road Safety Technical and Economic Studies
Ƙungiyoyin bincike na Jami’ar Ferdowsi
• Earthquake Science Research Group
• Eastern Iran Mineral Reserves Exploration Research Group
Makarantu
• Faculty of Literature and Human Sciences
• Faculty of Theology and Islamic Studies
• College of Science
• Faculty of Veterinary Medicine
• Faculty of Law and Political Science
• Faculty of Administrative and Economic Sciences
• Faculty of Mathematical Sciences
• Faculty of Education and Psychology
• Faculty of Sports Sciences
• School of Agriculture
• Faculty of Architecture and Urban Planning
• Faculty of Natural Resources and Environment
• Faculty of Engineering
Kayan aikin Ferdowsi University
• Koriyar hanyar keke da system
• Motocin jigilar mutane a cikin jami’a
• Harabobin hostel
• Manyan wuraren cin abinci guda 4
• Gidan cin abinci na gargajiya na mata
• Swimming pool
• Koren Fili
• Wurin gina jiki (gym) a farashin wata-wata mai rahusa
• Babban laburaren jami’a
• Filin wasan paintball
• Kowace makaranta tana da teria ta kanta a keɓe
• Babban kantin kaya na haɗin gwiwa
• Haka kuma akwai kantin sayar da kayan marmari da gidan burodi ga ɗaliban hostel
Jerin wasu daga cikin kwasa-kwasan da a ke yi a matakin Masters da PhD a Ferdowsi University ta Mashhad
• Persian Language and Literature
• Arabic Language and Literature
• French Language
• English Language
• Russian Language
• Social Sciences
• Geography
• History
• Islamic Philosophy and Wisdom
• Jurisprudence and Principles of Islamic Law
• Quran and Hadith Sciences
• Islamic History and Civilization
• Comparative Religions and Mysticism
• Islamic Education
• Geology
• Biology
• Chemistry
• Physics
• Economics
• Management
• Accounting
• Law
• Political Sciences
• Agricultural Economics
• Biotechnology and Plant Breeding
• Biosystem Mechanics
• Soil Science
• Agrotechnology
• Horticultural Science and Green Space Engineering
• Animal Science
• Science and Food Industry
• Plant Medicine
• Water Engineering Sciences
• Electrical Engineering
• Chemical Engineering
• Industrial Engineering
• Civil Engineering
• Computer Engineering
• Mechanical Engineering
• Metallurgy and Materials Engineering
• Textile Engineering
Ƙofofin shiga da yanayin kusancinta da gari
Ƙofar Arewa: Ana ɗaukarta a matsayin babbar ƙofar shiga Jami’ar Ferdowsi ta Mashad, inda shugaban wannan jami’a yake. Haka kuma cibiyar jami’ar, da makarantar Theology da ta Islamic Studies suma suna kusa da wannan ƙofa. Ƙofar ta na kallon babban titin Wakil Abad da kuma babban park na Mellat. Har ila yau, dangane da hanyoyin shiga cikin gari daga wannan jami’a, akwai layi mai lamba 1 na jirgin ƙasan garin Mashhad mai suna ‘Tashar Jami’ar Ferdowsi ta Mashhad – Park Mellat’, da kuma tashar motocin jigila na cikin gari duk a kusa da wannan jami’a. Ya kamata a lura cewa a halin yanzu, ana amfani da wannan ƙofa domin masu tafiya a ƙasa ne kawai.
Ƙofar Gabas: Wannan ƙofar tana kaiwa zuwa babbar hanyar Kalantari da Dandalin Azadi. Hakazalika bayan tashar mota, tana kusa da tashar metro da ke line 1 mai suna Azadi.
Ƙofar Yamma: Wannan ƙofar tana kaiwa zuwa titin Bahnar da Kausar Park. Har ila yau, bayan tashar autobus, ƙofar na kusa da tashar metro ta Mashhad mai suna Kausar. Makarantar Engineering da ta Mathematical Sciences na kusa da wannan ƙofar.
Ƙofar Kudu maso Gabas: Ita kuma wannan ƙofar, wacce ake kira ‘Darabe Razavi’ tana kaiwa ne zuwa titin Razavi. Makarantar Educational Sciences da Psychology na kusa da wannan ƙofar.
Ƙofar Kudu: Wannan ƙofar tana kaiwa zuwa babbar hanyar Pirouzi. Hostel ɗin Pardis 3, 5, 6, da 7 (na mata) duka suna kusa da wannan ƙofar.
Sauran ƙofofin shiga da hanyoyin gefe: A wurare daban-daban na jami’ar, akwai ƙofofi da a ka sanya domin masu tafiya a ƙasa. Za mu iya nuni zuwa ƙofar arewa maso yamma da ke kusa da Faculty of Mathematical Sciences da Bankunan da ke cikin jami’a, da kuma ƙofar psychology clinic ta Faculty of Educational Sciences and Psychology a titin Bahner.
