[gtranslate]
Search
Unit 3, No. 15, the beginning of Ahmad Abad Street, Mashhad, Iran

Karatu a Babol

Karatu a Babol

Loading

Idan kuna shirin karatu a Babol, mun shirya muku wannan maƙala wadda a ciki mun yi bayani a kan garin Babol ta yadda za ku iya yin zaɓinku cikin sauƙi. Ku kasance tare da mu.

Babol

Babol gari ne a arewacin ƙasar Iran a lardin Mazandaran. Garin Babol ya shahara da suna “Bahar Naranj” a tsakanin Iraniyawa. Mutanen Babol ƴan ƙabilar Tabari ne kuma suna magana ne da yaren Mazandarani.

Garin Babol na cikin muhimman garuruwan arewacin Iran ta ɓangaren likitanci, noma, jami’a, siyasa, al’adu, da kuma kasuwanci.

Adadin yawan mutanen garin ya kai mutum 250,217.

Bayani a kan Babol

Zirga-Zirga

Garin Babol baya da tashar jirgin ƙasa saboda kusancinsa da sauran gagruruwan arewacin Iran, sai dai ayi amfani da tashar jirgin ƙasa ta Qa’emshahr mai tazarar kilomita 15 daga Babol.

Akwai tashoshin fasinja guda uku a garin na Babol waɗanda ake amfani da su wurin jigilar matafiya.

Wuraren yawo a Babol

Wuraren shaƙatawa da morewa

Dalilin kusancinsa da tekun Caspian, garin Babol na da tafkuna masu yawa. Akwai Tafkin Sad Shayadeh wanda ke kusa da ƙauyen Shayadeh, ana yawan zuwa wurin domin shaƙatawa a kwanakin idin Noruz da lokacin zafi.

Babolkenar Forest Park wuri ne na shaƙatawa mai matuƙar kyau kuma cike da ciyayi wanda ke samun maziyarta da yawa a garin Babol.

Akwai wani waterfall mai kyau a gabashin garin Babol mai suna Haji Shaikh Musa Waterfall.

Daga cikin wuraren addini mafi muhimmanci na garin Babol akwai makwancin Imamzadeh Qasem, masallacin Muhaddesin, da babban masallacin Babol.

Saboda daɗewar da garin Babol ya yi da tarihin da yake ɗauke da shi akwai wuraren tarihi da yawa a cikinsa. A zamanin Qajar, Nasiral Din Shah a karonsa na biyu na zuwa Mazandaran, lokacin da ya shiga garin Babol saida hankalinsa ya karkata zuwa ga shaguna da masaukan baƙi na garin. Akwai masaukan baƙi da yawa a garin.

Fadar Shapour, hasumiyar fadar Babol, gadar Muhammad Hassan Khan, duk suna cikin wuraren tarihi da ke garin Babol.

Jami'o'in Babol

Cibiyoyin ilimi da jami’o’i

Akwai jami’o’i da manyan cibiyoyin koyarwa sama da guda 20 a garin Babol. Jami’a mafi muhimmanci daga ciki ita ce Babol Noshirvani University of Technology wadda ta zo a matsayi na ɗaya a tsakanin jami’o’in fasaha na ƙasar Iran. A sakamakon ranking na US News na shekarar 2022, an bayyana jami’ar ta Babol Noshirvani a matsayin jami’a ta 4 a ƙasar Iran inda matsayinta ya ɗara na jami’o’in Sharif University of Technology, Amirkabir University of Technology, Iran University of Science and Technology, da K.N. Toosi University of Technology. A wannan ranking ɗin jami’ar Babol Noshirvani ta samu matsayi na 104 a ɓangaren Engineering a tsakanin jami’o’in duniya. Domin samun cikakken bayani game da jami’ar, ku karanta rubutunmu na Karatu a Babol Noshirvani University of Technology.

Hakazalika garin Babol shi ne gari na farko a arewacin Nigeria wanda aka assasa jami’ar likitanci a cikinsa.

Wuraren yawon buɗe ido a Babol

Dalilin karatu a Babol

  • Idan kuna sha’awar karatu a Babol yana da kyau ku san cewa kuɗin makarantar jami’ar Babol Noshirvani na da sauƙi a kan na sauran jami’o’in garin Tehran, amma babu wani bambancin azo a gani tsakaninta da sauran jami’o’in fasaha. Haka kuɗin masauki a garin Babol ya fi arha da kusan kashi 20% akan Tehran, saboda haka garin Babol ɗaya ne daga cikin garuruwa masu sauƙin kuɗin karatu.
  • Jami’ar fasaha ta Babol Noshirvani da Jami’ar kimiyyar likitanci ta Babol suna daga cikin jami’o’in Iran mafi kyau kuma mafi inganci hakazalika shaidar kammala karatu da suke bayarwa karɓaɓɓiya ce a sauran ƙasashen duniya. Waɗannan jami’o’i suna da kayan aiki da tsarukan karatu mafi inganci da suka tanada irinsu laburare, ɗakunan gwaje-gwaje, rukunan wasanni da shaƙatawa, wuraren cin abinci duk domin ɗalibai.
Related Posts
Leave a Reply