Cibiyoyin Kimiyya
• Shahnameh and Ferdowsi Scientific Center
• Scientific Center for Bioeconomy and Healthy Food Studies
• Scientific Center for Analysis on Algebraic Structures
• Scientific Center for Modeling and Calculations on Linear and Non-linear Systems
• Scientific Center for the study of Abortion and Infant Mortality of Ruminant Animals
• Scientific Center of Special Crop Plants
• Science Center for Cold-tolerant Legumes (peas and lentils)
• Scientific Center for Management of Low Irrigation and Non-conventional Waters
• Iranian Natural Hydrocolloids Scientific Center
• Scientific Center for Soft Computing and Intelligent Information Processing
Kuɗaɗen da ake buƙata domin karatu a Ferdowsi University of Mashhad
Ɗaya daga cikin dalilan ɗalibai na zaɓar Jami’ar Ferdowsi shi ne rashin tsadar rayuwa idan aka kwatanta da sauran fitattun jami’o’in ƙasar nan.
Jadawalin Kuɗin Makarantar Ferdowsi University
Abun lura 1: Rangwamen kaso 70% a kan ƙayyadaddun kuɗaɗen makaranta da kuɗin darussa ga ɗaliban harshen Farsi da adabinsa.
Abun Lura 2: Rangwamen 70% a kan ƙayyadaddun kuɗin makaranta da kuɗin darusa ga ɗaliban ƙasar Afghanistan.
Abun Lura 3: Rangwamen aƙalla kaso 20%, tsanani kaso 40% na ƙayyadaddun kuɗaɗen makaranta da kuɗin darusa na fitattun ɗalibai (matsayi na farko zuwa na uku a matakin digiri).
Abun Lura 4: Daliban da ba Iraniyawa ba “Mazauna Iran” , za a iya ɗaukar su ba tare da jarabawa ba bisa dogaro da ƙa’ida mai lamba 307862/2, mai kwanan wata 10/17/1401, za su iya amfana da abubuwan da aka ambata a cikin wannan ƙa’ida, za kuma su iya karatu da rana a matakan Masters da PhD.
Abun Lura 5: Rangwamen kaso 20% a kan ƙayyadaddun kuɗin makaranta ga kowane ɗalibi wanda wani daga cikin danginsa (kamar: ɗan uwa, ƴar uwa, miji ko mata, mahaifa, ƴaƴa a matsayin ɗalibai) wanda su ma suke karatu lokaci ɗaya a Jami’ar Ferdowsi.
Abun Lura 6: Rangwamen kaso 30% a kan ƙayyadadden kuɗin makaranta ga ɗaliban PhD waɗanda suka kammala duka digirinsu biyu (Bachelor’s da Master’s) a Jami’ar Ferdowsi ta Mashhad.
Abun Lura 7: Rangwamen kaso 10% a kan ƙayyadaddun kuɗin makaranta ga ɗaliban da suka taɓa kammala kowani irin digiri a Jami’ar Ferdowsi ta Mashhad, a baya.
Abun Lura 8: Idan dalibi ya janye (daga yin karatu), ya zama dole ya biya jami’a ƙayyadaddun kuɗin makaranta na semester biyu.
Kuɗaɗen da ake buƙata don karatu a Jami’ar Ferdowsi sun kasu kashi biyu: kuɗin masauki da kuma kuɗaɗen makaranta wanda ake kira da shahariyya.
Idan kuna shirin zama a garin Mashhad, zaku iya neman masauki ta hanyoyi biyu. Hanya ta farko ita ce kama ɗakunan kwanan dalibai wato hostel, hanya ta biyu kuma ita ce neman masauki a wajen makaranta. Domin sauƙaƙe muku zaɓi, mun kwatanta duka hanyoyin biyu da juna a jadawalin ƙasa.
A ci gaban wannan rubutun, mun kawo muku dukan kwasa-kwasan da ake yi a jami’ar Ferdowsi a matakin Masters da na PhD.
Adireshin Ferdowsi University
Adireshi: Mashhad, Meidan Azadi, Ferdowsi University of Mashhad
سوالات متداول در مورد معرفی دانشگاه فردوسی مشهد
- آیا مقطع دکتری در دانشگاه فردوسی برای غیر ایرانیها پژوهش محور میباشد؟
خیر، متاسفانه در این دانشگاه بعد از مهر 1401 دوره به صورت آموزش _ پژوهش ارائه میشود. - آیا برای بررسی پرونده در دانشگاه فردوسی نیاز به پرداخت مالی میباشد؟
خیر، از نمیسال دوم سال 1401 این هزینه حذف شد. - مهمترین اصل برای ثبت نام و پیگیری وضعیت در دانشگاه فردوسی چه میباشد؟
شما برای ثبت نام در دانشگاه فردوسی نیازمند به یک شرکت با مجوز رسمی از طرف وزارت علوم میباشید مثل شرکت ما.
[neshan-map id=”22″]